← Book details A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 93

Sashe 42

A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kafin duhun dare ya shiga Sultana ta ji jiki,zazzaɓi mai mugun zafi ne ya kama ta, ba abinda take banda rawar sanyi, Hajiya Ikee ta shiga bangaren nasu ta tarar da Sultana kwance ta lullubu, sai rawar sanyi take, cikin tsananin damuwa ta isa gaban ta, ta na taba goshin ta, dan ture hannun ta sultana tayi, sanan ta juya baya, Hajiya Ikee, waya ta fara yi, akan a kira likita yanzun nan, cikin rawar murya sultana ta ce,

"Ko ya zo ba abinda zai iya min, ...ba na so ya zo,... ki barshi kawai, .....ki je ku ji sakamakon zaben da kuka riga kuka san ku ne ma zaku yi nasara"

Cikin washe baki, da rashin gane mai Sultana ta ce, ta miqe,

"Bari in tai, nahi son a hwadi komai a gabana gashi can ana ta hwadi, har yanzu akwai mazabun da ba su kai sakamakon su ba, da alama za mu samu nasara, mun godewa Allah, bari na tai, in likitan ya zaka sai mu taho a baki magani ke jiya? Allah shi yi miki albarka,"

A hankali ta amsa da

"Ameen"

Shin addu'ar irin su Hajiya ma na cin mutum ne? Ni Ko na ce uwa dai uwa ce, komai lalacewar ta, in ta yi addu'a inshaa Allah, Allah zai amsa, zunubin ta daban, addu'ar ta daban, da ace mummunan kalami zata yi ga dan ta zai same shi,kamar yanda Lamishi bata da burin da ya wuce ta zagi yaran ta, ta musu baki.

Likita ya zo da misalin tara na dare, ya bata magunguna, tare da bata shawarwarin rage tunani,domin jinin ta ya hau kadan, murmushi kawai ta yi masa ta yi godiya, Hajiya Ikee ta raka shi, ta koma wajen ta, dan dai ta san zabe kamar sun ci shi sun gama, amma me ke damun gudan jinin ta har jinin ta ya hau?

Cike da damuwa ta koma dakin, hawaye ta gani daga idon sultana ya na gangarewa a saman pillow duk da cewa  idanun nata na rufe ne.

Zama ta yi a gefen kan ta, tare da sanya hannu ta jaye gashin ta da ke gefen fuskar ta, ta shafa kan nata cikin kulawa da soyayya, irin ta uwa, cike da tausaya wa ta ce,

"Sulty Baby mi ka damun ki? Hawan jini? Mi ya maki zahi, da uwar ki da uban ki, ga dan uwan ki masu son ki? In akwai abinda ki ka so duniyar ga ki hwadi min ki na samun shi ko menene shi kuwa"

A wahalce Sultana ta daga ido ta kalli mahaifiyar ta, wadda take bata tsoro, tsoron gaske ma kuwa, dan bata san wanne ne halayen ta boyayyu ba kuma bayan wanda ta ji ta sani, cikin qunar rai ta ce,

"Kar ki damu,Wataqila wannan ciwon shi ne ajali na, wataqila kuma a hankali Allah ya yaye min, amma ku ba za ku iya min abinda nake so ba"

Cikin tsananin damuwa Hajiya Ikee ta sake mannewa a jikin Sultana, ta na jan ta jikin ta, da sigar lallashi, tausayi, soyayya, da tsantsar qauna,

"Habaaa Baby Sulty, wace irin magana ta wagga ki ke yi? Kin San dai ba abinda ki ke nema a duniyar nan ki rasa daga wajen mu, akan su wa muke fadi tashi dan mu tara abin duniya? Duk ba dan ku muke yi ba? Ki sanar da ni abinda ki ke so, yanzun nan zan sa a kawo maki shi"

"Hajiya kar ki damu, na fara lura da kuma sanin abinda za ki iya da wanda ba zaki iya ba, amma wannan kam na san ba zan same shi ba, Dan Allah ki bar wannan maganar ki tai an kusa sanar da sakamakon zabe"

"Rayuwar ki is more important to me, than anything else in the world my dear just tell me what you want and I will get it done for you yanzun ga"

Idanun sultana zafi suke kamar an zuba mata yaji, a hankali ta ware su a fuskar Hajiya Ikee wadda ta nuna tsantsar damuwa da gaskiyar maganar ta, na bawa sultana duk abinda take so.

"Auwal....Auwal shi ne abinda zuciya ta ka so, Auwal na ke so ku aura min, indai har da gaske ki ke za ki yi min duk abinda nake so, shi ne rayuwa ta, in ku ka hana ni auren shi Hajiya zan mutu"

Miqewa tsaye Hajiya Ikee ta yi tana kallon Sultana da wani irin kallon kan ki daya kuwa?

"Wane Auwal ki ke nufi? Lawwali driver? Ki na da hankali kuwa? Na haifi yarinya kamar ki, kyakkyawa, mai ilimin arabiyya da boko sannan ta b'ige da auren jahilin driver? Ki na hauka ne?"

