← Book details A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 93

Sashe 55

A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ku na ji na ko? Nan da sati guda nika so a yi auren mu da Sultana, in hakan bata faru ba, ku sani, har cikin dakin ta, zan shiga in dauke ta, domin babu abinda ba zan iya ba akan cikar buri na, kamar yanda kai ma ba abinda baka yi dan cikar burin ka"

"Lawwali d'iya ta ka ke son a yi wa irin wanga aure? Sati guda kamar d'iyar tallaka?"

Da sauri Hajiya Ikee ta ce,

"Kar ka ja mana magana, ka bari kawai a yi nan da sati guda din, kaga Lawwali, ka turo magabatan ka kawai a sa rana a yi komi a gama lahiya"

Murmushi mai kyau Lawwali ya saki, ya dauke qafar shi da ya dora a saman kujerar su, ya duqa gaban Hajiya, Ita kuwa ta yi baya da azama, dan ba ta so ma ya rab'e ta ko kusa, rabon da a dake ta ba zata iya tunawa ba, amma gata da girman ta, ta sha shaqa .

"Yauwa suruka ta, da kyau,bari na tai gida na sanar da iyaye na, gobe za su zo, a gobe nake so a saka rana, duk wanda ya lalata min shiri, zan lalata masa rayuwa, wanan alqawari na ne"

D'aga kai kawai Hajiya take, Gwamna kuwa kallon Lawwali kawai yake, ba komai, zai aurawa Lawwali Sultana, amma zai nuna wa Lawwali mulki gaba yake da dabanci................

*Hummmm kun amince Mulki gaba yake da dabanci?*

💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻

BY HAERMEEBRAERH

PAGE 41:

Zaune ya ke a kujerar da ke kallon ta a cikin office din na ta, su na fuskantar juna, hannun ta ya kama guda daya ya riqe a na shi, ya na kallon yanda gyararran farcen ta yake sheqi, cikin sassanyar murya ya ce,

"Ran ki shi dade, ki na ganin za ki iya zama da ni a duk inda na ajiye ki? Domin ba zan taba karbar gida ko wata alfarma da iyayen ki za su bani ba, ke sani Hajiyan ku da kyar ta yarda da auren mu, dan kawai ina diyan tallaka, ina so na yi komai da kuddi na, ina so ki goya min baya akan wannan, za ki iya?"

Tunda ya fara magana take kallon shi, ta gano gaskiyar maganar shi, ta kuma fahimce shi, ta na alfahari da kasancewar shi mijin da za ta aura, ya san yanda zai ya tsaya a matsayin shi a koda yaushe, baya manta tushen shi, sai dai ta na tsoron rayuwar wahala, amma indai da Auwal din ta ne ba komai, ba abinda ba zata iya yi domin shi ba, sai dai in abun  sab'on Allah ne, dan haka ta na ji a jikin ta, za ta iya taya shi cika duk wani burin shi, indai su na tare komai zai zo da sauqi da yardar Allah.

Cikin murmushin da ke nuna gaskiyar maganar da take son furtawa, ta d'aga kai, tare da janye hannun ta daga nashi ta ce,

"Na amince, na amince Zan zauna da kai a duk inda ka ajiye ni, duk inda ka sa qafa nan zan aje tawa, ni kai nake so,ba kudin ka ba,zan amfani da tushen ka ne, ba na iyaye na ba, kai nawa ne, ni taka ce"

Godiya ya mata, suka ci gaba da hirar su sama sama, ta na tsara takardun da za a ware tallafi zuwa ga mabuqata.

Bayan ya maida ita gida, suka ga motoci masu numfashi an Parker su a harabar gidan, Sultana na gani ta gane su waye a ciki, juya ido sama ta yi, ta amshe jakar ta a hannun  Lawwali da ke mata sai da safe,  sallama suka yi ta shiga gida, ta samu Hajiya Ikee a parlour su na hira da qawayen ta sai zuba musu qarya take, akan shaharar Lawwali a kasuwancin qasashen waje, duk da haka bata tsira ba, sai da  suka dinga yada mata da baqar magana, akan 'yar ta bata samu auren shugaban qasa ba.

Gaida su Sultana ta yi ta haye sama, ta na matuqar takaicin rayuwar qaryar da mahaifiyar ta ke gudanarwa.

A can parlour kuwa su Hajiya da qawayen ta sun gama tsare tsaren  yanda bikin zai kasance, a cikin qawayen ta akwai wadan da sun taba aurar da yara mata, sun yi alqawarin kawo masu gyaran jiki na musamman har gida.

Wani party da duk abinda Hajiya Ikee ta ke da buri ya faru a bikin nan, sun kammala tsara yanda zai kasance, a bangare guda kuma Lawwali ya gama hurewa sultana kunne kar ta yarda a yi wadannan abubuwan, kuma ta yarda da hakan, bata bayyana ma Hajiya abinda suka tsara ba ita da Lawwali sai bayan tafiyar qawayen Hajiya ne Sultana ta sanya  riga da skirt na bature, ta daure gashin ta a bayan ta, ta sanya takalmin ta ta sauka qasa, zama ta yi kusa da Hajiya,dauke da wayar ta a hannu, ta na dannawa ta na wa Hajiya bayanin da ya zama kamar dukan tsiya take wa Hajiyan.

