Sashe 66
A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zai hukunta duk wanda ya yi sanadin lalacewar shi, har iyayen nashi, ba zai barsu ba, ya san maganin su, ba dai kudin shi suke so ba? Kuma da shi suke taqama da fadi a gari ba? Zai ga wanda zai dinga basu kudin.
Ya na nan ya na ta tunani, har bacci ya fara kama shi,sannu a hankali ya miqe, tare da Sultana a hannun shi mai lafiya.
Dora ta ya yi saman gado, sannan ya hau, ya rufe su, suka yi baccin su.
Da safe kuwa ya dauki wayar No 5 ya kira gwamna, ta na shiga gwamna ya kece da wata mahaukaciyar dariya, tare da fadin.
"Yaro bai san wuta ba sai ya taka, aza shikai yadda muka sa shi ya zama wani a fagen ta'addanci, ba zamu iya creating wani ba, to gashi yanzu ka ga bayan shi, alqawari na ya...."
"Dad'i na da kai qaramar kwalwa wallah(qaramar kwakwalwa), shin mi yasa ka ke abu kamar wanda be je makaranta ba! Baka tunanin ko na kashe shi wayar shi na hannu na? Tunani ka ke ya kashe ni ya kira ya fadi maka ko? To ka tafka babban kuskure"
Lawwali na fadin haka ya kashe waya, bangaren gwamna Halliru kuwa hankalin shi in ya yi million ya tashi, wani irin tsoro da tashin hankali da damuwar makomar shi ne suka bi suka dabaibaye shi.
Ba shiri ya fara kiraye kirayen waya, akan ya na neman qarin masu tsaron lafiyar shi, da ta iyalin shi.
Hajiya Ikee da ke tsaye ta na so ta ji qarshen Lawwali kuka ta sanya,
"Se na dana fada maka kar a yi haka, yaron nan ba mutunci ne da shi ba, ni kad'ai na san yanda na ji sanda ya shaqe ni, baka taba shiga hannun sa bane, shi ya sa, yanzu Allah kad'ai ya san mi ze wa Sultana da ke hannun shi, Innalillahi wa inna ilaihirraji'un, mun shiga uku mun lalace"
Kukan ta ne ya jawo hankalin Sultan da ke karyawa ya shiga parlourn, kalaman da ya ji na Hajiya sun juyar masa da kai, waye zai cutar da Sultana?
"Waye zai cutar da sultana? Ku fada min me ke faruwa ne, kwana biyu babu natsuwa a tattare da ku, kun damu da rashin su Sultana, mata da mijin ta a dinga bin diddigin su bai dace ba"
"Dan uban ka Lawwali tsohon dan ta'adda ne ba mutunin kirki ba ne, ya dauke ta ta na can inda ya ke ya na gana mata azaba"
"Ban gane ba? Kun sake sanya ni duhu"
"Kai ba kalar daqiqai ba balle na ce ko takkwalanci(daqiqanci) ke damun ka, shin wane yare ne baka fahimta ba? Lawwali dai dan ta'adda na, ya ha'ince mu, ya auri qaunar ka, ya gudu da ita"
Qaryar da ta yi ta sa gwamna Halliru yin ajiyar zuciya mai qarfi, dan kuwa ta ce ce shi, a yanda ran shi ke tafasa dinnan, abu biyu za ai, ko ya bada amsa daidai, ko ya hasala ya wa Sultan abinda zai zo ya na dana sani da kan shi.
Sultan ne ya kalli Daddyn su cikin damuwa ya ce,
"Daddy u have to call the police and let them know about this, a gaggauta daukan mataki"
Cikin wata kakkausar murya gwamna ya ce,
"Kar wanda ya kuskura ya yi involving hukuma a maganar ga har sai na bada izini"
"But daddy what if suka cutar da Sultana? I can't let anything happen to her,ba zan yahe wa kai na ba in wani abu mummuna ya same ta"
Yanda Sultan yake ji a zuciyar shi, da zai samu ko kukan ne ya yi, kamar yanda Hajiyan su ke yi, da ya ji dadi.
Duk yanda yake tunanin shawo kan Gwamna a hada abun da hukuma ya gagara,qarya kan qarya suka dinga shimfida wa Sultan, daga qarshe suka bashi shawara ya je ya yi ta addu'a har Allah ya dawo da qanwar shi gida lafiya.
Sultan na fita Gwamna ya yi waya, Hajiya Ikee na jin me yake fad'a a wayar ta rikice, ta rude da kuka.
"Me ya kai ka nemo Mubaraka? Ga iyayen shi a gari? Ka rufa muna asiri akan wanda Allah ya lulluba muna, kar ka tone shi,ka sa a kama iyayen shi, ka bar batun yarinyar nan yar ido, yanda yaka son yarinyar nan, ko kan shi ba ya so haka"
"Wanne iyayen nashi za a kama? Yo Allah na tuba ko halbe su zan yi zai damu ne a ka fada Maki? Ke bari ki ji, ba na duba, kuma ba na ganin zuciyar kowa, amma wallah ba wanda yaron nan ya tsana a yanzu duk duniyar ga wanda ya wuce iyaye shi da ni, dan haka bar batun su ma, in na gano qaunar shi na kame ta, zai sako Sultana lahiya"..........
