← Book details A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 93

Sashe 68

A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Isah dai ya qi shiru, sai zuba yake, qarshe da ta ga ba zai daina cika mata kunne ba, daki ta koma, ita da Ameenatu, suka bar shi da su Bilkisu a wajen.

Sai da ya ga Ahmad na qoqarin balle stone din wata riga, ya tattare duk haushin Hansatu da yake ji na qin kula shi da ta yi, ya gaurawa yaron mari, ai kuwa ya gigice, ya dinga zindima ihu, murmushin mugunta Isah ya yi, dan ya san zata je bada hakuri, ya qara bankawa yaro mari, Ameenatu na ta yi wa Hansatu magana akan ta je ta bawa Baban nasu hakuri, ta yi Murmushi ta ci gaba da gyara dakin ta abun ta.

Isan da yaga ba wanda ya kula shi sai ya hau masifa da zage zage, nan ma ba wanda ya ce masa ci kan ka.

Haka ya qaraci masifar shi ya bar gidan, tare da tabbatar mata da a sati na sama zai koma Makka,tunda abin nata iskanci ne.

Shirun da ta masa ne ya qara tunzura shi ya bar gidan gaba daya.

**************************

Ya kasa zaune ya kasa tsaye, saboda labarin da ya samu, Gwamna Halliru ya raba hotunan Mubaraka, ma jami'an tsaro dake tare motoci a hanya su bincika, ko da za a ga Mubaraka akai masa ita direct wajen shi, babban abun takaicin shi ne Dan Talo da kan shi ya bada hoton diyar tashi, ba tare da ya san me ke faruwa ba.

Sultana ce ta kwantar da kan ta a bayan shi, ta rasa da me zata kwantar masa da hankali, gaba daya naman jikin shi rawa yake, hankalin shi a tashe yake, damuwar shi what if aka kama su Mubarakan shi fa? Ina zai saka ran shi, ya zai ya cika mata alqawarin da ya daukar Mata na bata kariya? Daga shi har ita ba su da kowa mai qaunar su domin Allah sai junan su, in wani abu ya same ta ba zai taba yafewa kan shi ba.

Zama ya yi a qasa dabar, ya fashe da wani irin kuka mai ban tausayi, Sultana ma kukan take, duk ta bi ta rame, saboda rashin kwanciyar hankali.

Kallon ta ya yi, ya rungume ta sannan ya ce,

"Ki yahe min Sultana, ban zama miji nagari a gare ki ba, ban san ya zan da raina ba in wani abu ya same ta, kin dai san ta na shiga hannun mahaifin ki kashe ta zai ko? "

Ta na qoqarin kwatanta yanda yake ji a ran shi, amma bata san ya zata bayyana masa hakan ba, ba tare da ta yi tunanin komai ba, ta kai bakin ta nashi,wannan shi ne karo na farko da suka jima su na sumbatar junan su, kuma shi ne karo na farko da sumbatar ta zarce, har sultana ta cire duk wani tsoro, da tsaro, da kuma dokar da ta shimfida a tsakanin su, na sai ya fara sallah zata yarda ya Kusance ta, tunawa ta yi a ran ta cewar, ita addu'ar saduwa tsakanin ma'aurata, ba dole sai namiji ne kawai zai yi ta ba, mace da namiji duk ana so su yi, in daya be yi ba, saboda wani dalili, misali mantuwa, ko rashin iyawa, wanda ya iya zai iya yi shi.

A yammar Lawwali ya yi nasarar karbar haqqin auren shi a wajen matar shi ta sunnah kuma diyar fitaccen maqiyan shi,Lawwali bai taba hango cewar rayuwar aure dama haka take da wani sinadari, da dandano ba, sai a yau, wanda da ya san haka abun yake, da bai kai wannan tsahon lokacin ba, ba tare daya karbi haqqin shi a wajen Sulty Baby ba.

Lawwali ne ya taimaka mata ya maida ta saman gadon su, duk qasan carpet din ya ɓaci, cikin tausaya wa ya ce,

"Sannu Sultana, yanzu ya za mu yi? Na ga kin ji ciwo,ni ban san ya zan yi ba"

Duk da ciwon da take ji a jikin ta, bai hana ta, murmusa wa ba, tare da godewa Allah, da bai yi ta mazinaciya ba, hannun shi ta kama ta sumbata, shi kuma cikin damuwa ya kalle ta ya ce,

"Ki sanar da ni, mi zan yi yanzu? Ban san me zan ba, na ga har yanzu jini na zuba a jikin ki"

Cikin dasasshiyar murya ta ce,

"Ina so ka yarda da Allah,ka yarda Allah ne kawai zai iya bawa Mubaraka kariya ba kai ba, ka yarda cewar mubaraka ta na cikin kariyar ubangiji, ba wanda ya isa cuta mata sai idan Allah ya so,ina so daga yau ka min kyakkyawar kyautar da zata faranta raina,kyautar da har na koma ga mahalicci na ba zan daina jin dad'in ta ba"

Kafin ta sauke numfashi Lawwali ya ce,

"Na miki alqawarin baki duk abinda na mallaka, na kuma amince Allah shi ne kaɗai wanda zai kare min Barakana a duk inda take"

Murmushi ta yi, gefen idanun ta kuwa hawaye ne ke zuba da gudu,

"Ina so ka koma bautawa Allah, kamar kowanne musulmi cikakke, kuma nagartacce, wannan ita ce kyautar da nake so, a matsayi na na matar da ta kawo mutuncin ta gidan miji"

