← Book details A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 93

Sashe 64

A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Hummm Hansatu ke dai sai dai ni ce Allah shi yi miki sauqi, kin bi kin koyawa yara baqar tabi'a, tunda sun ka shigo sun ka kawo abinci na yi godiya sun ka amsa, nace kwana (bacci) ki ke ne da Ameenatu tace ke ce su zauna sai kin taho, Diyan ga sun ka debo ijiya(ido) sun ka zuba min(Aminatu ta ce kin ce su zauna sai kin taho,suka dauki ido suka saka min) qalallahu qala ta'ala ba wanda yace min cikin su, har da wanga d'an tatsitsin yaro, maganar duniya sun manna min hauka, ba wanda yace min komi, sun yi didd'didd'ifff"

Dariya Hansatu ta sa, dan ta san wannan aikin Ameenatu ne, ita ce zata hana su magana kan su shiga, Bilkisu ta sha fad'a mata, in sun je waje Ameenatu na hana su magana, komai aka tambaye su, su ce su ma basu sani ba, ko su yi shiru su zubawa mutum ido kawai.

"Ki yi hankuri, na gode da ki ka aje min su, bari mu tafi gida, mangariba ta yi"

Tsaki 'Yabbuga ta yi, ta miqe daga gaban Ahmad, da tai Wa zaman neman gafara, ba kalar lallaba yaron da bata yi ba, dan ta ji labarai a wajen shi ya qi bude baki sam.

Ita kuma kamar mayya, a nan gaban su ta cinye abincin da suka kai mata, ta na yi ta na tambayar su gidan su, su kuma su na ta kallon ta, sun qi amsa ta.

Sai da Hansatu za su fita ta juya ta ce ma 'Yabbuga,

"Yau fa Baban su Ameenah ya dawo,"

Wata gud'a da shewa 'Yabbuga ta buga, ta buga cinya, kafin ta yi magana Hansatu ta tisa qeyar yaran, ta ce su yi gida, ita kuma ta tsaya, dan 'Yabbuga na iya bin ta, har gida, ta fadi abinda zai sa wa yaran ta tunanin me ake nufi da kazan nan da aka fada.

"Hahaiiiiii cassss! ko da na ji, yanzu na ji batu,dan ko na san ruwa da iska ba ki barin d'iyan nan zuwa ko ina, ku na nan manne da juna, ashe ashe uban su ne yaddawo ana can ana biyan bashi , shi yasa aka koro su, tauuuu, to ko za ki kawo su su kwana nan? Kar su yi mummunan gamo"

Cikin takaici Hansatu ta kalle ta tace,

"Bayan na haifi Ameenatu, Bilkisu ta biyo baya, duk su na nan sun fara wayo nayyi cikin Ahmad, kuma har yau idon su ko kunnen su bai gane musu komi ba in shaa Allahu, ke ga kuwa ba abinda za su gani a gaba ma, in shaa Allahu, na gode sai da safe"

Hansatu na fadin haka ta tafi, 'Yabbuga kuwa ran ta ya ɓaci, nan da nan ta hau sakin maganganu marasa dad'i.

"Keeeee wagga ban ce ki fada min baqa ba, yaushe na an ka jone da mijin har da za ki yi min kitihin yohi? Mijin da mun san komi, ba qaunar ki shi kai ba? Wanne irin kashin wahala ne baki sha hannun shi ba? Ba ci ba sha, ba sutura, nan nan gidan kin shigo shi kin yi maula ba a ko qirgawa, yo Allah na tuba wane dare ne jemage bai gani ba, kai ku ji min yarinya da kitihi,"

Hansatu na cikin gidan ta tana jin komai, kasa jurewa ta yi, ta fita, ta koma gidan 'Yabbuga dake ta sababi, ta ke yi mata gori kala kala.

'Yabbuga bata ji shigowar Hansatu ba sai kalaman ta,

"Na gode wa Allah, kuma na gode miki da Allah ya azurta mu a lokacin da muke cikin matsin rayuwa ta hanyar ki, na gode miki da kika taimaka mana a lokacin da muke da tsananin buqatar taimako, banda bakin yi miki godiya sai dai na roqi Allah da ya sauya maki halayen ki, daga munana zuwa kyawawa, shi saka maki da alkhairi, duk abinda kin ka fadi gaskiya ne, amma ki sani, in a baya Allah ya baki lada, to fa a yanzu zunubi ki ka dauka, domin kin zobe ladan da yabbaki ta hanyar yi min gori, kin san kuwa hanin da aka yi akan gori? kin tozarta ni akan abinda ki ka min a baya, kin yi min gori, ni kuma ba zan rama ba, amma kar ki manta abu guda, shi zama in ya hada ka da koma wane ne, abu guda dole sai ya faru, ko ku zauna lahiya kowa shi amfana da kowa, ko ku cutar da junan ku, ki dinga tuna baya kahin ki yi min gori, sai da safe"

Jikin 'Yabbuga bai taba sanyi ba irin na yau, ashe Hansatu na da baki? A fakaice wadannan maganganun da ta wa 'Yabbuga dukkan su suna da fassarar su da ma'anar su kala kala, da 'Yabbuga na tuna baya da bata yi wa Hansatu gori ba, domin sai da ta fara morar Hansatu kafin Hansatu ta more ta, sai dai duk abinda Hansatu ta yi wa 'Yabbuga Hansatun bata taɓa sanar da kowa ba, itama 'Yabbuga bata taɓa fadawa kowa ta mori Hansatu ba sanda ta na amarya, amma ko gishiri hansatu ta karba wajen ta, sai ta qara tace har da Maggi da mai ta bata.