*Hummmm wai haka???*
💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻
BY HAERMEEBRAERH
PAGE 49:
Gidan talabijin na NTA da ke garin Zamfara ke haska wata gagarumar gobara da wasu ke zargin Bomb aka sanya a wani babban wajen ajiya na kayyaki kala kala,mallakin gwamnati,kayan sun had'a da, kekunan d'inki, kekunan guragu, shinkafa, man gyada, wake, katifu, da dai abubuwa masu tarin yawa, gwamnati ta danqare su ta ajiye su, saboda zagayowar zabe, sai a yi ta raba wa mabuqata ana neman quri'un su, mutane kuma da yake a matse suke da lalure laluren duniya, in aka basu sai su karba su na murna, su na ganin an musu wani babban alkhairi ne, ba tare da sun yi tunanin cutar da su ake yi ba a hakan.
Wuta sai ci take an kasa kashe ta, mutane kuwa a hakan suka dinga qoqarin diban kayayyakin abinci, su na guduwa, labari ya kai har gidan Gwamnati, Gwamna Halliru kuwa ba qaramin tashin hankali ya shiga ba, domin wannan ce babbar ma'ajiyar shi,gashi an qona ta, kuma mutane sun samu damar kwasar abinci, da duk wani abu da ya adana domin zabe mai zuwa, gashi mutane sun gano manufar shi ta qanqame kayan more rayuwa a lokacin da ya dace a ce gwamnati na taimakon su, ta saka musu da wahalar da suka sha na zaben ta, ana jiran sai sanda suka matsu da neman abinci a basu.
Har haushin yanda ake ta masa waya ana sanar da shi abun jimamin yake, a fusace ya fita daga office din nashi ya na kiran wayar wanda ya bawa aikin bincika masa inda su Mubaraka suke.
An sanar da gwamna Halliru Murtala Gusau, garin da Mubaraka take,amma me ya sa har yanzu ba a gano inda take ba? Duk da cewar Ya sani Kano tinjimin bajimin gari ne, nemo Mubaraka zai wahala, amma ba zai gaji ba, ba zai huta ba, har sai an same ta.
Bai samu layin wanda yake nema ba, dan haka cikin fushi ya bar gidan gwamnatin gaba daya,ya fada motar shi, ya na ta waya tare da bada umarnin kula da ma'aikatu da duk inda ya kamata a bawa tsaro,masu tsaron lafiyar shi, tuni suka tada motoci, sai gida.
Lawwali bai fito ba sai da ya shirya, kafin sati ya sake zagayowa ya yi wa manyan ma'aikatun gwamnati, da ma'ajiya kala kala,da kadarorin gwamna Halliru barna, kusan wasu abubuwan da gwamnan ya mallaka,ba wanda ya san da su, Lawwali ne kawai ya san ya mallaki wasu kadarorin, tunda shi yake aika,ya sama masa su, ta qarfi da yaji,Lawwali ba qaramin birkitawa gwamnati da hukumar tsaro ta jiha da ta Nigeria gaba daya lissafi ya yi ba, gwamna Halliru ya koma kamar mahaukaci, a yanzu yanda yake ji, bai qi ba kowa ya san me ke faruwa a tsakanin shi da Lawwali da yaran shi ba, amma tsoron shi daya, kar ya aika da jami'an tsaro a buɗe musu wuta kuma Sultana na cikin su, ya zai yi ne.
Sati Uku currr ana abu daya ba d'aga qafa, Sultana ta yi iya bakin kokarin ta dan ganin ta taushi zuciyar Lawwali amma abun ya faskara, daga shi har yaran shi a tunzire suke, ta barauniyar hanya ake shigo musu da makamai daga wasu qasashen,gwamna Halliru ya yi danasanin damqa masu manyan makamai, domin kuwa ya tabbatar da su ake tarwatsa masu gari, sun bata masa suna a duniyar siyasa, dan ya tabbatar da cewa yanzu mutane na ganin baqin mulkin shi,da su na da yanda za su yi da sun tsige shi.
Ba gwamna Halliru Murtala kadai ba, hatta da Hajiya Ikeeleema bata da ikon shiga manyan taron matan gwamnoni lafiya, ba tare da an yi maganar tabarbarewar mulkin garin nasu na Zamfara ba.
Mummunan labarin neman da gwamna Halliru ke yi wa Mubaraka ya iske kunnen Oga Lawwali, cikin tsananin damuwa da tashin hankali Lawwali ya kira No 4, tare da bashi umarni, duk yanda zai yi, ya yi, ya kawo masa qanwar shi wajen shi cikin qoshin lafiya.
No 4 ya shiga damuwa matuqa, dan kuwa labarin tashin hankali da rashin zaman lafiya da ake ta samu a yankin Zamfara ba boyayye bane, ga shi ba ya so ko da kwarzane ne ya samu Mubraka, dan kuwa a yanzu ya gama tabbatar wa da zuciyar shi ya na tsananin qaunar Mubarakan, tsoron cin amanar Oga ne ya hana shi bayyana mata, da tinanin halin da Fateema za ta shiga in ta ji ya na so ya auri Mubaraka, Taheer No 4 na cikin matsala, ya rasa yanda zai ya cika umarnin oga ba tare da Mubaraka ta samu matsala ba, dan kuwa ya san duk wata hanya da gwamna zai bi dan ganin ya gano su zai bi ta.
*************************
Zaune ya ke ya na jefa soyayyan naman rago a bakin shi, ya na korawa da lemo kwali, in ya cinye ya gutsiri meat pie, Hajiyan Hansatu kuwa na ta zuba godiya da yaba wa surukin nata.
"Dan Allah Hajiya ki dena min godiya haka, ai ke uwa ta ce, musamman ma da ban da kowa ke nake gani na ji dad'i a raina"
"Ai dole na maka godiya Isah, irin wanga kayayyaki kamar dan ni ka tahi Makka, lallai na tafka babban kuskure a baya, da na qi ka, Allah ya bawa d'iya ta mijin maraniya, Allah ya jiqan Alhaji, da ya ga zab'i nai yau,"