← Book details A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 93

Sashe 27

A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Humm Auwal kenan, kai a ganin ka zan iya rintsawa? Bayan zuciya ta da ƙwaƙwalwa ta su na hango min abinda ban gani ba? Zuciya ta na hango min kukan yara ƙanana, da mata,da mazaje, zuciya ta na hasko min yanda jini ke malala na dan Adam ba dabba ba,ba tare da haqqin su ba, anya mahaifi na mutum ne kuwa? Anya wadan da suke aikata kashe kashe da zubar da jinin al'umma mutane ne kuwa?anya akwai zuciya a qirazan su kuwa?anya suna tunawa da cewa kamar yanda suke daukan rayukan bayin Allah suma watarana ran su za a dauka? Anya su na sane da cewa akwai wuta akwai aljannah? Anya su na tunawa da cewa su na da mahalicci wato Allah, mai yawan rahama, da kuma yawan azaba? Anyaa????"

*Makaranta Sultana na neman amsa*

A GARIN MU

WRITTEN BY HAERMEEBRAERH

PAGE 24:

Wata iriyar zufa ce ke karyo mishi, wadda ta sanya shi tunanin anya ya kunna AC ma kuwa, kallon saitin AC din ya yi, ya ga a kunne take, tashi ya yi ya kunna fan, sannan ya koma ya zauna, ya na sauraron yanda Sultana ke karanta masa abubuwan da ko Mubaraka mai yi masa nasiha da wa'azi kullum, bata taɓa fada masa wadannan kalaman masu matuqar taba zuciya ba.

Cikin tsagaita wa da kuka sultana ta ce,

"Allah shi ne mafi sani game da mutanen nan da Daddy ke aiki da su,su ke lahanta mutane, suke kassara su, suke illata su,in masu shiryuwa ne, Allah ya shirye su, in ba masu shiryuwa bane Allah ya musu abinda suke wa bayin shi, "

Shiru Lawwali ya yi, dan bai isa amsa wa da ameen ba, tunda ya san mene ne suke wa yaran wasu, jijiyoyin kan shi ne suka tashi rudu rudu, qit ya kashe wayar,gaba daya ya kashe ta.

Yawo ya fara yi a dakin, me zai sa Sultana ta musu wannan addu'ar , in wani abu ya samu ahalin shi fa? (Na wani bnza na ka dukiya kenan).

Ranar Lawwali bai samu bacci ba sai gaf da suba, bacci kuwa ya sha me kyau, bai tashi ba sai qarfe goma na safiyar ranar.

Sultana kuwa dama ta yi waya NGO akan ba zata je ba, bata jin dad'i, su kula da wajen, da duk wanda ya je neman taimako, abinda ya fi qarfin su su sanar da ita.

Lawwali ma sai da ya tashi ya ga message din ta, ji yayi hankalin shi ya tashi, me ke damun ta? Dole ne ya je ya duba ta.

Wanka ya dauka, ya sanya wasu riga da wando,na shadda sun yi mishi kyau sosai, ba hula, wayar shi da yan kudi, sai makullin mota ya dauka, ya fita, kafin ya je wajen ta, sai da ya shiga gari, ya siyo mata kayan kwalama na Bature, duk ya ma rikice ya rasa me ya kamata ya siya, haka dai ya siyi banza ya siyi wofi ya ja mota sai gidan Gwamna.

Ko da ya isa ya tarar da securities da yawa, sanin ko shi waye a wajen gwamna ne ya bashi damar shiga ba tare da wani bincike ba, gwamna Halliru da Hajiya Ikee ba su gida, Sultan ne da Sultana sai masu aiki, ranar Mai buruji da Lamishi duk sun samu zuwa, har a sannan qafar Lamishi bata qarasa warkewa ba, dan haka Sultan ya hana ta yin komai, sai godiya take, ya ce ta ci gaba da turo Mubaraka, ba se ta zo ba, tunda ba lafiya.

Sultana na zaune kusa da Sultan, ya yi tambayar duniya ta qi sanar da shi abinda ke ran ta, saboda ba ta son ya tsani Daddyn su kamar yanda ta tsani ganin shi,ba ta so ta b'ata kowa a rayuwar ta, ta fi so ta fadi alkhairin mutum, in ba ya zama dole se ta fad'i sharrin mutum ba, wannan ba yanda zata yi,balle mahaifin su, bata fatan Sultan ya sani, zuciyar shi zata karye sosai, saboda yanda yake son mahaifin nasu sosai.

Hawaye ta share sannan ta yi murmushin yaqe ta ce,

"Yah Sultan ba abinda ke damu na, ciwon kai ne kawai, in ina da matsala ka sani kai ne mutum na farko a duniya da ke fara ji"

"Haka ne, amma Ni ma kin san na fi kowa sanin ki, ba ciwon kai bane kadai damuwar ki, akwai wani abu da ya ke faruwa, wanda ki ke boye min"

Bude baki ta yi dan yin magana wayar ta ta dau qara, ko da ta ga sunan Auwal, sai ta samu kan ta da jin dad'in hakan,domin a daran jiyan ta yi ta sake gwada kiran shi bai shiga ba, har da safen nan ma ta kira bai shiga ba.

