Sashe 69
A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ban gane shi kira Daddy ba, me ke faruwa ne? Ku na ta sa wa kai na na daure wa,"
"Yah Sultan in har ka bamu goyon baya akan abinda muke shirin yi, na maka alqawarin sanar da kai komai game da iyayen mu, wanda nake boyewa ba na so ka sani, dan kar ka shiga damuwa"
Kallon su kawai yake, ya ma kasa magana, kenan ta tabbata sato shi aka je har qofar gidan su aka yi, kuma ya zo ba tare daya san sato shin akai ba.
"Excellency sir, ka na lahiya?.....yi hankuriii ba fada ne yasa na Kire ka ba, wasu kadarorin ka ne a waje na, wanda duk duniyar ga baka da kamar su, ina mai tabbatar maka da cewar in baka dakatar da neman qauna ta ba, ta iso gare ni lahiya, zan manta da wai an tai central mosque an daura min aure da diyar ka, zan sa bakin bindiga na halbe ta, d'anka da na tai na dakko dazu...."
Cikin wata iriyar tsawa Gwamna Halliru ya miqe tsaye daga saman dining table din da ya ke cin abincin dare shi kadai, ya ce,
"Lawwali kar ka kuskura, kar ka sake ka taba min yara na,....... kai wa Allah Lawwali ka dawo min da yara na lahiya, zan janye binciken da ake akan qaunar ka"
"Nooo ka ci gaba da yi min fadan mana, me ya sa ka dena? Ga Sultana na so ta yi magana da kai"
Wayar Lawwali ya miqa wa Sultana, tare da daga mata yatsan shi babba, cikin maqale murya da kukan qarya ta fara magana,
"Daddy ka zo ka cece mu, mutumin nan mugu na..."
Lawwali ne ya amshe wayar, ya kunna a handsfree ,Gwamna sai magiya yake, kamar zai kuka,
"Sultana are you ok? Ina d'an uwan ki shi ke? Lawwali kai wa Allah ka sake min yara na, zan janye duk wani neman qaunar ka da nake, kai zan manta ma da kai da rayuwar ka, zan kyale ka ka yi duk abinda ka ga dama, amma na roqe ka kar ka yi wa yara na komi"
"Amma dai ka san qa'idar aikin mu ko? Kai ne fa ka ce in mun amshi kuddi, in diyan 'yan siyasa ne,ko 'yan siyasan da kan su, mu kashe, kar mu bari da rai, yanzu kuma ka ke son sauya muna doka?"
"Lawwali na janye wannan dokar, ga sabuwar doka nan, Lawwali kai wa Allah ka sake min diya na lahiya, ina Sultan? Sultan..."
Sultan na zaune ya na saurara kuma ya na ganin abun kamar wasan yara, ah ah mafarki ne, bai ma san me ya dauki abun ba, gashi nan dai ne kawai.
"...Sultan ka yi min magana,Lawwali kaji tsoron Allah kar ka cutar min da yara na,ba su da haqqin kowa, kar ka cutar min da yara na, ka sanar da ni ko nawa ka ke so, zan baka, ka sake su"
"Ashe ka san Allah?Ka dai san na san kuddin ka kuddin sata ne ko? kuddin tsafi ne, to ni a yanzu mi zan da kuddin ka? Baicin na gama samun iya abinda nake buqata a wannan harkar, kawai yaran ka nika son kashewa, dan na rama lalata min rayuwa da ka yi, ai na fada maka, sai na dau fansar abinda ka yi wa qauna ta,da iya ni ka taba,da na kyale ka, tunda ni ma ina da laifi nawa na kai na,ni na kawo kaina gare ku dan neman taimako, ku ciyar da baki da tumbin da ke tsananin jin yunwa da qishirwa,amma me kuka yi? Sai ku ka jefa rayuwa ta cikin halaka da lalacewa, amma duk da na san mugayen halayen ku,na ci gaba da zama da ku, tunda in na yi abinda ku ke so ku na bani abinda zan ci har da iyaye na ma, da ace ni kad'ai ka tab'a a yanzu, wataqila da na hakura, amma qauna ta? Ka yi na farko, yanzu ka na so ka yi na biyu? Inaaa, ba zan iya hakuri ba sam sam"
Gwamna Halliru bai san ya na kuka ba tun farkon fara wayar, sai da kukan ya ci qarfin shi ya kufce masa da qarfi, tura kujerar da yake kai ya yi, ya durqusa da guiwar shi a qasa, ya na roqon Lawwali, da ya kyale masa yaran shi, kar ya cutar da su.
Lawwali ne ya bawa Sultan wayar, shi kuwa ya rasa me zai ce, kalma ɗaya ce ta fito daga bakin shi, wato,
"Daddy"
Haba mana Gwamna na jin Muryar Sultan da gaske sai ya sake rikicewa, domin sai ya ji Muryar Sultan kamar a wahale, bai san tsantsar mamaki ke damun Sultan din ba, ya nufi sama, a gigice, Hajiya Ikee na ta kyale kyale,duk da halin jimamin da ake ciki bai hana ta kwalliya ba.
