← Book details A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 93

Sashe 76

A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Barakana tashi mu tai, mun ji, mun amince, ku ba iyayen mu bane, mun yarda ba ku son mu, ba ku damu da mu ba, za mu rayu ko ba ku, mun kuma godewa Allah da ya nuna mana gaskiya, dan haka ku zauna ku ci gaba da rayuwar da kuke kamar ta dabbobi, yau ko dabba ta haihi d'a ta na so nai, ta na kare shi daga miyagun da za su cutar da shi, ta na bashi abinci, amma ku...ku ban san mi zan kira ku da shi ba"

"Yah Auwal ya isa haka, kar ka je ka jawo Allah ya yi hushi da kai, Iyaye na da girma da daraja, dole ne mu kyautatawa musu, ko muna so ko bama so, ko da basu zamo nagartattu ba, ko da kuwa kahirrai ne, ka yi hankuri mu tafi, kar ka hwadi kalmar da zata sanya Allah shi yi hushi da kai, duk yanda suke iyayen mu ne, dole mu yi musu biyayya"

Kallon Dan Talo ya yi, ya ga yanda ya ke ta kuka, shi abun ma dariya yake bashi, to kukan me suke?

Kudi ya kwaso a aljihun shi ya wurga masa, Mubaraka ta yi saurin kama hannun shi, ta na hana shi wulaqanta iyayen shi,domin ta ji wa'azi sosai akan girman iyaye,durqusawa ta yi ta na kwashewa ta na zubawa Baban nasu a jikin shi, a ladabce, wajen su Lamishi ya je ya wurga masu kudi suma, sanan ya kalli Mai Buruji ya ga yanda take kuka sosai.

"Ki dena kuka yanzu, kuka na tahe zuwa nan gaba, ba dai kin biye mata ba, dan kar ta dake ki, yanda kuke yi a baya, ki sha kashin banza, shi ne ki ke qin yi wa diyan ki tarbiyya ko? Ta saki nata sun bi duniya, kema kin saki naki ko? Da kyau, kuka na nan tahe, ki bar taya ta kuka, naki na tahe,"

Kama hannun Mubaraka ya yi, suka bar gidan, cikin tsananin fushi, basu zame ko ina ba sai gidan da ake ajiyar No 1........................

*Jama'ar kwarai gobe ranar Arfa..dan Allah kar ku manta a ajiye duk wasu ABUBUWAN da ba su da mahimmanci kamar yanda alhazai suke can Makka suke kwasar lada mu ma mu kwashi namu a gida, a yawaita karanta LA'ILAHA'ILLAHU WAHDAHU LA SHARIKA LAHU LAHULMULKU WALAHUL HAMDU WA HUWA ALA KULLI SHAI'IN QADEER.*

*Happy sallah in advance love you mutanen kwarai*

💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻

BY HAERMEEBRAERH

*Assalamualaikum barkan ku da sallah 'yan uwa musulmi...Allah ya maimaita mana mai yawa mai albarka...Allah ya karbi ibadun mu...ina nan ina jiran barka da sallah na😃❤️*

PAGE 56:

Mubaraka dai na zaune a mota, har wannan lokacin ba ta daina sharar hawaye ba, hawayen da ke zubo mata daga can qasan zuciyar ta ya ke tahowa, rayuwar da suke ciki bata da suna, balle fassara, ina ma ina ma su na da iyaye na gari? Lallai da ba wanda zai fi su jin dad'in rayuwa ,amma inaaa, rayuwa na ta gara su, duk inda ta kad'a can take kai su, su kuwa bin ta suke a koda yaushe.

Hanyar da ya ke shiga sabon waje ne a wajen Mubaraka , Ita dai nata ido, bata ce komai ba, har suka tsaya a wani madaidaicin gida.

Fita ya yi, ya zagaya ya bude mata qofar, sannan ya kama hannayen ta biyu, ya tsaida ita a gaban shi, fuskar ta ya d'aga ya na kallon cikin kwayar idanun ta, hawaye ya gani kwance su na rige rigen fitowa, wani abu me zafi da rad'ad'i ya ji a zuciyar shi ya na dukan shi , cikin kad'a kan shi ya ce,

"Ya isa haka nan, daga yau in shaa Allahu ba ki koma yin kuka Barakana, indai su ba za su so mu kamar kowanne iyaye ba, na maki alqawalin zan so ki kamar yanda iyaye nagari ke son d'iyan su, zan so ki kamar yanda yaya nagari yake son qaunar shi, Barakana duk abinda ki ke so na zamo miki ni Lawwali na maki alqawalin zama shi, abu guda ni ka so wajen ki, shi na ki dena kuka, ban san ya zan fahimtar da ke kukan ki ke yi min ga zucciya ba,"

Kwantar da kan ta ta yi a qirjin shi, ta qanqame shi, ta na jin dikkan soyayyar da ya lissafa na shigar ta, tabbas Lawwali babbar katanga ce a rayuwar ta, bata fatan abinda zai raba ta da shi duk duniya, za ta yi ko mene ne da bai sabawa Allah ba dan ganin ta tabbata tare da shi cikin farin ciki.

Kama hannun ta ya yi, suka shiga ciki, yaran oga na ganin shi suka hau fara'a, domin tun kan ya zo ya sanar da kowa shirin shi, ya kuma yi wa kowannen su alkhairi, No 1 aka kira ya fito, gaba daya Mubaraka bata gane shi ba, dan kuwa ya zama gurgu, ya daku matuqa, ya azabtu, duk jikin shi ya nuna alamar wahala da gajiya da azabtuwa.

