Sashe 50
A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hajiya Ikee fa ta kasa jure wannan iskancin, qoqarin barin wajen take dan ta isa ta ci wa Lawwali mutunci ta ga abinda bata taɓa tsammani ba, Lawwali ne ya duqa ya sumbaci kuncin Sultana, ita kan ta sai da ta saki ledojin hannun ta suka zube qasa, shi kuwa ko a jikin shi,ido ya kalli sama ya kashewa Hajiya Ikee dake tsaye a jikin window ya ajewa Sultana jakar ta ya tafi.
Sai da ya bar gidan gaba daya, ta dawo hayyacin ta, wajen da ya sumbata ta shafa, ta saki murmushi, can kuma ta ɗan bata rai ta ce,
"Auwal ba kyau fa,"
Kamar ya na ganin ta, wani sassanyar murmushi ne ya kubuce mata a karo na ba adadi, ita ta na taba shi, shi ya na guduwa, shi ne yanzu zai nuna mata ya iya taba jikin mutum yi ne kawai ba ya yi,daukan tarkacen ta tayi, ta shige gida cike da nishadi, Allah Allah take su hadu da Sultan ta bashi labari, ta na sanya qafar ta, a cikin gidan, ta ji an ce,
"Kee Sulatana, zo nan!"
Cikin tsananin firgita da tsoro ta taka zuwa babban parlour'n na su...........
*A yi hakuri da wanga sai zuwa anjima ko gobe inshaa Allahu zan ci gaba, thank u mutanen Ogaaa😂*
💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻
BY HAERMEEBRAERH
PAGE 38:
Mubaraka na matuqar jin dadin zama da su Taheer da iyalan shi,domin duk wani abu da take so, ko suka kula ta na da buqata da wuri za su yi mata shi.
Da kyar Fateema ta yarda ta ke taya ta girki,shi ma dan Mubaraka ta dage ne, kuma cikin ikon Allah, sai ya zamana su na samun qaruwa da juna, abinda dayan su bai iya ba, sai daya ya koya ma daya.
Yaran su kuwa kamar qannen ta haka ta dauke su, ita ke musu wanka, ta shirya su, su je islamiyya su dawo tare.
Ranar Monday mai zuwa za ta fara zuwa Makarantar boko, a tunanin Lawwali makarantar Army Day ne kawai za ta samar wa Mubaraka tsaro, dan haka can ya saka ta, ya sa Taheer ya nemar mata driver da zai dinga kai ta, saboda shi bashi da lokacin kai ta, ya fara zuwa kasuwa, ya na saida shaddodi.
Ranar farko da Mubaraka ta fara zuwa, ta samu masu son qawance da ita kala kala, musamman dan ganin a irin motar da aka kawo ta, amma dake tin kafin Lawwali ya bata gargadin yin qawaye barkatai, ita ba me son tarkacen qawaye bace.
Dan haka gaisuwa ke hada ta da kowa, ta raba ta da kowa lafiya.
Tun ranar da aka kai ta makaranta wasu sojoji wanda suka addabi d'alibai mata, suke kula da zuwan ta, da tafiyar ta.
Yanayin kamun kan ta, ya ja ra'ayin su, su na son sai sun lalata mata rayuwa, (wannan duniya yanda ta lalace Allah ne kawai zai gyara mana ita, in ka yi shigar banza, maza na kallon ka, su na dakon ka, in ka yi ta kirkin ma, wasu so suke su yaga maka rigar mutunci)
Lokuta da dama ta kan gan su, in ta je shago siyan wani abun, shagon na dan nesa da asalin cikin makaranta.
Watarana ta zo makaranta sai ta kula an sace pen din ta, gashi an basu assignment ta na son ta yi, in ta isa gida, dan haka tsayawa ta yi a shagon dan siyan pen.
Ta na tsaye ta na jiran a sallami wasu,sannan a bata abinda take buqata, kurtun sojan nan ne dai da ya sa mata ido shi da abokan shi ya zo shiga wajen, duk warin hayaqin sigari da wiwi ke tashi a jikin shi, ga hanya can da za ta ishe shi ya shiga shagon amma sai da ya rabi jikin Mubaraka har ya na gogar qirjin ta.
Tura shi baya tayi ta ce,
" Allah ya saka min azzalumi "
Kurawa sunan dake jikin rigar shi ido ta yi, ta kasa gane sunan nashi Saboda sunan arna ne da shi, kuma da yare aka rubuta,duk qoqarin ta na ta karanta sunan ta kasa.
Zuwa ya yi ya daddafe ko ina na jikin qofar, ya sanya ta a tsakiya kenan, da kyar take shaqar numfashi, hannun shi ya sa ya shaqe mata wuya, duk wajen ana tsoron shi, dan ya saba zuwa, in ya ga mata masu kyau, ya yi ta bibiyar su.
"Hey, what are you doing, pls let me go, stop touching me, I will tell my brother if I go home"
(Kai me ka ke yi ? Dan Allah barni na tafi, bari tab'a ni,se na fad'a wa yayana idan na ne gida )
Kuka ta fashe da shi, duk jikin ta na rawa ko ta ina, da kyar mutanen wajen suka bashi hakuri ya rabu da ita ta fita daga wajan a guje, motar ta ta nufa ta ga drivern da Taheer ya daukar mata baya ciki, ashe abokan sojan nan ne suka kira shi, suka tsare shi, sun tabbatar dole zata je inda motar take, daga nan za su kamata su tafi da ita, sai sun gama abinda suka so da ita su dawo da ita.