"To kin ji yanda mukai da Auwal, Hajiya in ba gyaran jikin ba ni dai dan Allah ki bar zancen wasu party har kala hudu, ayi guda daya ma ya isa, ni dayan ma da za a bi nawa da ba za a yi ba, amma saboda kema ki fita kunyar qawayen ki za mu yi, yanzu yaushe Juwairah din za ta zo, na ji ana zancen gyaran jikin ta, irin na sudanis ya na da kyau" (ta na a garin Bauchi ga mai neman kwararriyar mai gyaran jiki irin na sudanis ku min magana)

"Na ji duk bayanan ki, kenan ki na nuhin shi Lawwalin ne yacce ba a yin komi?"

"Eh Hajiya, ko na kira shi ku yi magana, dan..."

"Ahhhhh ni ba na neman tashin hankali da ki ka ganni nan, magana ta qare, ai auren ku ne, in ma cewa kun kai a daura a kai ki haka nan ku kun ka sani, ni na hau sama, in Sultan ya zo ki kire min shi, ba mu da lokacin fita waje dan siyayyar kayan aure, in ma mun ce order za a yi, yanzu yaushe mun ka gama zabe zaben abubuwan da duk muke da burin saye? Ni dai wanga aure naku Allah dai shi hisshe ni kunyar abukkai na"

"Ai Hajiya ki kwantar da hankali ki, domin kuwa ya na da inda zai aje ni, ya ce ko cibi (tsokali) ba shi so a siye, ni kad'ai ya ke so a bashi, kin san hwa gidan da yake a nan shiyyar yake, kuma gida ne mai kyawu daidai misali, dama ni kin san rayuwar qarya bata gaba na"

"Hummmmm in ji me ciyon haqurra, ba ke ji komi daga baki na ba, ballantana ki hwadi mai, na hau sama, Allah dai shi gwadi mana ranar bikin"

"Ameen Hajiya ta"

Sama ta haye ta na ta maganganu qasa qasa, ita kadai ta san me take ji a zuciyar ta, na baqin cikin auren Lawwali amma ba halin bayyanawa, da ace wani na sauraron abinda mutum ke quqqullawa a zuciya, lallai da Hajiya Ikee ta shiga bala'i.

Ko da Sultan ya dawo, ya ji dadi matuqa da ya ga qanwar shi cikin farin ciki, fatan alkhairi ya mata sosai sannan ya je kiran da Hajiya ke masa.

*************************

Lawwali ne ke ta Video call da Mubaraka, sai tsokanar ta yake wai ta girma, ya ga ta na fari, ko bleaching take ne?

"Haba Yah Auwal, mi zai sani bleaching, baqi na mai kyawu na wallah, tau ko ba shi da kyawu ma yanda Allah ya yi ni haka nan zan zauna, sab'a halittar Allah haramun na, ina dai gyara jiki na da abubuwan da muke da su na gida shi na yas-sa ka ga na yi haske, Aunty Fateema ke yi min gyaran jiki, in ta yi,"

"Ohhhh Mubaraka, wanga bayanin kare kai, anya ba bleaching din ki ke ba? Tau ba wannan ba, ke san kuwa maganar aure na ta tashi ni da mutuniyar ki?"

Hamdala ta dinga yi, tare da babbaka dariyar farin ciki,

"Yah Auwal yaushe ne bikin? Kuma yushe za mu taho"

Dan jimmm ya yi, kafin ya gyara zaman shi ya ci serious dan ba ya so ta masa daru,

"Ke gane ko, saboda abubuwan da suka hwaru a baya, shi ne nicce ko za ku zauna ba sai kun...."

Cikin kukan shagwaba ta katse shi,

"Ni dai gaskiya sai na zo, bikin ku ne fa"

"Baraka na ki saurare ni da kyau, zan so a ce ki na nan, rashin ki zai zama kamar bani da dangi ne a wajen, amma ba zan iya sanya rayuwar ki cikin hatsari ba, hatsarin da nake ciki a yanzu ya hi Wanda kin ka sani,ki bani goyon baya, na miki alqawari hatta da hita ta daga gida, sai an miki video kin gani, kwanciyar hankalin ki da zaman ki lahiya ya hiye min komi ga rayuwa ta, dan Allah kar ki min taurin kai"

Cikin hawaye da sanyin murya ta ce,

"Yaushe ne bikin?"

"Asabar din ga me zuwa, yau saura kwana biyu,ki yi hakuri, i am very sorry, in ji ku turawa"

Cikin kama kunnuwan shi duka biyun ya ke bata hakuri, ran ta ya ɓaci , wai a ce sauran kwana biyu bikin shi, sai yau yake fada mata, amma ba komai, za ta girmama maganar shi, wataqila hakan da ya yi shi ne daidai, fatan alkhairi ta dinga musu, ta na murnar yaqe, qasan ran ta kuwa ta na jin ba dad'i , za ai auren Yah Auwal din ta guda ba ita.

Shi kuwa wasa da dariya ya dinga mata dan dauke hankalin ta, ya samu nasara kuwa dan ba su bar video call din ba sai da ya tabbata ta saki ran ta.
Chapter 55 · 0% Book details