Sashe 11
A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ko da ta ga isa, ta ga yanda ya bata rai, ta san ba nasara, wani malolon baqin ciki ne ya tokare mata maqoshin ta, cikin murya mai rauni ta ce,
"An gane su?"
"Ba ke ce ki ka tafi nemo su ba? Ke zan tambaya an gan su ko ba a gan su ba"
Kafe shi ta yi da jajayen idanun ta, sannan ta ce,
"Yanzu tsakanin ka da Allah Baban Amina ba ka tafi neman diyan ga ba? Ni kad'ai zan ta neman su? Innalillahi wa inna ilaihirraji'un, Allahumma ajirni fi musibatee wa aklifnee khairan min ha, ya Allah ka bayyana min yara na cikin qoshin lafiya da aminci da salama"
Ta na taka qafarta wajen gate din ana kawo wutar lantarki, ihun yara har da wasu manyan ne ya karade kunnuwan su, hasken da ya bayyana ne ya sanya Hansatu jin kwarin guiwar ci gaba da neman su.
Gida gida haka ta dinga shiga neman su, wasu su tausaya mata, wasu su dinga ganin sakacin ta.
Har sha dayan dare Hansatu na yawo, ita da wasu daga matan unguwar da suke da mutunci, wanda ta zaci sun san ta za su taimaka mata wajen neman yaran ko leqe zuwa qofar gida ba su yi ba.
Hankalin ta ya tashi ainun, isa kuwa wajen mazajen unguwar ya tafi ya na cigiya, duk wani lungu da saqo na unguwar an duba ba yaran,shawara aka tsayar akan washegari a je akai cigiya gidan talabijin da rediyo, masu wayar cikin su tun a daren suka bi ta gida, ta na da wasu hotunan yaran da aka taba daukan su a Makarantar boko,nan akai zooming fuskar su aka dauka, aka watsa social network.
Hansatu ji take me za ta zauna a gida ta yi? Bata san a wanne hali yaran ta suke ba?
Tashi ta yi, ta yi alwala ta yi ta nafila, ga yunwa na cin ta, cikin ta se qara yake, qarshe da tsayuwar ta gagare ta, a zaune ta qarasa sallar ta.
Isa kuwa banda minshari ba abinda ya ke ja, daga farkon gado, ya koma qarshe, daga qarshe ya koma tsakiyar gadon har asuba ya na baccin asara.
Asshibi kuwa tunani da tausayin Hansatu ya gama nuqurqusar ta, ta sha kuka ta gode Allah, wannan tausayi nata ne ya jawo masu barin unguwar da suke a baya, da an rasa yara ko kuma ta ji an sace Wani ta dinga damuwa kenan, wasu sun danganta hakan da rashin haihuwar ta, wasu sun danganta hakan da ganin ido, duba da cewar bata da halin kirki itama, amma mutane na manta cewa dan Adam tara yake, bai cika goma ba, dik yanda ka kai da mugun hali, ba za a rasa mai kyau ba a tare da kai, haka duk yanda ka kai da kyakkyawan hali, ba za a rasa mummuna ba ko yaya yake a tare da kai.
***********************
Abu kamar wasa qaramar magana na neman zama babba, yau sati Daya da kwana uku, ba labarin su Amina ba motsin su, Hansatu ta fita daga hayyacin ta, mutane ko ta ina zuwa ake masu jaje, labari ya kai har wajen Hajiyan Hansatu, abin d'a da mahaifi, sai ga ta ita da yayan ta sun je, cikin wata rantsattsiyar mota mai numfashi, duk wanda ya ga Hajiyan Hansatu zai mamakin ta na da diya amma ta bar ta take a wulaqance haka, dukiya sai kuka take a jikin ta, duk da ba ta wani ci ado ba, a ganin ta, amma a ganin idon talaka ta ci ado ne sosai .
Hansatu ta dake, ko kuka bata yi, sai tasbihi a zuciyar ta, ganin Hajiyan ta ne ya sanya bakin ta rawa, a hankali kwallar da ta cika ta tumbatsa a idon ta ta fara kwaranya, zama Hajiya ta yi a kusa da ita, ta kama hannun ta, itama kwantar da kan ta tayi a cinyar Hajiyan nata, jaje Hajiya ta mata,ta amsa da kyar, cikin kuka ta ce,
"Hajiya yara na duka fa aka ɗebe man, ba guda ba, ba biyu ba, dika ukun, Hajiya ina ji a jiki na, mutuwa zan yi, hankali na ya fara barin gangar jiki na, zuciya ta tafi ciwon da aka sanyawa gishiri zafi, tafi gulandon da aka fama ciwo Hajiya, na rasa inda zan saka raina Hajiya ,"
Kwalla Hajiya ta mayar, domin ba wanda bai tausaya wa Hansatu ba a wajen, hatta da su Lamishi da suka shiga yi mata jaje sai da zuqatan su suka raunana.
"........dan girman Allah kar ku cutar da yaran nan, ku taimake Ni ku dawo mana da su, mahaifiyar su ba ta da isasshiyar lafiya, shin wai ku ba ku da imani ne?"
A guje Hansatu ta qarasa waje, dan jin me mijin ta ke fadi, ta zaqu ta ji me ke faruwa, a handsfree Isa ya Sanya wayar, kowa da ke wajen ya kasa kunne, Hajiyan Hansatu kuwa kamar ta amshe wayar take ji.
