← Book details A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 93

Sashe 80

A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lawwali ana gama daura auren ya bar wajen, wani waje ya nufa da ba mutane ya zauna shi kadai, ya na hawaye, tunanin rayuwar shi tun daga farkon ta zuwa yanzu yake yi,daga gobe zai bar wannan dajin ya koma zama a cikin gari kamar kowanne mutum mai 'yan ci, sai yanzu ya gane su aka sa a kurkuku, ba su suka sa a kurkuku ba, tunani ya ke, shin tuban da ya yi ya karbu kuwa? Ko dai har yanzu Allah na hushi da shi? Abubuwan da ya aikata manya ne, masu girma ne,tunanin kalaman Mubarakan shi ya yi, a duk sanda take masa nasiha, ta na sanar da shi cewar,

'Yah Auwal ka tuba ka dena wanga harkar, ka samu aiki na halal ka yi, in ka tuba Allah mai yawan gafara ne, mai son bayin shi masu yawan tuba ne, kar ka yanke tsammani daga rahamar Allah'

Nan da nan ya ji wani qarfin imani da Allah na ratsa shi, ya na jin tabbas Indai tuba da yarda da Allah na sa Allah Ya yafewa bawan shi, to tabbas ya na saka rai Allah ya yafe masa.

Ya na nan zaune ya ji kan reshen da yake kai ya yi qasa,alamar an zauna, kafin ya duba gefen shi qamshin ta ya sanar da shi wace ce, kwantar da kan ta tayi a kafadar shi tare da zira hannun ta a nashi.

Za ta yi magana ya ce,

"Shiiii, kawai mu yi shiru,mu saurari iska, da karar busassun ganyayyaki, mu saurari kukan tsuntsaye da bugun zuciyar mu, ina so na zauna da ke a haka na wasu mintuna kahin ku tahi"

Kissing din hannun shi ta yi, ta sake qanqame hannun, ta kwanta a jikin shi sukai shiru.

Suna nan zaune Mubaraka ta same su, murmushi ta yi, da ta ji sun yi shiru, ba abinda suke fadi, manne da junan su, a hankali ta taka, duk da qarar ganye da ke qoqarin tona asirin zuwan ta, ta na isa daf da su ta sanya hannayen ta ta rungume su a tare ta baya, Lawwali lumshe ido ya yi, sannan ya kama hannun ta ta gefe ya sumbaci yatsun ta,

"Barakana ya akai kin ka san muna nan?"

"Duba ku muke kawai sai na samu nasarar ganin ku anan"

Murmushi suka yi, a tare dukan su,

"Yah Sultan na jiran ki ku tai"

Kamo su duka biyun Lawwali ya yi, ya rungume su a jikin shi da kyau, suka fara takawa a hankali,sannan ya yi kissing goshin kowaccen su, ya ce,

"Ina son ku, ina qaunar ku, ku ne rayuwa ta, ina hwata mu dawwama a tare cikin hwarin ciki, duk da na san hakan ba lallai shi kasance ba, dan kuwa a rayuwa ta kaff na koyi wani abu sabo, ka na naka shirin duniyar ne, Allah shi na maka shirin komawa gare shi,kai d'an Adam, ba zaka taba gama naka shiri ba, shi ko Allah ya gama nashi Shirin akan ka Dan Adam,lokaci ne kawai da ya yi zai kire ka gare shi, kuma dole ka amsa kira nai, ina muku nasiha ku had'a kan ku, ku so junan ku, kuma ku riqe gaskiya da amana, kar ku ha'inci kowa a rayuwa, kuma ku nemi sanin Allah kahin ku bauta masa, da ace nasan Allah yanda ya kamata, da duk abinda ya hwaru bai hwaru ba, amma sai na aje neman ilimin sanin Allah, na nemi duniya, ina roqon Allah ya bar mu tare har a aljanna"

"Ameeen Yah Auwal /Auwal"

Suka hada baki suka fada, Lawwali ne ya sake Sultana ya dan tura baki,

"Ni dai gaskiya Sultyna ban yarda ba, wai shin ke ko dan sweetheart dinnan ko dan honey din nan baki iya ce min?"

Haba me za su yi banda dariya, shi kuwa tafiyar shi ya fara, ya na ta fadan rashin jin dad'in shi akan kiran shi da Auwal da Sultana ke yi, ba dan sunan soyayyar nan.

Bin shi ta yi da gudu, dan ya kusan isa filin wajen nasu, ta kama hannun shi ta ce,

"Zan fada maka wani suna mai daaadii, amma ba yanzu ba, sai mun koma gidan mu"

"Ni dai yanzu nake so"

"Ah ahh ba yanzu ba"

"To ke Aunty Sultana ki sanar da shi mana, ba a fa jinkirta bayyana soyayya, sai wata ta kwace miki shi"

Kukan shagwaba Sultana ta saka, ta na nuna Mubaraka,

"Ka gan ta ko? Har ta hwara yi min fatan kishiya ko shekara ban yi ba"

Dariya kowa ya ke yi a wajen,Sultan kuwa hankalin shi ya tashi, dan maganar da Mubaraka ta yi sai ya ji kamar da shi take, duk da bai ga alama ba,abinda bai sani ba kuwa shi ne, Mubaraka da shi take, amma ta yi kamar bata san ma ya na wajen ba, ta na so ta san shin hasashen ta gaskiya ne? Ya na son ta ko dan ta na son shi ne ya sa take ganin kamar ya na son ta?