"Hajiya ba fa jahili bane masanin qur'ani ne sosai, masanin qur'ani kuwa ai ba mai kira nai Jahili"

"Sai ni, ni zan kire shi jahili tunda banga alamar shi na aiki da shi ba, qur'ani ya hana neman ilimin boko ne? Namiji har namiji ace driving shikai? Ba da ni ba, kar ki bata min rai, ki nemi komai a waje na, amma banda wanga, yau ga zancen banza zancen yohi, to bari ki ji, kar ma ki kuskura ki wa mahaifin ku maganar ga, dan rai nai sai yahi nawa ɓaci, ba abinda ya tsana sama da talauci ga rayuwa tai, ba zai so ya miqa ki gidan wahala ba, na hwada maki tanadin da nake a kan ki, shi na ki ke debo min wahala? Sam ba zai yu ba,"

Ta na ta Masifa ta bar dakin, a qasan ran ta bata so suka rabu ta haka da diyar ta ta ba, musamman yanzu da bata da lafiya.

Sultana kuwa ko kukan ta kasa, tabbas sai yanzu ta fahimci me Auwal ke nufi,abinda babba ya hango dama an ce yaro ko ya hau rimi ba zai hango ba, ya riga ya fahimci ba za a bashi ita ba, ita kuma ta zaci son da iyayen ta ke mata zai taimake ta a bata wanda take so.

Ta na nan kwance ido biyu ta ji ana taken Nigeria, ana iface iface, a cikin gidan, rintse idanun ta tayi cikin qunar zuciya ta ce,

"Ban san sanda tallakan Nigeria zai bude ido nai ba, ban san sanda tallakan Nigeria zai fara addu'ar samun shugabanni wanda suka cancanta managarta ba, ba wanda suka so ba, ban san sanda tallakan Nigeria zai gyara tsakani nai da Allah ba, har Allah ya ji tausayin shi ya raba shi da shugabanni kamar su Daddy, ya Allah ka kawo mana qarshen wannan rayuwa mara aminci da muke ciki, ya Allah ka sa qasar mu Nigeria da duniya baki daya ta zama waje mai aminci ga bayin ka,"

"Ameeen Sulty Baby, ya jikin naki? Hajiya ta je ta na ta hwada, ban san akan mi take magana ba dai, amma na ji ta na akwai tanadin da ta yi akan ki, ko kin san akan mi taka magana?"

Murmushin da be kai ko ina ba ta yi wa Sultan da Ke bin ta da kallo, sannan ta ce,

"Ka manta mun je gidan dan takarar shugaban qasa?  To tun daga can ta fara ciniki na, ka shirya kaima za a yi naka kwanan nan, da ta samu wadda ta hito gidan kuddi za a saishe ka, Yah Sultan ina da wanda nika so, ta ce kar ma na bude baki na sanar da Daddy, sun gama maganar wanda za su bawa ni"

Hawaye ne suka fara tsartuwa daga idanun ta, ran Sultan ya ɓaci matuqa, zai d'auki komai akan shi, amma ba zai taba jure ganin Sultana cikin mummunan hali haka ba, nawa take har da za a ce hawan jini ya kama ta?

Cikin fushi ya bar d'akin, ta na ta kiran shi bai juya ba.

Ya na fita wayar ta na daukan ringing, da kyar ta janyo ta, ta na ganin sunan Auwal,  hannun ta ya d'au rawa, bakin ta na rawa saboda kukan da ya taso mata, ta na dauka kuwa ta fashe da kuka, Lawwali na jin kukan ta, ya ji wani abu mai qarfi ya daki zuciyar shi, ba ya son jin haka saboda ita, ba ya son jin damuwa da damuwar ta, amma ya kasa jurewa sai da ya tausasa murya ya ce,

"Ran ki shi dade ki yi min afuwa,na shiga matuqar busy ne, inda na tai ba network ,shi yasa ban dauka ba,amma ki yi hankuri, gani na dawo gida,dan Allah ki dena kukan"

Cikin shagwaba ta ce,

"In ka sake tafiya inda ba Network zan yi fushi da kai mai tsanani, ba zan sake kula ka ba"

Siririyar dariya ya yi, Sannan ya ce,

"A min ahuwa, in ki ka dena kula ni, ashe qarshen rayuwa ta ne ya zo, ba ke ba Mubaraka, lallai da zan zama kamar gunki, domin zan zam ba rayuwa a tare da ni"

Itan ma dariya ta saka, wadda ba zata iya tuna sanda ta yi dariya ba a ranar gaba daya.

"Na maka alqawarin sai ka mallake ni a matsayin matar ka, kuma sai mubaraka ta dawo gare mu lahiya"

Kalaman ta na qarshe ba karamin faranta ran shi suka yi ba,har ya ji sabon lamari game da ita...............

*Tambaya ta anan shi ne, Sultana da ke yi wa Lawwali alqawari, ta manta maganganun Hajiya ne?*

💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻

BY HAERMEEBRAERH

PAGE 34:

"Dakata min Sultan, kai har ka isa ka taho ka yi min titsiye? To bari ka ji, kai kan ka, ina nan na tanadar maka wadda za ka aura, lokaci nika jira, ta na kammala digirin ta ta dawo qasar ga za a daura muku aure, diya ce ga minister'n tsaro, kuma babbar diyar shi, na duba wayar ka tass na ga duk matan da ka ke mu'amala da su, duk ba ya wuce gaisuwa, Ita dai nigga ku na hira jefi jefi, tunda Allah ya sa hankalin ku ya gamu waje guda, Daddyn ku ya ma iyayen ta magana, kuma sun yi na'am, ka shirya, ana gama auren Sultana naka za a yi"
Chapter 42 · 0% Book details