Jiki ba kwari ta yi alwala ta shige daki.

Hansatu kuwa ko da ta koma bata ga Isah ba, ba kuma ta ga akwati guda ba, a cikin kayan da ya zo da su,bata ce komai ba, ta jawo dan qaramin gas din su, ta ɗora ruwa, ta na so ta yi musu abincin dare.

**************************

Gwamna Halliru ya kira wayar Lawwali, cikin nasara kuwa ta shiga, ya na dauka Gwamna ya fara magana cikin fada.

"Lawwali ina ka kai min d'iya ta? Lawwali in wani abu ya samu d'iyaa ta..."

"Uban mi zaka min in wani abu ya same ta? Na ce uban mi za ka min? Ka ga.."

Sauke Sultana ya yi, da ke kwance a jikin shi, ta na wa kan shi susa, wai ta na so ya yi bacci, ya huta da horon da ya dage ya na bawa yaran shi, fita ya yi waje, dan baya so ta ji da wa yake magana, duk da ya kula hankalin ta ya tashi, da jin kalaman shi.

"...na ce uban mi ka isa ka min? Kai ka san ko ni wane ne, inna ga dama a yau ba zaka kwana gidan gwamnati ba ko gidan ka, ka san ba ka kwana ko? Kaiii inna so yau da kai da iyalan ka kafff ba ku kwana duniyar ga baku kwanan ta ko? To mi zaka min?"

Wasu irin jijiyoyi ne manya manya suka fito rudu rudu a goshin Lawwali, qirjin shi da babu riga, sai bugawa yake da qarfi, hannun shi d'aya ya dunqule kamar mai shirin kai naushi.

Gwamna Halliru ne ya sassauta murya ya ce,

"Lawwali kai wa Allah kar ka cutar da d'iyaa ta, she is innocent, ba ta da wani alaqa da abinda ke tsakanin mu, na amince, na yarda ban kyauta maka ba, duk yanda kake so ka yi ka yi da ni, amma kar ka cutar da diya ta"

Wata mahaukaciyar dariya Lawwali ya saki, sai da yaran shi da ke waje suka kalle shi, sun san kalar dariyar, dariya ce ta ɓacin rai matuqa, kuma ko waye Lawwali ke wa irin dariyar nan, ya na gab da d'and'ana azabar Lawwali.

Tafiya ya yi jikin wata bishiya ya tsaya, sannan ya ce,

"Kar na cutar da d'iyar ka fa kace, she is innocent, me qaunata ta yi maka? Bari in maka da Yaren da zaka fi ganewa Excellency you are going to regret making me the way I am today, ba dai turanci ne ba? Na iya shi, ga shi nan na yi ma, innocent d'iyar ka ka san yanzu haka ta na can na..."

Cikin b'acin rai Gwamna ya ce,

"LAWWALIII !"

Lawwalin ma a hasale ya ce,

"HALLIRU ! Babu yadda za ka yi da ni, sai na shayar da kai gubar da ka dura min ta ta'addanci, sai na lalata rayuwar ka ta inda baka yi zato ba, sai na qarar maka da duk wani abinda ka mallaka, ko me ne ne shi, sai na maida kai abin kwatanci a Nigeria kai har da wasu qasashen, sai na nuna maka ba kowanne d'a ya kamata Ku manya ku lalata wa rayuwa ba ! Sai na shayar da kai abinda ka shayar da ni na baqin cikin rayuwa da duhun ta"

Kashe wayar ya yi, ya wurgar, ya dinga sauke wani irin nishi, duka ya dinga kai wa bishiyar da ya ke tsaye a jikin ta, yaran shi duk sun tsaya cirko cirko, ba mai zamar da ya isa ya tunkare shi a wannan halin da yake ciki.

Gashi duk ya ji wa kan shi ciwo, da dane zuwa zai yi ya debo mutane ya yi ta kisa ba gaira ba dalili, amma yanzu ya na qoqarin sauyawa, daga yawan kashe kashen da yake.

A guje Barirah ta fad'a dakin su Sultanan ba tare da ta nemi izini ba, kwance ta ga sultana ta na ta tunanin da wa Lawwali ke waya, ta ga ran shi bace, har ya na kiran uban wa.

"Ran ki shi dad'e ki gafarce ni, na shigo ba tare da izini ba, amma Oga na buqatar ki a waje, ya na can shi na ji wa kan shi ciwo"

Ai kafin Barirah ta qarasa kalaman ta Sultana ta dire a qasa, jikin ta har rawa yake, wanne irin ciwo kuma? Dankwalin ta take ta ja, ya maqale a jikin gadon, sakin shi ta yi ta fita da gudu, Barirah na gaba, su na zuwa wajen Barirah ta nuna mata Lawwalin ta maqale a baya, Sultana na hango jini a hannun Lawwali ta sa kuka, ta tafi da gudu ta fada jikin shi da qarfi,hannu ya sa ya fizge ta daga jikin shi ya wurga ta gefe, ta fadi qasa, cikin bacin rai ya kalle ta, ya ce,
Chapter 64 · 0% Book details