← Book details A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 93

Sashe 89

A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Biki fa ya yi biki, daga gidan ango har amarya kowa ka gani bakin shi a bude ya ke da fara'a, ga abinci daidai gwargwado ba yunwa, Hajiya Ikee ta yi matuqar mamaki yanda ta ga qawayen ta sun qi halartar bikin, wadan da ta ke rainawa a baya, take zaben wasu akan su, su ne suka je, su ne suka had'a mata gudun mawar da bata tab'a zata ba.

Wannan karon Sultan bai gayyaci kowa a abokan karatun shi ba na can qasar waje, duk da cewa Sultana ta so hakan ya faru matuqa,amma ba su da kudin da za su yi hidimar da suka gudanar a bikin Sultanan, sai dai wasu daga cikin abokan nashi da suka ga sanarwar auren nashi a shafin shi na facebook, sun zo da kan su, ba tare da ya san za su zo ba, ya yi matuqar farin ciki da hakan kuwa, a qalla ya tabbatar da cewa in wani na son ka dan kai wani ne, to wani na son ka ne domin Allah.

An daura auren Mubaraka da Sultan akan sadaki nera dubu hamsin,wanda yayan Hajiya Ikee ne ya bayar a matsayin tashi gudunmawar.

Lamishi ji take kamar za ta rabu da jaririyar yar ta ne, domin kuwa a wadannan watannin da suka yi a tare,ta nuna wa Mubaraka gata kamar na qaramar yarinya, duk wata kulawar da bata samu ba a baya Lamishi ta yi matuqar qoqari wajen bata a yanzu, Ita kuwa sai ta ninninka akan biyayyar da take wa iyayen nata.

'Dan Talo dai ba shi da kudin kayan dakin amarya, dan haka ya dinga fafutukar yanda zai ko bashi ne ya had'a a yi mata, sanda Sultan ya samu labari daga bakin Sultana, da kan shi ya yi takakkiya, ya sanar da Dan Talo kar ya samu damuwa, domin kuwa Mubaraka kawai suke buqata, ba kayan daki ba.

Dan Talo ya yi kukan dana sani, har ya godewa Allah, da ace shi mutumin kirki ne a baya, wanda ya kafu da qafafun shi akan neman kudin da zai rufawa iyalin shi asiri,da yanzu bai zo ya na shiga halin qunci akan ba shi da sisin sa wa yar shi komai a dakin ta ba, Lawwali kuwa a gefe guda ya na batun siyan kayan d'akin Mubarakan shi Sultan ke masa bayanin inda za ta zauna bata da buqatar kayan daki, komai akwai, dan haka kar ya damu da kashe kudi, se dai in ya na ganin Barakan shi ta fi qarfin kwana a tsoffin kayan d'akin shi, dariya Lawwali ya yi, ya ce

"Wanne kayan ne tsoho? Dakin da kullum mamaki nake wai d'akin namiji ne kamar na budurwa tsabar yanda aka qawata maka shi?"

Murmushi kawai Sultan ya yi, dan tunawa da Daddyn su da ya yi, shi ne ya tsaya tsayin daka dan ganin komai ya wadatu a dakin shi.

Da yamma kuwa Mubaraka na ta kukan rabuwa da iyayen ta, Lawwali ya shiga cikin gidan,ya bada Umarnin in an gama shirya amarya a sanya ta a motar shi, shi zai kai ta har dakin ta kamar yanda ya ke da buri a rayuwar shi.

'Yabbuga ce ta leqa kan ta waje cikin ladabi ta ce masa

"An qare shirya ta, tun dazu ba ta son hitowa na, su na nan su na kuka ita da Lamishi"

Lawwali ne ya sake dubawa da kyau,dan ya ga shin da gaske yau 'Yabbuga ce ke masa magana? Wani murmushi ya sauke, mai sanyi, a cikin ran shi kuwa ya ce,

'Alhamdu lilLAAH, na tabbata yanzu rayuwa ta ta yi kyawu yanda ya kamata, ba dan ta dena jin tsoron na ba, sai dai alamar nutsuwa da ta bayyana ga huskata har ta jawo mutane yanzu suka daina shakkata, sai ma soyayya ta da ni ke gani ga ijiyar su (idanun su)'

"Me ka ce?"

"Cewa na yi bari in shigo in hito da amarya"

Cike da murna 'Yabbuga ta koma ta sanar da su Ta Yahai shigowar Lawwalin, fita mata suka dinga yi a dakin, Mubaraka na zaune a qasa, ta ɗora kan ta a cinyar Lamishi da ke ta tsiyayar da hawaye.

"Dan Allah ku bar wanga kukan, rayuwa fa dama haka take,kowace mace sai ta bar gidan iyayen ta in lokaci ya yi, kai watarana ma duniyar za mu bari gaba daya, sai mu manta da hankulan mu? Ko za mu manta da hakuri ne akan rashin masoyan mu? Ballantana hwa duk wadda ke son ganin wata cikin ku nerar ga dari biyu ta ishe ku, ku tai ku dawo, to mi?"

Mubaraka ce ta daga kai ta kalle shi, hawayen ta da ke zuba kamar pampo na taba zuciyar shi, hannu ya miqa mata, da gudu gudu kuwa ta isa gare shi ta fada jikin shi,Lawwali kasa jurewa ya yi, sai da ya zubar da hawaye shi ma.

