← Book details A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 93

Sashe 72

A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jefi jefi suke hirar su, cikin nishadi, da kuma sabo, Taheer na matuqar jin dad'i da girmama wannan lokaci da hirar tasu baki daya, domin bai sani ba, ko na qarshe kenan da za su hadu har su yi hira haka, ko kuma akwai rabon haduwar su a gaba.

Sun isa garin zamfara da misalin qarfe 12 na rana, saboda gudu sosai da yake zubawa, hamdala Mubaraka ta yi, sannan ta kalli Taheer, ta na qoqarin motsa baki tai magana ta ga wasu sojoji na nuna ta, amma ba su tsaida motar su ba, sunkuyar da kan ta tayi qasa, dan ta san dalilin da ya sa suke nuna ta, da an basu dokar kama ta, yanzu an janye.

Sai da suka shiga gari sosai, Taheer na qoqarin daukan hanyar dajin nasu Mubaraka ta cire nauyin baki ta ce,

"Yah Taheer Dan Allah tsaya,"

Bai tsaya jin dalilin tsayawar ba, ya samu gefe ya tsaida motar, Sannan ya tattara duk wata nutsuwar shi ya miqa mata a hannun ta, d'an cizon leben ta tayi na qasa, cikin tsoron me zai je ya zo ta ce,

"Dan Allah ka fara kai ni gida wajen su Umma, dan ban sani ba ko Yah Auwal zai  bari na je na gan su, dan Allah kar ka qi, in ka qi kai ni na ga Ummana zan yi maka kuka, kuma Yah Auwal zai ga na yi kuka, kuma..."

"Tau ya yi haka nan, ban ce ki bani tsoro ba daga shigowa ta, tau yanzu in munka tai ya ji labari fa? Kin dai san in kin tsira ni ina ruwa ko?"

Cikin zumudi da murna ta ce,

"Ba abinda zai yi maka, Indai na ce ni ta ni nace ka kai ni, Please Yah Taheer ka kai ni naga su Umma" ta qarasa magana cike da shagwaba.

Taheer dai bai so ba, amma an sa shi na dole, tiryan tiryan take nuna hanya, har suka isa, ya na tsaida motar ta fita a guje, ta fad'a gidan,shiru ta ji ba kowa, daga iyayen nasu, har yaran.

Cikin sanyin jiki, ta dinga leqa d'akuna,ta fita, gidan da ke manne da nasu ta shiga, suka gaisa,mutane ne na kirki, masu dattako, tambayar su ta yi inda iyayen ta suke, nan suka sanar da ita Kareeman 'Yabbuga ce ta haihu, yau suna, dan haka su na can gidan Kareema.

Sallama ta musu da godiya ta koma wajen Taheer jiki ba kuzari, idanun ta sun cika da kwalla.

Hakuri ya bata bayan ta masa bayanin komai, ya ce in sun je, ta roqi Auwal, ya san zai kai ta da kan shi.

Hanya suka miqa sai daji.

A can dajin kuwa Sultana da Lawwali sai zumud'in zuwan mubaraka suke, sun yi kwalliya, sun sha ado gwanin ban sha'awa, kamar masu tarbar wani hamshaqin, su Barira da yaran Lawwali kuwa ,sun matsu su ga wace ce wannan yarinyar da ta shiga ran Ogan su? Ya take? Shin ta kai wadda za a gigice da so ko bata kai ba?

Abinci da abun sha, mahallin kwana, da duk abinda za su buqata komai an tanadar musu, su kawai ake jira.

Da misalin qarfe hudu da arba'in su Mubaraka ne a cikin jejin Oga Lawwali, tun daga hanya Mubaraka ta tsure, ganin mutane dauke da makamai, kamar masu zuwa yaqi,Taheer ne ya yi ta kwantar mata da hankali.

Lawwali ya kasa zama, sultana sai dariya take masa,Sultan da ke tsaye ya na kallon su, shi ma murmushi yake ta zabgawa, Lawwali na hango motar su No 4 ya zabura zai yi wajen, Sultana ta d'an kwalla qara kadan, juyawa ya yi ya kalle ta, ya ga ta dafe cikin ta, da sauri ya duqa gaban ta, ya na mata sannu, a lokaci daya kuma ya na juyawa dan ganin rabin ran nashi.

Sultana bata d'aga daga duqawar da ta yi ba sai da ta ga Mubaraka ta fita a motar, cikin washe baki, da murna, Sultana ta kwace hannun ta daga na Lawwali ta kwasa da gudu, ta nufi Mubaraka, suka rungume juna, mamaki da haushi ne suka kama Lawwali, kawai sai ya tsaya ya kama qugu, mutanen wajen kuwa me za su yi banda dariya.

Sultan kuwa har ya na duqawa dan dariya, ga dai Lawwali qatoto, maji da qarfi, amma Sultana yar firit ta masa wayo,Mubaraka gani ta yi ba shi da niyyar zuwa wajen ta, sai ta shanye dariyar ta ta daga murya ta ce,

"Yah Taheer mu juya kawai, ka kaini wajen su Umma na, tunda Yah Auwal din baya son gani na"

Wata harara Lawwali ya zuba mata, sannan ya taka da sauri, Itan ma da sauri ta ke zuwa wajen shi, rungume ta ya yi kamar ba zai rabu da ita ba, Ita kuwa kukan farin ciki ta saka, wani abu ya ji ya tokare masa maqoshin shi, wanda ya ke bayyana tsananin kewar ta da ya yi, ji ya ke dama zai iya kwaranyar da hawaye wataqila da ya ji sauqin abinda yake ji a ran shi,sake qanqame ta ya yi, ya na godewa Allah, da ya dawo masa da ita lafiya.

