← Book details A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 93

Sashe 37

A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lawwali na nan kwance wani tunani ya fado masa, kamar wanda aka mintsina haka ya miqe, ya na murmushi, cikin wata iriyar murya Lawwali ya furta,

"RAN KI SHI DADE MASOYIYA SULTANA, MASOYIN KI AUWAL NA TAHE"

*HUMMMM LAWWALI KAR KA DAU FANSA AKAN SOYAYYAR GASKIYA PLSS😭😭😭😭*

💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻

BY HAERMEEBRAERH

PAGE 30:

"Alhamdu lilLAAH, a qallah Yah Auwal ya san inda nike da ma shi d'ai na damuwa ta, na san shi d'ai na zai shiga matsanancin tashin hankali akan rashi na, a wajen iyaye na kamar dashen iccen juji ni ke, wanda ya fito ga jeji a kuskure, zai gama rayuwa tai ya mace ba tare da sanin kowa ba,"

Idanun ta abushe take wannan maganar babu digon hawaye cikin su, sai tsantsar quna da suya da zuciyar ta ke yi, gaskiya ta fad'i, ko ta na raye ko bata raye ta san iyayen ta ba damuwa za su yi ba, wataqiila qannen ta su Jameelu su damu da rashin ta, amma mahaifin ta da in ya fice ma ba ganin shi ake ba sai zai ci abinci, be bawa Kowa abinci ba, amma ya na tsammanin komawa shi a ciyar da shi,babban aikin shi bai wuce zaman majalisa, da bin bangon gidajen abokan da suka ci abinci qofar gidan shi, shi ma ya ci nasu ya kade riga y koma majalisa.

Lamishi kuwa jin gulmar ta da zuwa aikin ta, sun fi mata komai mahimmanci, ta na iya fita daga gidan da safe ta je aiki, ta dawo ta yi baccin awa daya ta fice gulma sai magariba ta dawo, duk abinda Mubaraka ta yi mai kyau ko mara kyau a matsayin fad'a ne, har nemo laifin ta take.

Mai Buruji kuwa sama sama ne, to iyayen da suka haife ka ma sun yar da kai balle wani? Sai wanda Allah ya taimaka ne yake samun masu yi masa kara su kula da shi .

Yah Auwal, Yah Auwal shi ne rayuwar Mubaraka, shi ne ruhi da numfashin ta, tun da aka sace ta ba ranar da za ta zo ta wuce bata wuni ta kwana kuka ba sai ranar da ta samu labarin zuwan shi, kullum a cikin damuwa da tashin hankali take, ta yi zazzabin ta yi ciwon, amma a banza, bata taɓa sanin ta na da jinnu ba sai a wannan wajen, ta tada su, har sun gaji sun lafa da kan su.

Murjanatu ce ta kalli Saliha ta ce,

"Yanzu daga tahiya ta yauce (toilet) har kin hwadi mata? Sai da an kace kar mu hwadi mata, yanzu ki na ganin rage damuwar da za ta yi ba zai sa su fahimci wani abu ba? Mun rusawa Yayan ta shirin da ya ke son yi kenan hwa, ke wai mis-sa ba ki iya riqe siri ne a ga rayuwar ki? Mtwss"

Murmushi mai ciwo mubaraka ta yi, sannan ta dauke idanun ta daga kallon waje dayan da ta yi ta zuba su akan Murjanatu ta ce,

"Kwantar da hankalin ki,ni a yanda nake dinnan ba zan taba komawa gida ba, ba zan bari Yah Auwal ya maida ni gida ba, abun kunya ne na koma gida a haka, amma ku? Ku za ku iya komawa gida, ina me baku hakuri, domin na san ni ta suka son dauka sun ka haɗa da ku,amma na sani, na san yayana ba zai taba hutawa ba sai ya his-she mu daga nan, inshaa Allahu ku na barin wajen ga"

Cikin kuka Suhaila ta ce,

"Mi ki ke nuhi? Ke dai san ba mu barin wajen ga in ba ke ko? Ko yayan ki ba na jin zai yarda ya his-she mu nan wajen ba bu ke a cikin mu,"

Shiru Mubaraka ta yi bata sake magana ba, amma ta san abu d'aya dole ya faru, za su tafi ba tare da ita ba, bata ga amfanin komawa gida ba, dama can ita GANTALALLIYA ce kamar yanda MAHAIFIYAR TA ke fadi kullum ba fashi .

************************

Da misalin takwas na safiyar litinin, Auwal ne ke tsaye a jikin motar Sultana, ya gama goge ta tass, sai sheqi take, gyara hannun rigar shi ya ke yi, ya na nannade shi sama, Sultana ce ta fito sanye da gilashi a idanun ta, fuskar nan kamar hadari, ta hade ta gam gam, ba alamar walwala, ko fara'ar nan ta ta, ba wani alamar nishadi, ko farin ciki, ga rama  ta yi ainun har ba ta boyuwa, hatta da doguwar rigar da ta saka sai da ta nuna alamar ta mata yawa.

