← Book details A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 93

Sashe 77

A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da suka tsaya Lawwali ya yi siyayya ta kayan kwalama, da duk wani abu da ya san Mubaraka na so, har zai fita daga wajen shopping din bai sai wa Sultana komai ba, sai ya ji ya kasa tafiya, komawa ciki ya yi, ya daukar mata best chocolate din ta, da candy din da ta fi so, sannan ya ga wani turare mai kyau na mata, daukar mata ya yi, ya na murmushi.

Sai da ya biya kudin komai, sanan ya koma mota, Mubaraka na nan zaune, ta na ta tunanin yanda za ta sanya Lawwali ya bar Su sultana Su je su ga iyayen su, Hajiya Ikee ta matuqar bata tausayi.

Ajiye mata ledojin ya yi a cinyar ta, ya koma mazaunin driver ya zauna.

"Barakana ga naki nan, wancan na Sultyna ne, ki bata amma kar ki ce ni ne na bayar a bata,"

"Yah Auwal kenan, ana soooo ana kaiwa kassuwaaa"

Dariya suka yi, sannan ya tada motar dan komawa gida.

Mubaraka ta matsu su koma, dan basu yi sallar azahar ba, ga la'asar ta Kunno Kai.

************************

Hajiyan Hansatu ce ta kira Hansatu, ta ke tambayar ta, tunda Isah ya tafi sun yi waya kuwa? Saboda yau sati d'aya da kwana uku ba labarin Isah ko ta ina, layin shi tun ya na shiga ba a dagawa, yanzu ya ma dena shiga.

Hansatu ta rasa amsar da za ta ba Hajiya, kawai sai ta ce,

"Shi na lahiya qalou Hajiya, kar ki damu, in mun kai waya zan sanar masa ki na so ku gaisa"

"Ahhh ahh basshi d'ai, dama son nikai na ji lahiya shike ko ah ah"

"Shi na lahiya lumui Hajiya, ina Yayah Musa? Shin aunty bata dawo ba har yanzu?"

"Shekaran jiya dai Yayan ki ya aika musu da takardar saki, ya ce ya gaji da iskancin ta,na so na hana shi, na kira na mata magana, ta inda take shiga ba ta nan taka hita ba, wai na bi na qanqame d'a na, na hana su sakewa, ban barin shi ya je wajen ta, ke ki ji hwa?"

"Kayyaa ban ji dad'in rabuwar su ba, Allah shi sa hakan shi ne ya hi alkhairi"

"Ameen, ina wannan me gidan da bai iya cehwane ba?"

"Shi na lahiya, ya ce zai siyo maki haqorin roba ki laqa, tunda na ki ya hwara tsuhwa"

Dariya Hajiya ta yi, suka ci gaba da hira cikin nishadi, ita da yar ta

************************

A kurkuku kuwa, Isah.............

*Sai anjima Inshaa Allahu*

💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻

BY HAERMEEBRAERH

PAGE 57:

Isah na can an miqa shi wajen kuliya manta sabo, ba irin bayani da Isah bai yi ba,amma abu ya ci tura, duk iya bincike da shaidu sun nuna koken ta Isah ce,dan haka nan take aka yanke masa hukuncin shekara goma a gidan maza da horo mai tsanani,dan kuwa Saudiya ba kamar Nigeria  bace, ba su b'ata lokaci wajen yanke wa duk wani mai laifi hukunci, Isah ya yi kuka, ya yi kuka, ya godewa Allah, ba irin yunquri da bai ba na a bashi dama ya kira gida ba wanda ya bi ta kan shi, haka aka ingiza qeyar shi zuwa kurkuku.

Duk da cewa kurkukun su ba irin namu bane, mai cike da datti,qazanta da rashin abubuwan da mutum zai buqata, amma kurkuku kurkuku ne, Isah ya yi dana sanin zuwan shi Makka, ya yi dana sanin sanin sana'ar saida goro a rayuwar shi.

Tun ya na kuka da qarfi, ya koma yin na zuci, sai dai hawaye da ke kwaranya kamar an bude magudanar ruwa, rayuwar shi tun daga yarinta ya ke tunawa, shi dai gaba d'aya bai da sa'a a rayuwa, bai rabu da iyaye lafiya ba, ga iyalin shi ya baro su na fushi da shi, bai kyautata alaqa da su ba balle su neme shi, yanzu da ace a baya ya na kiran Hansatu da ya zo,ya san da ta ji shi shiru dole za ta neme shi,

"Kaico na, kaicon rayuwa ta ni Isah, yanzu ina zan saka rayuwa ta na ji dad'i, shekara goma ba kwana goma bane ba fa,"

(A haka Isah ya samu rangwame ne, domin kuwa wasu hukuncin kisa ake yanke musu a Saudiya, indai aka kama mutum da miyagun kwayoyi, wasu shekara biyu da bulalai, wasu goma da bulalai)

A ranar ko abinci Isah bai iya kaiwa bakin shi ba, duk ya fad'a ya yi zuru-zuru kamar ya yi shekaru a wajen.

A can gida Nigeria kuwa Hansatu ta d'auki shawarar Hajiyan ta, sun saka yaran a makarantar kud'i, driver guda Yaya Musa ya sama musu da mota, ya je ya kai su, in an tashi ya maida su gida.

Da yamma kuma Hansatu da kan ta za ta raka su Islamiyya, ta kuma gargad'e su kar su kuskura su koma gida ba tare da ta je daukan su ba, su zauna wajen Baba me gadin makarantar har ta je.

A cikin gida kuma ta kama sana'ar had'a sabulan gyaran jiki, dan kuwa ta kware sosai a haɗawa, jikin ta ya yi luwai luwai kamar matar wani hamshaqin.