Sallama Lawwali da Taheer suka yi, Taheer na qoqarin barin motar Mubaraka a nan, Lawwali ya ce ya je da ita, ya dinga kai yara makaranta, godiya ya dinga yi sosai, sannan ya cire yar qaramar jakar shi daga motar da za akai shi tasha ya mayar a wadda suka zo da ita.

Sallama ya dinga yi da mutanen wajen d'aya bayan d'aya,sai da ya zo kan Sultan ya rage murya ya ce,

"Kar ka tsaya kallon ruwa kwado ya maka qahwa wallah"

Kada kai Sultan ya yi, cikin yaqe, dan gaba d'aya hankalin shi ya tashi, ga dai Mubaraka ba wata babba ba, amma kwarjinin ta ya cika masa ido matuqa........

*Washhh na gaji,amma ya kuke gani mutanen kirki, shin ya kamata Sultan ya bayyana soyayyar shi a dajin Oga, ko kuma ya bari sai sun shaqi iskar gari???*

💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻

BY HAERMEEBRAERH

PAGE 59:

Taheer ya tafi  da rabin awa, Sultana ma su ka yi haramar tafiya, zaune suke a cikin mota ita da Sultan, sai wanda zai kai su, dan ba za su gane hanyar fita ba.

Ido Sultana ta zubawa Lawwali kamar ta ce masa su je tare, ba ta so su rabu ko na awa guda ne, amma ta san ba ta da wannan damar, in ba shi ya sakko da kan shi daga fushi da Gwamna ba, ba wanda ya isa ya ce ya sauka din, to wataqila sai Mubaraka .

Mubaraka ta gama yadda da cewar hasashen ta na Sultan na son ta qarya ne, hasashen farko na ita din bata kai wadda zai so ba shi ne gaskiya, sallama ta musu, zuciyar ta na matuqar quna, ta bar wajen, za ta koma dakin ta, dan a yanzu ba ta so ta bude baki ta yi magana, za ta iya fashewa da kukan da ya tokare mata wuya.

Muryar shi ta ji a bayan ta, cikin sanyi ya kira sunan ta,

"Mubaraka"

Bata gasgata kunnen ta ba, dan haka bata juya ba, a zaton ta gizo Muryar shi ke mata, saboda ta na tsananin so ya kira ta din dan ya furta mata kalmar so.

Tafe take shi kuwa binta yake, tun da ta juya ta fara tafiya ya kasa samun sukuni, kasa jurewa ya yi, ya ce a jira shi, Sultana da Lawwali na tsaye su na kallon shi ya bi ta da gudu.

Maimaita kiran sunan nata ya yi, Ita kuwa a yanzu ta tabbata ba gizo Muryar shi ke mata ba, dan haka tsayawa ta yi cak, bakin ta dauke da murmushi, da hope din son jin kalmar so daga bakin shi,idanun ta taf hawaye,

"Mubaraka, na kasa tafiya ba tare da na bayyana maki saqon da zuciya da gangar jiki na ke ta bani ba, Mubaraka ina son ki, I love u so much, tun randa na fara dora ido na akan ki a gidan mu, na ji wani baqon lamari ya darsu a zuciya ta game da ke, ban fahimci ko me ne shi ba, saboda ni baqo ne a fagen so, tun daga lokacin nan ba ranar da za ta zo ta wuce ban tuna ki ba, amma na bar wa zuciya ta, dawowar ki daga Kano, na ga kin qara girma, kin qara nutsuwa sai na ji abinda nake ji game da ke ya na nunkuwa a rai na, a yanzu na tabbatar da cewa, ke kadai nake so, ke ce macen da na ke jira, shi ya sa na kasa kula kowacce mace da sunan soyayya"

Wata ajiyar Zuciya suka sauke kusan a tare, Mubaraka ta ji dadi kwarai, wanda ba shi da misali,Sultan kuwa ji ya yi kamar an sauke masa wani babban nauyi da ya jima ya na dauke da shi akan shi.

Juyawa ta yi a hankali suka hada ido, cikin jin kunya ta sauke nata idon,sannan ta saki murmushi, shi ma ita yake kallo, cike da so da qauna,amma ya tabbata da ta na kallon shi ne tun dazun da ba zai iya furta kalaman da suka dinga fita daga bakin shi ba kamar ruwa.

A hankali ya ce,

"Baki amsa min ba, kin karbi soyayya ta, ko dai ban miki ba ne?"

Da sauri ta kalle shi, daga sama har qasa, sannan ta ce,

"Wacce mace zaka ce wa ka na so ta ce bata son ka Yah Sultan?"

"Macen da ba ta son na miji mai kama ta, ko mai irin halaye na mana Mubaraka"

"To ni dai kamannin ka, da halayen ka duk sun yi min, ba ka da makusa a iya sanin da na maka"

"Hakan na nufin ki na so na kenan?"

Daga kai ta yi, ta juya cikin sauri ta nufi hanyar dakin ta, kallo ya bi ta da shi, Lawwali ne ya dafa shi, ya ce,

"Tau baban soyayya, tunda ka qare aman zucciyar ka, yi hankuri ka dena kallon qauna ta haka nan, kar ta faɗi"

Dariya Sultan yayi,ya ce,

"To babban Yaya za a bani?"

"Shi kadai ne buri na tun farko ,kuma gashi kun had'a kan ku, ya na daga cikin sharadin da nake da burin mahaifin ku ya cika min, sai ga shi kun hada kan ku da kan ku, Allah shi sanya albarka cikin wanga lamari"
Chapter 80 · 0% Book details