Sun jima a haka, sannan ya dago da kan ta ya juya ga mutanen da ke wajen, fuskar su dauke da kallo na sha'awar soyayyar da ke tsakanin yaya da qanwar shi.

"Kunga yanda  qaunata ta dawo gare ni lahiya? Na muku alqawarin zan maida ku ga iyalin ku lahiya, da yardar Allah, ba zan gaji da neman yahiyar ku a gare ni ba, ku yahe min, ko ba yanzu ba, ko bama tare ne, ku yahe min dan Allah"

Hayaniya ce ta karade wajen, Sultan na gefe ya na murmushin jin dad'in ganin shaquwa da aminci da ke tsakanin Oga da mutanen shi.

Ta gaban shi su Sultana suka wuce, shi ma ya bi bayan su.

Kafin su qarasa ciki Mubaraka ta gaida shi, amsawa ya yi, cikin sakin fuska, sannan ya tambaye ta ya hanya, ta bashi amsa da,

"Alhamdu lilLAAHi"

"To masha Allahu, sannun ku da zuwa"

"Yauwa Muna godiya"

No 4 da Lawwali sun tsaya daga waje, su na tattaunawa, kafin daga baya suyi sallama, ya tafi tsohon dakin shi, da ya samu baqi a ciki, amma still gadon shi na nan, a ciki, ga abinci nan da abun sha an aje masa.

Sai da Mubaraka ta fara wanka, sannan suka hadu dikan su a saman carpet suka ci abinci, su na yi su na hira.

Sultana kan ta ta sallama, ta sani ba zata tab'a samun kalar soyayyar da Lawwali ke wa qanwar shi ba, Mubaraka ta yi gaba, ta na bayan ta, ta yarda da hakan, kuma bai dame ta ba, domin dama kowa da matsayin shi .

Ranar Lawwali ya sha labarin Kano, har tsokanar ta ya soma yi da cewar,

"Ohhh su Barakana daga zuwa Kano a yi watanni, har an koma yin kananci, Sultyna, qaunar nan taki bata ko yadda ba wallah, gani takai yanzu ta zama bakanuwa"

Dariya sukai tayi, ita kuma ta na qoqarin kare kan ta, haka suka yi ta shan hira, tare damurnar dawowar ta lafiya.

*************************

Jirgi ya d'aga sai Saudiya, Isah kuwa wayar shi ya zaro a aljihun gaban rigar shi, ya na ta kallon hotunan Hansatu, wanda ya mata, ta na bacci, da wanda ya mata ta na aiki, duk bata sani ba, sai murmushi ya ke zubawa, ashe akwai ranar da zai kalle ta da soyayya a ciki? Ni kuwa nace ba soyayya ba ce sha'awa ce, ai da can da take son ka san da baka da komai, kai baka so ta ba, sai yanzu da ka ga ita Allah ya mata komai ka ke son ta.

Jirgi ya tsaya a king Fahad international airport, mutane na ta qoqarin sauka, Isah na tafe shima cikin ayari, wayar shi ya mayar a aljihu, ya riqe 'yar qaramar jakar kayan shi,ya sauka.

Wannan bawan Allahn ya gani daga nesa da shi, ya na masa murmushi, tare da yi masa sallama.

Mayar masa da sallamar shi ya yi, ya nufe shi, dan su je su d'auki kayan su, sai bawan Allahn nan ya nuna wa Isah qaramar jakar shi, ya sanar da shi ita kenan yake da, dan haka anan suka yi sallama, ya tafi, Isah kuwa dole sai da ya je daukan manyan jakunkunan da ya isa da su.

Ina can ina kalle kalle Hameeda ta shiga Saudiya (Allah ka amsa ka bama duk wanda be je ba ikon zuwa) sai na ji ihun mutane, larabci na tashi ko ta ina, kafin na koma wajen dan ganin me ke faruwa sai na hango askar sun kewaye Alhaji Isah, Isah ya durqusa qasa ya na rantsuwa tare da baza musu Hausa, ya na bayani ba na shi bane.

Ko da na leqa da kyau, sai na ga wani abu fari tasss a leda guda hudu, da na kasa kunne da kyau, sai na ji ana fad'in koken ne abun, hankali na ya tashi nai baya, ina leqe daga nesa, bawan Allah'n nan na hango cikin tsananin damuwa da b'acin rai ya na kiran

"Shit, shit, this man na mumu, de don catch am"

(Wannan mutumin Wawa ne sun mama shi)

Da sauri ya rataya  jakar shi ya bar wajen, a cikin gudu-gudu, sauri-sauri.

Tuni an sanqame Isah, ya na ihu ya na kuka, sai fadi yake ya na kumawa.

"Goro ne kaɗai nawa na rantse, koken din ban san na waye ba, dan Allah ku maida ni Nigeria ba zan sake safarar goron ba,ni Ko zuwa ma ba zan sake yi ba"

Gaba daya fuskar Isah ta sauya, cikin qanqanin lokaci ya zama kamar ba shi ba, saboda shiga tashin hankali.

Ba su tsaya da shi ko ina ba sai wajen ajiye masu manyan laifuka.

Isah na nan na kuka, da roqon gafara, tare da qoqarin bayyana musu gaskiyar shi, amma ba mai sauraron shi, balarabe d'aya aka kawo wanda ya ke dan jin Hausa, duk wani bayani da Isah yake yi, abu dai na komawa kan shi ne, tunda ya kawo goro ta boyayyiyar hanya to tabbas koken tashi ce,

"Innalillahi, yau na shiga uku, na lalace, wai da wane yare kuke so na muku bayani ne, ba tawa bace,"
Chapter 72 · 0% Book details