Lawwali bai san sanda ya rungume ta ba ya na kuka, tare da fadin

"Allah na tuba, Allah ka yahe min, ban san wanne aikin alkhairi na aikata ba ga rayuwa ta, da ka bani mace kamar wagga, Allah ka yahe min, Allah ka tausaya min ka yahe min ba dan hali na ba, Allah na san ka na so na da rahama ne ya sa ka azurta ni da mace kamar Sultana, Allah ka bani ikon sauya halaye na ka yi min afuwa"

Daga shi har ita kuka suke, da kyar suka lallashi kan su, suka yi shiru,

"Ka ce wa Barirah ta kawo ruwan zahi, kai kuma ka je ka yi wankan tsarki, ka shirya ka je gidan mu, ka taho da Sultan,ba tare da kowa ya sani ba, ka ce zaka kawo shi waje na mu gaisa, in ka yi haka, Daddy ya ji labari daga baya, ba zai sake ya cutawa Mubaraka ba har ta iso nan lahiya, ko ka na da wata shawara da ta hi wagga sauqi?"

Lawwali sake fashewa ya yi da kuka, ya rungume Sultana, yau zuciyar shi ta koma danya shataff a gaban matar tashi,su na haka, ta koya masa yanda ake wankan, ya tafi ya yi, ya kuma bada umarnin a kula da ita, ya bar dajin.

Kamar yanda suka tsara kuwa haka aka yi, tun Sultan na ganin nisan waje,har ya fara tambayar shin ina za su ne? Lawwali kuwa budar bakin shi sai cewa ya

"Za mu tai ne ka ga inda Daddyn ku ya bamu dan mu zauna ni da mata ta"

Mamaki ne fal ran Sultan,yanzu duk gidajen da suke da shi a cikin gari a rasa inda Sulty Baby na ta zauna sai kauye?????......

*Hummmm Sultan kenan, U never see anything*

💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻

BY HAERMEEBRAEH

PAGE 51:

Mutanen da ya gani sanye da qananan kaya da bindigogi, sun tsoratar da shi matuqa,nan take ya tuno da kalaman iyayen shi akan Lawwalin, amma ya rasa dalilin da ya sa ya kasa gasgata maganar su a qasan ran shi, har yanzu ya na ganin Lawwali a matsayin mutumin kirkin da ya ke gani a baya.

Su na isa sansanin Lawwali ya bude mota ya fita, ya na jiran Sultan, Sultan cikin daurewar kai ya fito,kwakwalwar shi da kowacce gab'a ta jikin shi na so a masa qarin bayanin abinda idanun shi ke gani.

"Kar ka samu damuwa ran ka shi dade Sultan, mu je za ka san duk wani abu da ka ka buqata, Sultana na ciki na jiran mu"

"Wai dan Allah da gaske anan Sultana ke rayuwa? Ko dai wasa ka ke min, me ya had'a ku da irin wadannan mutanen?"

Gaisuwar da Sultan ya ga ana miqawa Lawwali ne ya sake sanya shi cikin rudani, sun kusan isa dakin su sultana, sultanan ta fito cikin wata iriyar kwalliya, mai ban sha'awa, ta yafa mayafin ta kalar shaddar da ke jikin ta, ta saka flat shoe, sai qamshi take zubawa, Lawwali na dora ido akan ta, ya ji duk wata soyayyar ta da yake ta qoqarin dannewa, da wadda bai ma san ya fara yi mata ba, ta taso ta lullube shi, wani qayatacce, kuma sassanyan murmushi yake zuba mata, Itan ma haka, sai dai kunyar shi ta fi yawa a tattare da ita a yanzu, bata iya hada kwayar idon ta da na shi, Sultan tsaye yake ya na kallon ikon Allah, cikin gyaran murya, da gyara tsayuwar shi ya ce,

"Baby Sulty ta dena so na yanzu,"

Da sauri ta kauda kan ta daga kallon qasan ido da take wa Lawwali, ta fara takawa, cikin tsananin kulawa dan kar su gane sauyawar tafiyar ta, ta isa gare shi, rungume ta ya yi, ita ma ta sa hannayen ta biyu ta rungume shi, sai da suka gama farin cikin ganin junan su, sannan Lawwali ya saqale hannun shi daya a qugun ta,  sannan suka shiga ciki.

Lawwali ya yi mamakin yanda aka gyara wajen, sai kamshi ke tashi, ga abinci nan an kawo, da abun sha.

Aikin Barirah ne wannan.

Zama suka yi gaba dayan su, tare da yiwa Sultan Bismillah, kame hannayen shi ya yi, a qirjin shi, sannan ya ce,

"Ni fa ba zan iya sanya ko da ruwa ba ne a ciki na, ba tare da na san mi ya kawo ku dajin ga ba, shin sace ku an ka yi ko mi na na?"

"Mun yi maka kama da wanda anka sace?Kai dai aka sato, domin kuwa a yanzu haka in ba mun samu abinda muke so ba a wajen mahaifin ku, ba zaka koma cikin gari ba"

Wata dariyar rainin hankali Sultan ya yi, ya kalli Lawwali ya ce,

"Habaa habaa suruki na, ai ni nafi qarfin a sace ni, in ka ga an sace ni to qaddara ta ce ta zo da haka, ni da ka gane ni ban wasa da azkar, ban wasa da addu'ar hita da shiga gida, ka ko ga me sace ni sai ya shirya"

Sultana ce ta yi dariya ta ce wa Lawwali,

"Kira Daddy"
Chapter 68 · 0% Book details