← Book details A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 93

Sashe 70

A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hankulan su ya tashi, da jin mahaifin su ba lafiya, shi kuwa ya na sanar da su, ya tafi ya na neman layin No 4, yanayin network din wajen akwai matsala, dan haka da kyar ya same shi, ya na dauka ya ce,

"Gobe da subahi ku taho, hanya lahiya lau ne yanzu"

"To Oga Allah shi kai mu"

"Ameen, lahiya kuwa Taheer? Akwai damuwa ne?"

Da sauri No 4 ya daidaita Muryar shi ya ce,

"Lahiya qalou Oga, kwana na hwara shi ya sa ka ji murya ta haka nan"

"Tau yayi, ka sanar da Barakana gobe mu na tare, ba na so na kira ta yanzu na san ta yi kwana"

"To Oga zan isar da saqon ka, kahin mu taso ma ai na san za ka kire ta ko?"

"Kwarrai da gaske, sai goben"

"Tauu Allah shi kai mu"

"Ameen"

Cikin murna ya fada dakin nasu,  Sultana da Sultan ya gani har sun riga shi isa dakin, su na jayayya akan zuwa ganin mahaifin su, Sultana na bawa Sultan hakuri, akan ya bari ba yanzu ba, shi kuwa ya dage sai ya tafi.

Lawwali ne cikin nuna halin ko in kula, dan ba wai ya ji wani abu bane dan gwamnan na asibiti, budar bakin shi ya ce da Sultan

"Ka ga Suruki na Sultan, na san kai mai addu'a ne da ibada, amma wagga qaddara kai ma ta kamma, ba ka tahiya ko ina, har sai mahaifin ka ya warke ya biya mana bukatun mu, domin ba rayuwar shi ce kad'ai adda mahimmanci ba, mu ma mutane ne"

Lawwali na gama fadin haka ya fita,Sallah ce a zuciyar shi, amma bai san ta yanda zai fara zuwa ya yi alwala ya gabatar da Sallah ba, gani yake kamar in ya yi ba zata karbu ba, kuma ma dai maganar gaskiya, ya na ganin kamar ya manta wasu abubuwan, shekarun da ya dena sallah da yawa, Gashi yanzu Sultan ya zo, ya na neman kawo masa wata maganar komawa gida, ba zai taba barin shi komawa ba, sai ya cika alqawarin dawo da mubaraka wajen shi lafiya.

Dakin marigayi No 5 ya sa aka gyarawa Sultan, ya je ya lallaba shi, akan lallabawar da ya tarar Sultana na masa, ya raka shi har dakin, suka yi sai da safe ya koma nasu dakin.

Alwala ya je ya yi, ya zauna, ya kasa tashi ya tada sallar,Sultana kuwa ta fada duniyar tunanin halin da mahaifin su ke ciki, dan haka bata kula da halin da mijin ta ke ciki ba.

"Uhummm na ce, kin yi sallah ne?"

Da sauri ta zare hannun ta daga tagumin da ta yi,ta kalle shi, dan ta na so ta tabbatar da shin Lawwali ne ya ke tambayar ta tayi sallah ko ah ah, ganin ya kafe ta da ido ya na neman qarin bayani ne ya sa  ta ce,

"Eh na yi magariba kahin Ku zo, amma ban yi Isha'i ba"

"Ok to ki tai ki yi mana, mu kwanta, kwana nika ji"

Tashi ta yi, ta tafi ta yi alwala, duk tunani da damuwa sun addabe ta.

Tada sallah tayi, Lawwali kuwa ya maida hankali ya na kallon me take, da yanda take bin qa'idojin yin Sallah, duk ya na haddace wa a kan shi.

Sai da ta idar ta yi sallama sannan ta kula da kallon da yake mata.

Murmushi ta yi, dan kuwa an ci gaba, in zata shekara Sallah dan ya kalla ma abun ya bashi sha'awa ya yi, ba zai kalla ba, qarshe ma bar mata dakin yake, yau kuwa Gashi sai binta yake da kallo.

"Ka na buqatar wani abu daga waje na ne"

Sunkuyar da kan shi ya yi, cikin jin nauyin ta, ya ce,

"Ki koyar da ni yanda  aka yin sallah"

Gyara zaman ta tayi sannan ta ce,

"Ba a jin kunyar tambaya a addini, duk girman mutum duk qanqantar shi, duk sanin shi duk rashin sanin shi, a kullum shi mai neman sani ne, dan haka kar ka ji kunya, ni ma har yanzu akwai abubuwan da ban iya ba, ina neman sani akan su"

Nan dai Sultana ta koya masa abubuwan da ya mance.

Ya kuwa yi sallah,ranar Sultana sai da ta yi kukan farin ciki, saboda yanda Lawwali ya jima a sujjada ya na kuka ya na qasqantar da kan shi gaban ubangiji, sai neman gafarar Allah yake ya na kumawa.

Tausayin shi ya gama ratsa duk wata kafa ta jikin ta, ya jima ya na sallar da bai san adadin ta ba, sai da ya ji qafafun shi sun kasa tsayuwa sannan ya sallame, da gudu Sultana ta fada jikin shi, suka rungume juna su na kuka.

Cikin kukan ya ce,

"Ki na ganin Allah zai gafarta min kuwa? Abubuwan da na yi a rayuwa su na da yawa Sultana, rayukan mutane da na dauka da hannun ga nawa su na da yawa, ba zan iya qayyade miki su ba, Sultana wasu lokuta in mun ka kashe gari guda hukuma na qiyasta mutane ne fa kawai su ce an kashe mutum kaza, amma adadin ya hi haka nan, ki na ganin Allah zai yafe wa mai laifi da yawa, kuma manya kama ta?"

