← Book details A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 93

Sashe 20

A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariya ce ta kwacewa sultana , ta ce,

"Mubaraka kenan, ni da ko saurayi ban da wa zan aura?"

Zaro ido Mubaraka ta yi cike da mamaki, sannan ta ce,

"Aunty ko dai ke ta baki kula su? Ko ni din nan, maza na cewa su na qauna ta, balle ke, aunty Sultana ke gane ki kuwa? Wa zai ce ba shi son mace kamar ki?"

Murmushi kawai sultana ta yi, domin ita maganar ma saurayi ko miji bata gaban ta tun da can, a kullum damuwar ta be wuce ta ga yanda zata fara aiki dan ta koyar da al'umma abinda Allah ya sanar da ita ba, sannan ta bude gidauniya ta na taimakon mutane, to yanzu ta samu buri d'aya ya cika, wataqila za ta duba maganar aure a nan gaba, domin maganar lecturing da take son yi da alama ba zai samu ba.

Lokaci Mubaraka ta kalla, ta ga ya tafi sosai, har hudu da rabi,da sauri ta miqe tsaye,

"Subhanallahi, na manta Yah Auwal na waje ya na jira na, na tsaya surutu"

"Jiran ki kuma? Yanzu ki na nufin sai mutum kamar Auwal ya tsaya jiran ki? Namiji ne fa, ba su son jira"

Murmushi mai dauke da tsantsar so da qauna Mubaraka ta yi, sannan ta ce,

"Aunty Sultana, ina so ki sa ido akan Yayana da kyau, a hankali za ki san wane ne wannan Auwal din, Yah Auwal daban shike cikin maza"

A bakin qofa Sultana ta tsaya, dan sauraron Mubaraka ba ta san ma ta na bin ta ba.

"Zan sa ido na biyu akan Yah Auwal din ki Mubaraka, sai gobe, ki gaishe da Lamishi da jiki"

"za ta ji"

A gurguje ta fita daga katafaren gidan, a zaune ta tadda shi a saman kujera ya na bacci, tsinke ta samu ta saka masa a hankali a qofar hanci, ai kuwa atishawa ya saki mai qarfi, miqewa ta yi ta na dariya, daga baya ta kama kunnen ta ta na bashi hakuri, kama ta ya yi, ya daga hannu kamar zai mare ta, cikin wasa ya san daki kuncin ta kadan, suka yi wa masu gadin qofar gidan da ke kallon su cikin sha'awa sallama, suka fita.

Sultana bata bar jikin window ba har sai da ta daina hango su, fuskar ta dauke da annuri ta fada wanka.

A hanya kuwa Mubaraka ta kwashe duk yanda sukai da Sultana ta sanar da Lawwali, murna a wajen shi kamar har ta ce masa ta na son shi.

Ko da suka isa gidan shi, sai da suka ci suka sha, ta yi wanka, ta maida kayan da ta cire, suka dauki yar qarama kuma tsadaddar motar shi da gwamna ya sai masa, tunda yanzu ba ya cikin tawagar su ta daji,ya na buqatar mota, ko da fitar gaggawa ta kama.

A motar suka isa gida, kafin su shiga Mubaraka ta lallaba shi ya sai balangu mutumin Lamishi, har da kaza da madara, suka isa.

Ko da suka shiga gidan shiruuu, ba kowa, ajiye ledojin hannun ta tayi, ta lelleqa, ba kowa da gaske, to ina suka je? Ina ita Lamishi me jinya?

Tsaki ya ja, sannan ya zauna su ka hau hira, ita kuma ta duba ko akwai abincin dare, ko se ta ɗora, gani ta yi akwai a flask, da zai ishe su, na gidan gwamna ne, dan haka ajiye naman ta yi, ta ce in sun dawo daga duk inda suka je an ci.

"Ke da kissani? Ta na can yawon gulma"

"Yah Auwal ina fada maka ka dinga tausasa harshen ka ga uwayen ka, umma ka ke fadin ta tai gulma"

Irin abun nan ya yi na 'yan mata masu yanga,  ya murguda baki, ya yi fari, shi a dole an masa fada.

Dariya ta yi, ta ce,

"Dama Aunty sultana ta gan ka"

"Ki na ganin duk mun ka hadu in yi mata haka nan? Za ta so ni?",

"Walle ba ruwa na, in tayi shiri shiri kwancin kwana ta shere ka mari, ka gan ka kuwa? Awab-budurwa wallah"(ba ruwa na in ta yi kwance kwance ta kwad'a ma mari, ka ganka kuwa kamar budurwa)

Dariya sukai ta yi, har Dan Talo ya shiga gidan a gaggauce, buta ya dauka dan zagawa, Lawwali na ganin shi,ya miqe ya daure fuska,

"Lawwali, ai na hango motar ka ne, muna dawowa daga garkar Yahai, nicce bari na zo, ko zan samu wani abu, bari na hito daga yauce, (bayan gida)"

Ya na fadawa bayi, Lawwali ya zaro dubu biyar ya ba Mubaraka Ya ce,

"Amshi ki ba uban nan nawa me kwadayi, in ya hito daga tutun wahala, ban jira nai wallah, na tafi nemo yaki halal yaki haram din da suka so"

Magana ya ke kamar da wasa, amma cikin zuciyar shi zafi take, a ce iyayen ka basu damu da inda ka ke samo kudi ba, kuma da ganin Lawwali sun san dai ba aikin jima  yake ba ko kafinta, ko dako, balle aikin office, Amma kullum nema suke a wajen shi, kuma basu yake, manyan kudi ma kuwa, se kace wani babban ma'aikaci, ko babban ma'aikaci watarana ya na zama bai da shi.