Yanayin da ta ga mijin nata ne ya sa ta sakin kwalbar turare a qasa, ta nufe shi zata kai masa cacuma ya bangaje ta, ya dauki sauran wayoyin shi zai fita, maganar da ta ji ya na yi ne ya sanya ta fahimtar inda aka dosa, cikin tsananin damuwa kuwa ta bi shi ta na kira, ko juyawa bai ba, sai da ya kai waje, cikin fada ya juya ya ce,
"Ke dayalla can ki koma gida ki zauna gani nan zuwa yanzun ga"
Wayar shi ya kalla dan yin magana ya ga an kashe kiran, bin kiran Lawwali ya dinga yi amma ba a dauka ba, tashin hankalin da ya shiga ba abun kwatanta wa bane, balle misali, da kyar ya ke ganin inda yake sanya qafar shi, kiran waya ya dinga yi, ya na dakatar da neman Mubaraka ta kowanne bangare.
Video'n yanda Lawwali ke ganawa wanda suka kama azaba ne ke gilmawa a idon gwamna, Muryar Sultan da Sultana sun cika masa kunne ,hango su yake a yanayi na azabtuwa da uqubar Lawwali.
Kafin ya kai jikin motar shi,jiri ya kwashe shi, ya fadi a qasa,drivern shi da securities ne suka daga shi aka sanya shi a mota, asibiti aka nufa da shi direct dan kuwa ba ya motsi.
Hajiya Ikee kuwa kuka take ta na qarawa, tare da tsinewa Lawwali albarka.
*********
A can daji kuwa Lawwali da Sultana sun bawa Sultan labarin duk abinda yake a boye a gare shi, na shekara da shekaru, har da wanda basu sani ba ma, sai da Lawwali ya basu.
Duk dauriya da qarfin zuciya irin na Sultan sai da ya yi kuka, da wahala ya yi kuka akan abu, sai dai a ga jijiyoyin kan shi na tashi, a ga idanun shi sun yi ja jawur, amma banda kuka.
Zuciyar shi ta gama karyewa, yanzu ace duk mahaifin shi ke aikata wadannan mugayen laifukan saboda son duniya da abinda ke cikin ta? Saboda siyasa da son mulki? To me ya tanadar wa kan shi a lahira? Me ya ke aikatawa na gari wanda Allah zai yafe masa wadannan mugayen laifukan? Shin mahaifin su musulmi ne kuwa? Ya na tantamar imanin shi da Allah, wanda ya ce Allah shi ne Ubangijin shi, Annabi Muhammad shi ne annabin shi, qur'ani da Hadith ne littafan da ya yadda su zama madubin shi, ba zai aikata shirka ga Allah ba, ba zai aikata abubuwan da gwamna Halliru Murtala Gusau ya aikata ba.
Miqewa ya yi ya fice daga wajen, bai san ina yake tafiya ba, kawai sai ganin shi ya yi, a wajen mutanen da aka kamo,a cikin hasken solar da aka sa a wajen yake hango wasu har da jariran yara a hannun su, wasu da ciki, wasu kuma gasu nan a wahale saboda hana shan kwaya da giya da Lawwali ya yi.
Hawaye ne kawai ke zuba a idanun Sultan da sultana dake take masa baya, Lawwali kuwa na tsaye ya na hango su, idanun shi sun kad'a sun yi jawur, to meye amfanin wannan rayuwar mara mamora?
Shi nashi iyayen su na can hankalin su kwance, basu damu da shi ba, basu damu da halin da yake ciki ba shi da qanwar shi, anya kuwa da ake cewa ba wanda zai haifi d'a a cikin shi ya qi shi gaskiya ne? Domin shi gashi ya gani da idanun shi, shi shaida ne,iyayen su basu damu da su ba, jiya ya amsa kiran 'Dan Talo ya na washe baki, wai gwamna ya ce ya bada hoton mubaraka sati Uku da suka gabata, wai gwamna ya mata miji, kuma sun ji shiru, ko zai bincika a ji me ke faruwa, a qarshe ya fara masa qorafin basu da abinci su da bisashen shi (awakin shi) gashi su Lamishi sun dena zuwa aiki,tunda yanzu su gwamna surukan su ne, be kamata su na zuwa aiki gidan ba.
Sai da Lawwali ya gama jin surutan Dan Talo ya fada masa jimla daya wato "Ku saida bisashen ku ci abinci" sannan ya kashe wayar shi.
Jikin wani kututturen itace Sultana da Sultan suka zauna, hannun su na cikin na junan su, sultana ce ta kwantar da kan ta a kafadar Sultan, ta share hawayen ta da ke zuba, ta ce,
"Yah Sultan ka ga rayuwar da iyayen mu suke aikatawa, a tunanin su dan jin dad'in mu suke yi, su na quntata rayuwar wasu bayin Allahn, su na haskaka ta mu,"
Sultan ya kasa magana har a wannan lokacin, wani abu yake ji ya tokare masa maqoshi ya qi wucewa.
Hannu ta sanya ta na ta shafa bayan shi, a hankali ya ke sauke ajiyar zuciya, cikin wata iriyar Murya mai rauni ya ce,
"Iyayen mu sun halaka, sun biye wa son zuciya, da son duniya sun halaka, ya Allah mai shiryar wa ka shiryar da su, ka yahe musu zunuban su,...sultana yanzu ina Daddy zai kai haqqin rayukan da ya salwantar?"
Wani irin kuka ne mai maqaqi da zafi a wuya ya turniqe Sultan, tausayin shi ya gama kashe zuciyar Sultana, wannan halin da zai shiga take tsoro tun farko, saboda ta san he is very sensitive kamar ta, har ma ya fi ta.
Su na nan zaune, Lawwali ya je wajen nasu cikin murna, ya sanar da Sultana mahaifin su ya janye neman Mubaraka da ake yi, amma fa ya na kwance a asibiti ba lafiya.