Godiya ya yi wa Lawwali da ya kauda kai daga ganin shi, ba dan alqawarin da ya yi na dena kisa ba, tabbas da No 1 ba zai bar wajen nan da rai ba, amma ko gurgantakar da ya samu a qafar shi ta hagu ta ishe shi tuna abinda ya aikata har qarshen rayuwar shi.

Kallon da ya kure Mubaraka da shi ne ya sa ta gane ko wane ne, ai kuwa da sauri ta labe a bayan Lawwali, Lawwali kuwa a harzuqe ya kai masa shaqa,

"Shin kallon mi ka kai mata? Ba ka tahiya sai na sauya ra'ayi na na sa harsashin bindiga na hwashe ma kai?"

Da sauri Mubaraka ta riqe hannun shi, amma har a wannan lokacin bata fito sosai inda No 1 zai gan ta ba, ta na labe a bayan Lawwali, hakan ke baqanta ran Lawwalin, No 1 kuwa zubewa ya yi a guiwowin shi duka biyun, ya duqar da kan shi,sai da mubaraka ta saki qara ta yi baya ta sake qanqame Lawwali.

Hakuri No 1 ya fara bata, cikin wata iriyar murya mai son yin kuka, Lawwali ne ya janyo Mubaraka gaban No 1 ya ce,

"Sanya ijiyar (idon) ki cikin na shi, ki gan shi a qasqance a qasa a gaban ki,ba shi iya miki komai wallah, in har baki dena jin tsoro nai ba zan kashe shi yanzun nan, dan ba zan bar abinda ki ke tsoro ya ci gaba da yawo a doron qasa ba"

A hankali ta fara jin tsoron No 1 na barin jikin ta, ko dan kar a kashe shi, dole ta ware, sai da Lawwali ya ga Mubaraka ta daina kyarmar da take sannan ya sa aka tusa qeyar No 1 ko na mota ba wanda ya bashi, ya na ji ya na gani aka rufe gidan,aka bawa Lawwali key, suka shige motocin su suka bar shi a wajen.

Su Lawwali basu tsaya a ko ina ba sai asibiti.

"Yah Auwal waye ba lafiya?"

"Mu tai ki na ganin ko waye"

Asibiti ne na hamsaqai, riqaqqun masu abun hannu, Mubaraka sai kalle kalle take, sai da Lawwali ya samo dakin da za su, ya ja hannun ta suka tafi, 'yan sanda ne guda biyu a bakin qofar dakin, su na tsaron wajen, Lawwali bayani ya musu da cewa shi surukin mara lafiyar ne, sannan suka barshi ya shiga.

Hajiya Ikee na ganin shi ta tafi da sauri cikin kuka ta tsugunna a gaban shi,

"Dan Allah Lawwali ka yi hankuri, ka yahe muna, ka tausaya wa halin da Daddyn Sultan ke ciki, ba shi iya magana, qafar shi ta shanye, hannun shi guda ba shi motsi, gashi har yanzu damuwa bata bar shi ba, rashin ganin yaran shi na damun rayuwar shi,duk daren duniya da ihu, da kururuwa muke kwana, kamar ya na ganin wani abu, gashi ba shi magana balle mu gane me ya ke gani, "

Dariya Lawwali ya yi sannan ya ce,

"Me zai gani ko banda aljannun da ya ke wa tsafi? Bai basu jinin bil'adama ba kwana biyu, ba dole su biyo sahu ba? In ba ku je aka rushe dakin da ya gina ya na tsahi cikin shi ba,kuma baku yi wa aljannu sadaka ba walle yana cikin tashin hankali, kad'an ya fara gani"

"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un, yanzu ya za mu yi?"

"Ina nissani? Na so gobe yaran ku su zo ganin ku, Sultan ya dawo gare ku, amma 'yar ku ta lalata shirin, ta ci amana ta, ta qone duk wata shaida da zan hannintawa hukuma, dan mu karbi hukuncin mu daidai da abinda muka aikata, amma ta qone su, dan haka ba za su dawo yanzu ba,"

Kuka Hajiya Ikee ta fashe da shi ta ce,

"Yau na shiga uku ni Ikileema, ina zan sa rayuwa ta? Yanzu Lawwali ba wata alfarma da zaka yi muna mu gan su?ka duba halin da Daddyn Sultan ke ciki"

Dariya Lawwali ya yi, sanda ya kalli yanda Excellency ke dalalar da yawu, ya kasa magana sai hawaye.

"Ke walle wanga aljannu ka damun shi ba kewar d'iya nai ba, in ku na neman maganin aljannu ku nema, sai an jima"(ke wannan aljanu ke damun shi ba kewar yaran shi ba, in zaku nemi maganin aljanu ku nema se an jima)

Mubaraka ce ta ce,

"Hajiya ki gafarce ni, ni qarama ce, amma ina mai baku shawara, da ku nemo mallammai na kwarai,wanda sunka san Allah, su yi addu'a aljannun su tafi, amma in kuka yi musu yanka, za su dawo su ce wani abu suke so, ko rayuwar wani a cikin ku, Allah shi kiyaye"

Ai Hajiya ikee na jin rayuwar wani a cikin su, ta tsure, kallon Gwamna Halliru ta yi, ta ce,

"Mu na zaman zaman mu da rufin asirin mu ka doko muna siyasa, gashi nan, mu na ganin ibtila'in rayuwa, ba mulkin, ba dukiyar, ba d'iyan mu, ga wani tashin hankalin yanda za mu rabu da aljanun da ka jajibo muna"

Lawwali kam dariya kawai yake kamar wani wawa, cikin surutai da sambatu suka bar Hajiya Ikee, Gwamna Halliru kuwa na kwaranyar da hawaye ta gefen ido.
Chapter 76 · 0% Book details