Kanta a qasa ta fito, Sultan na biye da ita da mug din tea a hannu, roqon ta ya ke ta sha ko da tea din ne amma taqi, qarshe ma fad'a ta fara yi, kwata kwata hakan ba halin ta bane, Sultan bai ji zafin fad'an ta ba, sai ma tausayi, kama ta ya yi ya rungume, jin ta a jikin shi ne ya sanya ta jin wani abu a maqoshin ta mai ciwo, ya tokare ta, ta na son fidda abun, amma ta gaji da fitar da shi kullum, meye laifin ta? Meye laifi dan ka so driver din ka? Hajiya ta tsaya tsayin daka akan ba ita ba Auwal, kar ta sake ganin wani abu mai kama da soyayya a tsakanin su, daina zuwan shi ba qaramin dad'i ya wa Hajiya ba, Daddy ne kaɗai ya damu, saboda tsaron lafiyar ta, sai Sultan, jin ta take ita da watan da ke sama ba su da bam-bamci, domin kuwa shi ya na kewaye da taurari ko ta ina, amma still shi kadai ne, ita ma ta na tare da su Sultan da Daddyn ta, amma jin ta take kamar bata da kowa a duniya, mutum d'aya da ya mallaki zuciyar ta ya mata nisa.

Da sauri ta d'ago kan ta a lokacin da ta ji Dadyn ta da wanda ta ke tsananin kewa da son gani su na magana, kamar jiri ze debe ta, Sultan ya yi sauri ya tare ta.

Leqa bayan Sultan ta yi, dan tabbatar da abinda kunnen ta ya ke jiyo mata,

"....DPO ni ma ya kiren jiya, ya min bayanin da ya yi min dad'i, ya ce ana ta bincike, kuma su na ganin akwai alamun nasara, ana samun ta inshaa Allahu, shi na ma ya sa na ji hankali na ya ɗan kwanta"

"Da kyau, na yi ma alqawarin ana ganin ta, nan ba da jimawa ba, ka d'ai kwantar da hankalin ka"

Wani kallo ya wa Gwamna, wanda duk sa idon mutum ba zai iya fassara shi ba, murmushi ya saki mai sauti, irin wanda ya san ya na rikita sultana ,tabbas kuwa ya samu nasarar tarwatsa zuciyar ta in to thousad pieces, wasu hawayen farin cikin ganin shi ne ke gudu a kuncin ta, tabbas shi ne ba mafarki bane, ta na jingina jikin Sultan Daddyn su ya daga mata hannu, ya shige ciki, Lawwali kuwa cikin tafiyar shi mai dauke hankalin duk wani mai kallon shi,ya ke takawa zuwa inda suke,rigar Sultan sultana ta qanqame ta baya, hannun ta na rawa, wannan wanne irin so take wa Auwal?

Ko da ya isa gaban su, dan duqar da kai ya yi, ya sanya hannun shi daya a qirji, daya a bayan shi, ya ce,

"Barkan ku da swahiya ran ku shi dade"

A hankali ya d'aga idanun shi cikin salon sace zuciya ya kalli Sultana, kashe mata ido d'aya ya yi, kamar yanda ya saba, wani numfashi ta ja, sannan ta hau qiqqifta idanun ta, dariya ta sake mai sauti, tare da hawaye,hannayen ta duka biyun ta d'ora a saman bakin ta, a hankali ta zare gilashin ta ta na goge hawayen idon ta,cikin dakiya ta ce,

"Ka gama naka saura nawa, mu je ka kai ni office ina da abun yi"

Cikin murmushi mai sauti Lawwali ya ce,

"Dan Allah in za a hukunta ni a duba halin da nake ciki a min adalci, ina mai bada hakuri akan duk abinda na aikata, ni ma ba da so na bane, a duk inda na shiga ruhi na, hankali na, zuciya ta, su na tunanin ki, su na jin zogin rashin ki, amma qauna ta ban san halin da take ciki ba har yanzu, yanzu ma na kasa jure rashin ki na yas-sa na dawo gare ki Ran ki shi dade"

Gaba dayan su ya basu tausayi, Sultan ne ya taka ya isa gaban shi, cikin jimanta rashin mubaraka ya ce,

"Tabbas dole ka shiga tashin hankali da damuwa, mu kam mu hankalin mu ba a kwance yake ba da batan kamilar yarinya kamar Mubaraka, ballantana kai, Allah ya bayyana ta cikin aminci, kuma na san sultana ma ta yahe maka,"

Har zai tafi ya juya ya sanya fuskar Babban yaya, ya ce,

"Ga amanar qauna ta nan, kar na ji kar na gani, duk ta sake kuka akan ka, za ka gamu da ni"

Dan duqar da kai Lawwali ya yi cikin girmamawa ya na murmushi ya ce,

"Ran ka shi dade ba ko ka sake ganin hawaye a wannan kyakkyawan idanun mai haske kamar hasken rana idan ta hito"

Wata iriyar kunya ce ta kama sultana, ta yi matuqar kewar wadannan kyawawa kuma dad'ad'an kalaman daga wajen kyakkyawan masoyi Auwal.

A tare suke takawa wajen motar, banda murmushi ba abinda suke yi.

Bude mata motar ya yi ya ɗan duqar da kai, dan tura baki ta yi, sannan ta ce,

"Na kula da wani sabon salo ka dawo, na ce ka dai na ce min 'Ran ki shi dad'e' ka kira ni da Sultana, ka qi, yanzu kuma wani sabon salo ka zo da shi na duqawa ko?"

Cikin murmushin shi mai sauti ya ce,

"Duk inda mai girma da daraja shike dole na a bashi girma nai, duk inda kyakkyawa take dole ne a girmama kyaun ta"

'Wayyooo zuciya ta, Auwal na so ya hwashe ki da kalaman shi' abinda sultana ta fada kenan a ran ta.
Chapter 37 · 0% Book details