"Assalamu alaikum,"

"Wa'alaikumussalam, Ran ki shi dade ya ki ke? Ya jiki? Ina hwata dai kin samu lahiya ko? Na taho na duba jikin ki, tunda kin ce baki da lahiya"

Miqewa ta yi da sauri ,ta isa gaban window'n da ake hango farfajiyar gidan, ganin shi tayi tsaye da ledar shopping a hannun shi, murmushi ne mai kyau ya kwace mata, ta jingina da ginin wajen, sannan ta ce,

"Lallai ka iya zuwa dubiya, haka ake zuwa dubiya an sha gayu? What if mara lafiyar ta rikice fa?"

Waige waige ya fara ya ga ta ina zai hange ta, bai gani ba,  cikin sa'a ta sake leqa shi suka hada ido, dariyar shi da ke rikita mata kwanya ya saki, sannan ya shafa kan shi, tare da lumshe ido ya sauke su fess akan ta,

Sultan ne ya isa gaban ta, ya harde hannayen shi a qirjin shi, ya na kallon ta da mamaki, dazu fa kuka take.

Su na hada ido, ta bar wajen za ta hau sama, ya riqe hannun ta, a hankali ta ce,

" ka shiga parlour na baqi gani nan zuwa"

Kashewa Lawwali ya yi, ya shiga gidan ya shige har inda aka ce masa, ya zauna zaman jiran ta.

Ita kuwa qoqarin gudu take Sultan ya riqe ta,

"Ina zaki je baki min bayanin sauyawar ki ba a lokaci qanqani? Na fi qarfin awa biyu ina tare da ke, kina ta hawaye, kin kasa fadan komai, yanzu daga amsa waya sai ki fara dariya?"

Shiru Sultana ta yi, dan ko me zai faru ba zata sanar da shi mummunan sirrin mahaifin su ba, gwanda ta tonawa kan ta asiri, akan ta fada masa gaskiya.

"Yah Sultan, i am in love, ....i am in love with my driver, amma ban sanar da shi ba, shi ma kuma da alama ya na so na, bai sanar da ni bane kawai, Yah Sultan ina cikin damuwa ne saboda na san ba wanda zai goyan baya a gidan nan,labarin soyayya ta ina hango qarewar shi tun kafin ya fara"

Bilhaqqi yanzu kuma kukan hasashen da ta yi take yi,

"Sultana tabbas zabin ki ba mai karɓuwa bane a wajen su Hajiya da Daddy, amma a waje na karbabbe ne, in dai ki na son shi, ya na son ki, zan tsaya a gefen ki, har sai kun cimma burin ku"

Qanqame hannun shi ta yi cikin nata, tare da fadin,

"Na gode,"

Shafa kan ta ya yi, sanan ya ce,

"Wannan shi ne abinda zan miki, duba da yanda iyayen mu suka maida ni mara mamora a cikin al'umma, ba na aikin komai, ana kulle na kamar mace, ba na baki wata gudunmawa a matsayi na na yayan ki"

"Yah Sultan kar ka ce haka, soyayyar ka a matsayin dan uwana ta wadatar da ni komai,"

Cikin ran ta kuwa cewa ta yi,

'Dole iyayen mu su yi kullen mu, domin sun san me suke aikatawa, su na tsoron kar wani abu ya same mu,'

Sai da ta ɗan gyara fuskar ta ta sanya sutura mai kyau da ta rufe jikin ta sosai, sannan ta isa wajen Lawwali, sassanyan qamshin ta ne ya fara yi masa maraba, kafin kyakkyawar fuskar ta  ta masa sallama.

Sake baki ya yi ya na kallon ta, anya da gaske bata da lafiya? Shi be ga alama ba,

"Kallon nan na ka na neman ya yi min yawa wallah"

"Anya kuwa? Ke taba jin inda wata ya ce wa mutane kallon da suke mishi ya yi yawa?"

"To ai Ni ba wata bace"

"Kin fi kama da wata mai haske shi ya sa na yi misali da wata, sanyin ki kuwa ya fi kama da ruwan qorama, shi ne ba shi cutar da kowa sai amfanarwa"

Kunya ce ta kama ta, tabbas ta gama yarda da cewar, abinda ke zuciyar ta shi ne a zuciyar shi,

"To dubiya kacce ka taho, amma ba ka yi min ya jiki ba"

"Ban ga alamar ciwo a tattare da ke ba, sai ma alamun cikakkiyar lahiya, amma, ya jikin ki? Ina hwatan da sauqi ko?"

"Na ji dama, ciwon da ke jiki na ba a zahiri yake ba, a badini ne, domin kuwa zuciya ta na quna matuqa akan abinda zai iya koma ya  faru da mutanen can, da kuma abinda ka hwaruwa a garin nan, da ma Nigeria baki daya"

"Hummmm"

Shi ne kawai abinda Lawwali ya iya cewa, nan da nan ya tuna addu'ar da ta musu, cikin sauri kar a zurfafa magana ta sake yanko wata addu'ar ta cimmusu baki daya ya ce,

"Ran ki shi dade, ina fatan ban yi karambani ba, na je zan siyo ma mara lahiya kayan dibiya, na rasa mi zan kawowa, na kwaso wadannan"

"Na gode sosai, amma da baka wahal da kan ka ba"

"Babu komi, indai ke ji dad'in kyauta ta, farin ciki na zai qaru"

"Lallai ka yi farin ciki domin kuwa na ji dadin kyautar ka"
Chapter 27 · 0% Book details