Ta na yin sabulun tumeric

Sabulun water melon

Sabulun hinna

Sabulun carrot da

Sabulun cucumber.

Sai man kitso mai kyau da gyaran gashi, ta dage sosai wajen bunqasa sana'ar ta, da inganta ta, ta yanda kowa ya gani zai sha'awa, in mutum ya siya ya yi amfani da su, sai ya koma, kafin wani qanqanin lokaci Hansatu ta fara shiga gari itama,ta maida wa yaran ta da sana'ar ta hankali,lokuta da dama, in ba wani abu ne ya faru ba, mantawa take da Isah, ita kan ta ta na mamakin yanda a lokaci daya ya fita a ran ta.

(Duk Mai son man kitso Mai Sanya gashi tsaho da santsi da maganin amosalin Kai da karyewar gashi, ko Kuma Mai son sabulu Mai kyau da zai gyara wa mace fata ta yi kyau da sheqi, ko body scrub ko body oil ta nemi wannan No 09031416423...HAMIBRAH PRODUCTS sune na d'aya wajen maida TSOHUWA YARINYA )

(Haka lamarin yake, duk sanda aka samu namiji azababbe, da ya addabi iyalin shi da mugun hali da d'abi'a, to za a wayi gari duk wata soyayya, biyayya, da tsoron shi da iyalin ke ji ta kau, qiyayya mai qarfi da rashin jin qai za su maye gurbin soyayyar da aka masa a baya, haka in mace ce da bata iya magana ba, kuma bata da kyakkyawan hali da d'abi'a, a hankali take fita a ran miji, duk kauda kan da yake akan ta, kuma da ya fito mata da halayyar shi ta musguna wa shima, sai ka ji mace na fad'in mugu ne, ba shi da dad'in zama)

In sun samu lokaci da weekend sukan kai wa Hajiya ziyara, watarana kuma Hajiya da kan ta take zuwa,su gaisa.

Bayan Hansatu ta tura yaran ta makarantar boko ne, ta yi wanka, ta shirya cikin wani yadi mai kyau, da tsada, Hajiya ce ta musu anko har su Ameenatu, kulle gidan ta yi, ta fad'a na maqotan ta, wato 'Yabbuga, bakin ta dauke da sallama ta shiga.

Shiru ta ji ba wanda ya amsa,

"Shin mutanen gidan ga su na nan kuwa?"

Cikin wata iriyar murya, kamar an shaqe mutum, ko kuma mutum na cin abinci, haka ta ji an amsa mata da,

"Ko ni shigo ciki,na amsa"

Qarasawa ta yi, dan ta san masifar 'Yabbuga, ko ba abinda akai, ta na iya b'ata rai, ta na amsa wa mutum magana d'aya d'aya.

Hansatu ce ta ja ta tsaya, tare da rafka salati,

"Waggaa, mi ya faru hakan  na gankin  huska ta qabe (kumbura) me ya kwashe maki huska? Shin gobara ta kun ka yi ban sani ba? Ko hatsarin mota?"

Wata harara 'Yabbuga ta samu da kyar ta wurgawa Hansatu, sannan ta lashe dan saman bakin ta da ya haye, ya yi sintim, zama Hansatu ta yi a gefen 'Yabbuga, ta nata watsawa'Yabbugan tambaya, dan ta na son sanin me ya faru da ita, ta ga guiwar ta d'aya a dauje, ga gefen fuskar ta ya dauje shima, baki ya haye, 'Yabbuga dai bata kula ta ba, sai ma wani tuquqin baqin ciki da ke taso mata a rai da take ji, wai me ma ya kawo Hansatu gidan a irin wannan yanayin?

Sallamar Dan Jumma ce ta karad'e tsakar gidan, Dan Jumma da Hansatu sun gaisa ta masa ya me jiki ya amsa, tare da fad'in,

"Jiki dai ga shi nan, mai shi na jin shi,tunda kin gane ta nan, ta dai girme ki, amma kin hita hankali, da sanin ciwon kai, ta je jidali(fad'a) , can gidan Dan Talo, sun ka liqa mata mugun kashi"

A hasale 'Yabbuga ta kalle shi da kumburarran baki, ta ce,

"Wai shin uban wa yacce kashi an ka ban? Wacce ma kashi an ka ban eyee?"

"Tau sanda kin ka yi aniyar tahiya yin hwada(fad'a) akan atanhwar (atampa) da ko dubu uku ba a siye ta ba ban hana miki zuwa ba? Nan nan na dinga baki hankuri, zaman tare ba a haka nan, kema su na kyautata maki, kin ka ce ba ki iya hankuri sai sun biya, ki ka tai, kuma ki ka dawo a haka, bani cewa liqa miki kashin wahala an ka yi?"

"Banga wahala ba, sai dai ka gan ta nan bisa kan ka, ba wadda ta isa liqa min kashin wahala duk shiyyar nan balle gidan Dan Talo, bai auri matar da zata liqan kashi  ba, nace bai auri matar da zata ban kashi ba,"

"To in ba kashi sun ka baki ba mi na na ya hwaru?"

Cikin bata rai ta labarta musu duk abinda ya faru, Hansatu da Dan Jummaa kasa riqe dariyar su suka yi, sai da suka dara sosai, sannan Dan Jummaa ya ce,

"Ko da na ji, ashe ke da giinaa (gini) kin kai hwada tak-kashe ki qas, (ashe ke da gini ki kai fada ta kayar da ke qasa) kuma ke da d'an ki menene na gudu har da haure gini? Inda kin samu karaya hwa?"

"Walle gwanda na samu karaya a gini, da ace yaron nan mai baqar zucciya ya kammin, na zama abar kwatance ga shiyya,iyayen shi ma ba barin su ya yi ba balle ni"
Chapter 77 · 0% Book details