Daga wayar ne mai magana ya ce,
'Taurin kan ka ne zai sa na kashe daya daga yaran yanzun nan, tun shekaran jiya na ce ka aiko milliyon goma, ka tsaya neman ragi, Ina ruwana da talaucin ka da ka ke fada? Bani da lokacin jiran ka, in baka kawon milliyon goma ba nan da kwana uku, gawar yaran ka za ka gani a titi'
'Dil Dil Dil Dil'
Shi ne qarar da wayar ta yi, sai a sannan ne mutanen wajen suka kula Hansatu ta suma.
Ruwa aka yayyafa mata sannan aka kaita daki,ta na tashi ta dinga kuka,
"Yanzu baban Amina tun da jimawa aka ce akai kudi ba ka fadan ba? Me gadon nan yake ko gidan nan da muke ciki suke? Da ba za mu siyar ba? Yara na sun fi min komai na duniyar nan, ka nemo mai saida gidan a siyar dan Allah ka amso min yara na"
Kuka take sosai, isa na share hawayen qarya.
"Hansatu kaina ya kulle ne, kwata kwata na manta a gidan kan mu muke ma, bari na je na siyar da gidan na aika musu kudin"
Miqewa ya yi zai fita, Yayan Hansatu ya ce,
"Dakata, in kun saida gidan yaran sun dawo ku zauna a ina? Muje na rubuta maka cheque ka karba ka fidda kudin ka basu"
Isa zubewa ya yi gaban qanin bayan shi ya na godiya, kamar wani soko, Hansatu kuwa kukan farin ciki take tayi, ko ba komai yaran ta za su dawo gida lafiya da yardar Allah, kuma gashi ta shirya da iyayen ta.
Ana bama isa cheque ya wuce banki ya cire kudin , ya nufi maboyar su shi da mijin Asshibi, tun a hanya ya sanar da shi ya na tafe.
Kamar yanda suka tsara kuwa Isa ya bashi kaso daya cikin kaso uku na dukiyar nan, sannan ya tafi ya boye nashi kason a banki.
Sai da ya gama komai sannan ya koma ya debi yara suka nufi gida.
Yara fess da su, Ahmad har dan kumatu ya yi, saboda kullum sau uku suke cin abinci a rana, Amina kuwa dake ita ta na da wayo, ta rame ta yi duhu, saboda kewar Umman su.
Ko da suka isa gida ranar ba wanda bai kukan farin ciki ba, yanda Hansatu ta kidime da murna da sujjada ba adadi dan godewa Allah, abun ya sanya mutane hawaye.
Qanqame su ta yi tsam a jikin ta kamar za ta maida su cikin ta.
Labari kan labari haka su Bilkisu ke bawa Hansatu da mutane, Amina kuwa ta lafe jikin Umman ta, can kamar daga sama suka ji ta ce.
"Umma kin ci abinci kuwa? In baki ci abinci ba umma ki ci abinci, Ni ma na kasa cin abinci saboda ina tunanin ki, umma ina ta tausayin ki, ina ta tunanin irin halin da za ki shiga idan ki ka rasa mu"
Kuka mai maqaqi a wuya ne ya taso ma Hansatu ,
"Amina ban ci abinci ba, ruwa da koko kawai nake iya sha,shi ma ba ko yaushe ba,Amina inna rasa ku mutuwa zan yi, ba zan iya jure rashin ku ba"
Ai kuwa ba bata lokaci Hajiya ta zaro kudi, ta bawa Isa ta ce a siyo kayan abinci, a siyo risho da kananzir a zo a dora abinci, su ci su qoshi,ita za ta wuce gida, tunda an ga yara.
Mutane daya bayan daya ake shiga taya su murna, wasu da suka ji labarin mahaifiyar Hansatu ce ta biya milliyon goma sun sha mamaki,dama su din masu azziqi ne amma take a wahale?
Isa ya samu kan gaba, ya dinga zagin iyayen Hansatu , ya na nuna wa mutane ai ba su da tausayi, dan ta auri talaka suka guje ta....
Anyaaa kuwa Isa .......
A GARIN MU
WRITTEN BY HAERMEEBRAEH
PAGE 12:
Mubaraka na ta sauri Dan ta kammala wanke-wanken da take yi, ta wuce islamiyya, Lamishi da Mai Buruji Suka koma gida daga gidan Isa.
Sannu da zuwa ta musu, sannan ta shigar da kwanukan ta kitchen,
"Hummm ke ga ikon Allah ko? Ashe iyayen Hansatu attajirai na, sun ka barta ta na cin azabar Isa ko? Rayuwar duniyar ga na ban mamaki, Wai mutane su dinga wahal da yaran su da kan su"
Murmushi Mubaraka ta Yi, Wai Lamishi ke ganin laifin wasu iyayen, ita ya take mata? kenan a ganin ta duk kyara, tsangwama, da kyamar da take nuna Mata Abu ne Mara illa,ta manta ita ma haka take mata azaba, take wahal da ita kamar ba ita ta haife ta ba.
Daki ta Shiga ta bar su,su na ta jajen abinda ya faru.
Shiri ta Yi tsaf, ta Yi kyau abin ta, uniform din ta fes kamar ba ta zama saboda tsafta.
"Umma na tafi makaranta"
"To sannu Uwa ta, ke yanzu baki raba kan ki da Wagga wahala ko? Makarantar nan dai ban ga mi ta ke Yi maki ba gidan duniya , Dan kawai ki tai wajen qawaye ne ai ta d'umin banza da yohi"
"Umma ba haka bane, shi karatu ko ba Kai aikin gwamnati ba zaka Yi na sa Kai, sannan ba zaka zauna da duhun jahilci ba, Umma inshaa Allahu Zaki alfaharin da ilimi na a gaba"