Haka kawai jikin ta ya bata ta gudu, tunda bata hango driver a motar ba, dan acaba ta gani, irin masu fitar da mutum wajen gate dinnan, ta haye, ta ce ya Kaita gida ko nawa ne zata bashi.
Ai kuwa ya na jin haka ya ce ta hau, ta haye ta rufe fuskar ta dan kar a gane ta, gudu suke zubawa, har suka kai gate, sun fita kenan, ta hango qaramar motar da sojojin uku suke ciki, dira qasa tayi daga machine din, ta buya a gefen wasu ciyayi da ke bakin kwata, duk abinda ta ke su na ganin ta, gani ta yi sun tunkaro ta, bayan sun rufe motar su, cikin Barack ta shiga da mugun gudu, duk ta daddauje jikin ta, ya na mata zafi,sojojin da ke bakin gate ta dinga roqa kar su bari su tafi da ita, ta na ta rusar kuka, bata fatan sake riskar abinda ya faru da ita a baya.
Su na ganin haka suka koma, domin ana ta complain akan su, kar akai rahoton su.
Cikin sa'a kuwa ta tarar da wani babban soja na qoqarin shiga motar shi, gefen shi wani karamin soja ke bude masa mota, wajen shi Mubaraka ta kwasa a guje, ta masa bayanin komai, akai akai ta fadi sunan shi ta kasa, sai ta rubuta a qasa, Sojan na gani, ya gane wa take nufi, duk da bata rubuta daidai ba.
A nan take ya bada umarni a je a nemo driver din ta, a cikin daji aka same shi an daure shi, ya sha duka ,har gida sojan ya raka ta shima a tashi motar.
Godiya ta dinga mishi, ya ce aikin shi ne, ba sai ta yi godiya ba, bayan ya koma Barack ya sa aka nemo wadannan sojojin, aka musu hukunci daidai da abinda suka aikata, su kuwa cikin zuciyar su sun qudirta duk inda suka hadu da Mubaraka sai sun dau fansar abinda aka musu.
Mubaraka kuwa Taheer na dawowa daga sabon wajen sana'ar da Oga Lawwali ya bude masa a kasuwa, wato shagon saida shaddodi na mata da maza, ta sanar da shi komai, ya kuma yi mata alqawarin daga ranar ta bar zuwa makarantar barikin sojoji, tunda ba diyar soja take ba.
Da kan shi ya sauya mata makarantar private da ba ta da nisa da su, a kai ta a maida ta hankali kwance.
Ya gargade ta da kar ta sake Lawwali ya ji wannan maganar, in ya ce me ya sa aka sauya mata makaranta su ce ba a karatu a can shi ya sa.
Dariya ta yi, ta daga kai, ko dama da ta ce za ta gayawa yayan ta shi take nufi ba Lawwali ba.
************************
Tun saukar shi a jirgi ya ke gwada layin No 1 bai dauka ba, Gashi dai ta na ta ringing amma ba a daga ba, lambar No 4 kuwa ma sam ba ta tafiya, damuwa ce qarara a fuskar shi, tsoron shi kar dai yaran sun hade masa kai da Ogan su?
Da sanyin safiyar masu tsaron lafiyar shi ne tsaye a bakin motocin da suka zo da su dan daukan shi, bude masa motar da zai shiga aka yi ya shige ya zauna, sake gwada No yake amma gashi ta na ringing ba a dauka.
Cikin zuciyar shi ya ke tunani,
'Na manta yanzu safiya ne, wataqila ko tashi ba su yi ba'
Maida wayar shi ya yi, ya ajiye, har suka isa gida bai dena jin yanayin da yake ji ba, na rashin dadi a zuciyar shi.
Hajiya Ikee da ta san da dawowar mijin ta, ta sha gayu, har ta gaji, ta bawa masu aiki umarnin hada abin karin kumallo masu rai da motsi, na musamman.
Kwararru kuma hadaddun masu girkin tuni suka fara bade gidan da qamshi, Sultana na zaune a saman sallaya, bayan idar da Sallah da azkar, ta fara karan ta qur'ani, ta na jin qamshi na tashi kala kala, ta tabbatar Daddyn su na tafe, murmushi ta yi, tare da qara qaimi wajen karatun ta, dan ta na so ta haɗa da addu'ar samun nasara daga wajen Allah.
Da misalin shida da hamsin da bakwai 6:57am Gwamna Halliru ne a zaune bakin katafaren gadon su, ya zubawa Hajiya Ikee ido, ta na ta rattaba masa bayanai, akan abubuwan da ke ta faruwa a bayan shi,(rashin iya tarbar miji, daga dawowar shi, ba a bashi ko da abin da zai sha ba, balle a bari ya huce gajiya an fara bashi munanan labarai)
Gwamna Halliru shiru ya yi ya na sauraron ta,
".....shi ya sa na fada maka, ka kori Yaron nan, ka qi, gani ka ke in ba shi Sultana ba zata iya takawa ko da gate bane ba tare da an halaka ta ba"
"Kwarai da gaske, baki da masaniyar waye shi, har yanzu cikin jahilcin sanin waye shi kk, shi ya sa ki ke wannan surutan,"