Mubaraka da ke tsaye cikin tausayin Yayan nata ne ta amshi kudin, ta na so ta bashi ko da hakuri ne, dan ta san ya yake ji, amma ya fice, tun kan ta ce komai.

Dan Talo da ya fito ya ga ba Lawwali, a zaton shi ya tafi ne, nan da nan kuwa ya hau ashar, ya na kiran lawwali da sunaye marasa dadin ji.

"Gashi hwa, ya bar maka kuddin, ya dai tafi ne an kira shi ga waya"

Baki Dan Talo ya washe, ya na kuma godiya, soke su ya yi, a sassan aljihun jikin shi, sannan ya fita.

Girgiza kai Mubaraka ta yi kawai, ta na nema ma ahalin ta shiriya.

***********************

Su Lamishi kuwa su na gidan Isah, Yabbuga nan ta tattare su suka fada, har da Asshibi, yau ta samu leqa gidajen shiyya, duk gidajen mutuncin unguwar ba d'aya da Yabbuga ta raka ta, sai nasu ya nasu.

Qarshe da suka shiga gidan Lamishi suka gaisa shi ne suka rankaya gidan Hansatu gaba dayan su.

Sun tadda Isah na gida, sun gaisa su na ta wani hira kamar sun samu abokin su, kafin daga baya ya fada daki, da fita zai amma ya fasa,Hansatu kuwa ta gama dafa shinkafa da wake, ya ji yaji mai dadi, ga man ya samu matsayi har albasa aka saka masa.

Nan dai Yabbuga uwar kwadai ta hau yaba qamshin girkin, Ita kuwa Hansatu jin haka ya sa dole ta debar musu, haqqin su ne sun ji qamshi tunda akwai ta zuba musu. (Da damar mutane rowa ta saka ba su damuwa da haqqin maqoci, a yi girki mai dadi, me qamshi a lashe a sude hannu, wasu ma maqotan su talakawa ne, amma ba za su sammusu ba, duk da dai yanzu duniya ta sauya, ka na iya bawa mutum dan Allah da haqqin maqotaka, ya ce dan a san ka na cin dadi ka bayar, amma ka tsarkake zuciyar ka ka bayar, mutum shi ya sani da ya maka sharri, sannan wasu in suka ga ana basu, sai su fara zaqewa da roqo, har mutum ya koma boye abu ya na rowa, da ace kowa zai gyara da an zauna lafiya)

Su na kai loma su na zuba hira, rabi da kwatan hirar bata wuce ta auratayya ba, Isah na daki ya na jin su, ya na kuma jin dadin hirar saduwar auren da suke ta yi, Hansatu kuwa sai fada masu take, su yi a hankali mijin ta na ciki, Matar Yahai na bude baki kuwa, sai da ta fadi maganar da ta sa Hansatu shiga wani irin hali na matsananciyar kunya, su kuwa suka sheqe da dariya, Asshibi kuwa sai ta ji matan sun kwanta mata a rai,dan kuwa wajen hirar banza ta fi kauri dama.

Hansatu ta gaji da jin maganganun su, masu sanya ta kunya, cikin tattausan lafazi ta ce,

"Wai ku in tambaye ku? Me ne ne jigo a rayuwar aure ne?"

"Saduwa mana heeeeee casssss"

Suka yi shewa tare da tafawa, Isah kuwa dake daki, har sake gyara kwanciya ya yi, ya na sauraron su.

Zama Hansatu ta gyara ta ce,

"Tabbas saduwa daya ce daga jigon da ka sa a yi aure, amma ba ita kad'ai ba ce  jigo a gidan aure  ba, abubuwan na da yawa, su din ginshiqai na da ka riqon aure, in babu su da tuni aurarraki da dama sun watse.

Na farko akwai yin auren ma shi kan shi domin Allah, sannan Yarda, riqon amana, saduwa, ladabi, biyayyah, soyayya, qauna, tausayi, ciyarwa,tufatarwa, wajen zama,girmama juna, qimanta juna, mutunta juna, tausayawa juna,iya girki,da wasu mahimmai dai.

Wa'yanga abubuwa in suka hadu, aure ya ginu, ya zauna kenan sai dai in ajali nai na ya yi.

Na fahimci me ya sa kuke ganin kamar saduwa ita ce kad'ai abinda ka riqe aure, ba komai na yasa ba saboda fadi da ankai cewar,Aure shike hada wata alaqa, tsakanin mace da namiji, wannan shi na  nufin hade rayuwarsu ta zama daya haka nan kuma makomarsu ta kasance guda daya. Kowacce irin al'ummah akwai irin matsayin da ta ba wa aure, Aure a musulinci wani daurine da shike halatta wa ma'aurata mace da namiji jin dad'i da junansu, ta hanyar saduwa  irin ta jima'i,da sauran mu'amaloli na jin dadin saduwa, Allah (subbahanawu wa ta'ala) ya halicci mace daga hakarkarin namiji ya kuma sanya soyayya da tausayi a tsakaninsu.

Wannan babban dalili ne da zai sa ku ga kamar saduwa tahi komai a aure, amma duk wadda bata iya kula da miji ba, ta hanyoyi da dama, musamman iya girki, tsafta, kwalliya, ladabi da biyayya, bata iya magana ba, komi yattaho bakin ta hwadi takai, to wallahi mace na da saura a gidan aure ba ta iya komi ba"

Gaba dayan su har Isah da ke kwance, hansatu ta basu mamaki, ba mace ba ce me yawan Suratu, amma sai gashi yau ta yi magana cikin ilimi da nutsuwa da fasaha.

Mai Buruji ce ta fara yunqurawa ta miqe ta na sude hannu,
Chapter 20 · 0% Book details