Mutanen unguwa 'yan gulma sai leqen su ake, wasu har dauka suke a waya, a haka Dan Talo ma ya shiga, ya sanya wa Mubaraka albarka, Mai Buruji ma ta na kuka ta sanya albarka, Lawwali ya share mata hawayen ta, ya share nashi,suka fita daga gidan,motocin da suka je daukan amarya har sun yi gaba, dan an sanar da su Yayan Amarya ne zai kai ta da kan shi,Sultan kuwa da ya ji labari, ya ce, dama ya san za ai haka.

Ya rage motar Lawwali kawai a wajen wadda  zai kai qanwar shi dakin miji da ita.

Bayan ya sanya ta a mota ne, ya tada motar, sai GRA, gidan tsohon Gwamna Halliru Murtala Gusau.

Tafe suke Lawwali na yi wa Mubaraka wata iriyar nasiha da ke ratsa dukkan kafofin jiki da ruhin ta, kuka kawai take saboda yanda take jin kalaman shi kamar mai mata bankwana, sun shiga kwanar da za ta sada su da GRA ne Lawwali ya ga wannan tsohuwar da ya saba gani kullum ta na zaune a bakin titi, ta miqe, ta yi wurgi da mayafin kan ta, abun bai gama bashi mamaki ba sai da ya ga ta zaro bindiga, ta nufe su ta na dingisa qafa, a sannan ne ya kula da kyau, ba tsohuwa bace, No 1 ne, nan take kuwa Lawwali ya take motar da gudu zai bi ta kan shi, kafin ya qarasa No 1 ya sake harsashin bindigar shi a qirjin Lawwali, nan take motar kuwa ta bi ta kan No 1 ko shurawa bai ba.

Mubaraka kuwa ganin yanda jini ke zuba a qirjin Lawwali kuma a haka ya na qoqarin tsaida motar sai ta rikice, motar na gama tsayawa, ta bude ta zagaya ta wajen Lawwali ta na ta kuka, tare da kwalla ihu, ta na neman taimako, wajen shiru ba kowa.

Kama shi ta yi, ta na ja, da kyar ta samu ta fitar da shi daga motar,  ta na kuka

"Yah Auwal ka tsaya, yanzu za a kawo mana taimako, ya Allah ka tausaya min kar ka jarabce ni da rasa yaya na, ya Allah ka zama gatan mu,kar ka raba mu a daidai lokacin da muke buqatar shi, wayyoo Yah Auwal Dan Allah ka bude idon ka, ka dena ruhe shi, a taimaka manaaaa"

Muryar ta ta dashe saboda kukan da take, su na nan zaune, masu gadin unguwar suka iso, da 'yan sanda, domin sun ji qarar harbi a wajen, ganin halin da Mubaraka ke ciki riqe da Lawwali a hannun ta ne ya sa nan da nan suka nufe su, wasu kuma su ka hau duba gawar No 1, a motar 'yan sanda aka saka Lawwali, sai bayan an saka shi a motar ne Mubaraka ta tuna da waya, a guje ta nufi motar su, ta na kuka, mai ban tausayi, ta dauki wayar ta ta kira Sultan,kukan ta ya hana shi fahimtar komai, sai wani mai gadi ne ya karba ya masa bayani, salati kawai Sultan ya dinga jerawa.

A guje ya bar gidan, Sultana da Hajiya Ikee da wasu cousins din shi da suka zo bikin, sai tambayar shi me ya faru suke, bai amsa kowa ba ya bar gidan.

Sultana kuwa ji ta yi abun da ke cikin ta na mata motsi sosai, har sai da ta samu waje ta zauna, ta na mamakin irin motsin da yake ta yi.

Ko da Sultan ya je wajen bai tarar da motar 'yan sanda ba, sai Mubaraka da ke zaune dabar a qasa, ta na kallon waje d'aya, ba ta uhummm, ba ta Ah ah, ta gaji matuqa, ta kai qololuwa wajen gajiya da kukan, ya na ganin ta ya nufe ta da gudu ya rungume ta, kwantar da kan ta ta yi a kafadar shi kawai, ta yi shiru.

"Mubaraka mu je asibitin mu ga ya ya ake ciki"

Ba tare da ta amsa masa ba, ta miqe, ya taimaka mata, ya sanya ta a motar shi,kayan ta farare tass na amare da suka gaji da kyau sun yi face face da jinin Lawwali, d'aya daga masu gadin ne ya sanar da su asibitin da suka sanar za a kai Lawwalin.

A haka suka isa asibitin, ko da suka je, sun tarar 'Yan sanda na tsaye a dakin da aka shigar da Lawwalin.

Likita da nurses na fitowa daga dakin suka sanar da mummunan labarin da ya daki zuciyar Mubaraka ta tsaya cakk, ta dena aiki na wasu seconds, sannan ta ci gaba da bada jini ta kowanne lungu da saqo na zuciya da sassan jikin ta, nan take ta yanke jiki ta fadi a wajen.

Sultan ya na ganin tashin hankali a wannan ranar,ranar da ya kamata ta zama ranar farin ciki, ranar murna, ranar kafa tarihi mai cike da nishadi, yanzu ta koma rana mafi baqin ciki, da muni a wajen su baki daya.

Sultan rasa inda zai saka ran shi ya yi, ta ya zai fara sanar da wannan mummunan labarin? Wanne hali qanwar shi za ta shiga? Mahaifan Lawwali fa? Ya na nan zaune aka shige da Mubaraka dakin kula da marasa lafiya na gaggawa.

Qoqarin ceto ran ta likitoci ke ta yi,abun na neman fin qarfin su, Sultan kuwa addu'a kawai yake yi, Allah ya jiqan Lawwali ya sanya wa duk wasu masoyan shi hakuri da juriya, tare da danganar rasa shi.
Chapter 89 · 0% Book details