Shafa fuskar shi ta yi, ta na share masa hawayen shi, ta kai labban ta da suka bushe saboda kuka, ta manna a nashi, ba tare da ya mayar mata da martani ba, ba tare da Itan ma ta na jiran martanin shi ba, ta daga ta kalle shi tace,

"Allah subhanahu wata'ala ya ce, kar mu yanke tsammani  daga rahamar shi, shi mai rahama ne, Allah subhanahu Wata'ala ya ce, da bawa zai je masa da zunubin da ya kai kumfar teku, ya tuba, tuba mai kyau, to zai gafarta masa dukkan zunubin shi, bawan da Allah baya gafarta wa yake sawa a wuta shi ne, bawa mai shirka, har ya mutu ya na shirka, kuma bai dena ba, to wannan bawan zai dawwama a wutar Allah ne, ba ranar fita, dan haka ina kyautata wa Allah zato, zai karbi tuban ka, da izinin Allah"

Tunda suka zo Hajiya Ikee bata taɓa kiran Lawwali ba sai yau, ringing din wayar ne ya cika dakin, Lawwali ya kalli Sultana, Sultana ta kalle shi.......

*A daga ko kar a dagaaaa????😂*

💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻

BY HAERMEEBRAERH

PAGE 52:

Sultana ce ta miqa hannu za ta dauka, Lawwali ya yi saurin janye wa,ya kafe ta da wani mugun kallo, idanun ta ne suka ciko da kwalla, saboda ta na so ta ji a wanne hali mahaifin su yake,ganin idanun ta na qoqarin zubar da ruwa ne ya sanya Lawwali sassauta kallon da yake mata, bin kiran ya yi ba dan ya so ba, sai dan ba ya son duk abinda zai sanya ta zubar hawaye, a handsfree ya sanya wayar, kamar jira Hajiya Ikee take a kira, ta yi sauri ta dauka.

"Hello,...Hello,...Lawwali ka na ji na kuwa? Ka wa Allah, ka wa iyayen ka ka maido min da yaran mu,"

Fashewa ta yi da wani irin kuka, mai ban tausayi,sultana ma kukan take, ba abinda ke tsakanin su da iyayen su illa matsananciyar soyayya da kulawa, duk wani abu da zai sanya su farin ciki su na musu shi, duk wannan halin da suke ciki, dan ganin sun faranta musu ne,sai dai kashhh ba su bi hanya madaidaiciya ba, wannan shi ne babban kuskuren su a rayuwa.

"Ka na ji na kuwa? Don Allah ba dan halin mu ba ka sake mana yaran mu,His Excellency na cikin mawuyacin hali, tunda an ka kawo shi bai san wanda ke kan shi ba, bai san wanda ke gehen shi ba, ko motsi ba shi yi, ka taimaka ka maiso mana da su, ko Allah zai sa shi bude ido"

"Hajiya ki na bata bakin ki,domin ke baki san kala da kalan dokoki da yasa ba,kuma ni ban tab'a tsallake umarnin shi ba, shin su iyayen da munka d'auke Wa yara mun san halin da suke a yanzu? Ko kin san cewa akwai wad'anda sun shekara uku zuwa hudu nan wajen? Akwai wad'anda suke anan wajen tun farkon fara aikin da shi mijin ki yasa mu yi, su to ya iyayen su suke ji? Ke San ciwon ka nemi naka ka rasa? Baka san inda shike ba? Ba za ki sani ba, ni zan baki labari, lokacin da mijin ki yaci amana ta, ya dauken qauna ta, lokacin nan ba irin tashin hankali da u'qubar da ban shiga ba, ashe ta na nan kusa da ni, ban sani ba, ku gode Allah kun san inda suke, kar ki qara kira na,"

Sultana ce ta matsa jikin shi za ta amshi wayar, ya wurga mata wani kallo mai dauke da warning, sannan ya wurga wayar saman gado ita kuma ya dauke ta cak ya dora a saman cinyoyin shi, ya manna bakin shi a nata, ranar Lawwali ya bawa kan shi mamaki, ashe ya iya irin wannan soyayyar bai sani ba.

Sultana kuwa tun ta na kukan hana ta magana da mahaifiyar ta da ya yi, har sai da ta manta kowa da komai, jin ta kawai take a duniyar da Lawwali ya kai ta, mai cike da ni'ima da nishad'i, mai cike da gamsar wa, duk wata nutsuwar da ke tattare da ita ta kwace, ba abinda take gani a idanun ta, sai Auwal din ta, ta na tsaka da amsar saqon salon soyayyar shi mai wuyar fassara ta ji ya na qoqarin cimma burin shi, da sauri ta bude ido, dan kuwa bata gama warkewa ba, kyabe baki ta yi, irin na shagwabar nan, Lawwali ya kalle ta da rinannun idanun shi, da alamar tambaya, sauke idanun ta tayi, ta kalli qasa, ta na wasa da qirjin shi ta ce,

"Da zafi fa, ban warke ba"

Da sauri ya d'aga ta, ya na nuna nadamar abinda yake son aikatawa, ganin hakan da ya yi, sai ya bawa Sultana dariya, hancin shi ta ɗan ja kad'an tare da kai wa lips din shi kiss sau daya ta ce,

"You are so cute,"

Murmushi ya yi sannan ya ce,

"Sannu Sultana, ki yafe min, ban San zaki ji ciwo ba, ko za mu tai gari ki ga likita?"
Chapter 70 · 0% Book details