← Book details A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 93

Sashe 57

A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ohhhh Allah na gode maka, ashe da rabon zan daura suhwa a duniyar ga,Allah ya kaimu wannan rana da rai da lahiya"

"Ameeen, ki na da takalme da jikka?"

"Ina da su, amma tun wanda na ci bikin Kareema ne wallah"

"Kayya, ki ce baki da su kawai"

"Sai goben ki taho akwai wanda zan baki, na Mubaraka ne, Sultana tabbata su,"

Wani tsallan bad'ake 'Yabbuga ta buga ta yi baya, ta ce,

"Yo ance miki kwana na na yaqare da zan saka kayan Mubaraka? Banni na tai bukin ga lahiya mu dawo lahiya, ke san halin Lawwali akan abun Mubaraka, walle ba ze ji nauyin yagan rigar mutunci ba gaban kowa, banni na tai da tsohhin nawwa, ai guntun gatarin ka ya hi sari ka bani"

Dariya Mai Buruji ta ke ta yi, bayan ta dasa kujera a gefen Lamishi ta zauna.

"To bid'i wuri ki zauna in ke qare tsallen, matsoraciya, jiya kuwa yattaho, na san yau ma shi na nan tahe"

Rarraba ido 'Yabbuga ta fara, tuna ranar da ya dawo cikin bacin rai ta yi, ta na baccin wahala, takalmin ta ta shura ta ce,

"Too mutanen ga na yi gida, zan bawa bisashe(awaki/tumaki) ruwan yami, rabon su da ruwa tun jiya"

"Ke dai hwadi gaskiya, dan an ce Lawwali na tahe, shi na ki ka son gudu"

"Ko ni ba haka nan na ba, ai ko Allah sanya alheri ina tsayawa na yi mai, zan dai je ne na ba bisashe ruwa"

"To ya yi, jira na doko miki kayan da za ki saka goben"

Lamishi ce ta shiga ciki, ta dakko atamfar ta bawa 'Yabbuga, kaya ne kamar sababbi fess da su, Godiya ta yi ta yi, ta tafi.

Su kuwa suka ci gaba da shirin kayan zuwa biki, har lalle suka tsara za su daura a daren.

***************************

A gidan gwamna kuwa, ko ina ka wurga ido mutane ne, na birni da na kauye, Sultana ta yi mamakin ganin yawan mutane, ko dan ba a taba aurar da kowa a gidan bane, tunda sukai kudi, mahaifin su ya zama Gwamna dangi suka dena shiga jikin su, saboda tsabar wulaqanci da tozarcin da Hajiya Ikee ke musu, in ka ga ta kula wani a dangi, to fa ya na da maiqo,bata bar dangin ta ba, balle dangin miji, kowa ma tabawa take.

Sai gashi mutane sun yi hakuri da halayyar da ta musu a baya, sun zazzo bikin, domin zumuncin Allah ba dan halin ta ba.

Amarya ta sha gyaran jiki da gyaran gashi, duk inda Sultana ta wuce qamshi ke bin ta,a cikin yan uwan su, har da masu taba jikin ta, dan kawai su ji ya yake, tsabar kyaun da ta musu a ido.

Sultan kuwa na can na hada ma Sultana babban surprise din da ya san in ta gani sai ta yi murna sosai da sosai.

Washe gari kuwa da safe tun safiya ake qawata hall din da za a yi bikin na su, duk wanda ya ga yanda aka qawata wajen zai tabbatar da bikin na manya ne ba na qananan mutane ba.

Amarya da ango kuwa kyawun da suka yi ba mai faduwa ba ne.

Lawwali ba shi da abokan da suka wuce abokan shi na cikin daji, sabbin matasan da suka horar suka bari tsaro da gadin dajin nasu, su No 2, No 3 da no 5 su ne manyan abokan ango.

Da yamma kuwa Mota biyu Lawwali ya aika unguwar su, dan ya san sai su Lamishi sun yi gayya, ai kuwa motocin nan sai da aka cika su taf da mutane.

Su Aunty Asma'u, Khadeeja Katuru, Halima (Maman yayana),Khadeeja Jabo, Eeshaa, Maman Jasrah,Aunty Rumma,Ameena Saudia, Su uwar gida Sarautar mata Iyar Ilham, Ashwal, Mom Sawwama, Maman Husnah,Maman Muhseenah,Mum Basheer, kai da dukkan mutanen group din A GARIN MU, sai da suka samu mota guda ta kwashe su zuwa event center din nan.

Amarya Sultana kuwa a zaton ta tunda bata da qawaye Lawwali ne kawai zai je su tafi, sai ta ga an kawo motoci da yawa, da damar su gilashin su baqi ne, har wadda akai wa decoration wato ta amarya da ango, a tunanin ta sauran motocin da ke take musu baya securites ne a cikin su, haka ta shiga motar cike da son ganin irin kwalliyar da angon ta ya yi.

Lawwali ma Allah Allah yake ta qarasa shiga motar ya qarewa kwalliyar da ya hango ta baqin gilashin motar kallo.

Ana budewa qamshin su ya qauraya da na juna, kasa lumshe idanun su suka yi, saboda yanda suke kallon juna.

Kowannen su na godiya ga Allah, da ya haɗa shi da abokin rayuwa kyakkyawa kamar dan uwan shi.

Hawayen farin ciki ne suka fara sauka daga idanun Sultana, tissue lawwali ya miqa hannu gaban mota ya zaro, ya fara goge mata hawayen ta, duk abinnan da suke, masu video da hotuna na ta dauka.

Mai hoto guda daya aka samu ya zauna a gaban motar, da ya ga sun yi abinda ya burge shi sai kuji kyasss kyarasss ya dauki hoto.

A hankali motocin ke tafiya, har suka isa wajen event din, wani irin kidan waqar Hamisu breaker aka saki da ya yi wa amare, Lawwali ne ya fara fita, ya zagaya, ya budewa Sultana mota, ta fita, hannun ta na cikin nashi, kan ta a qasa, ta fara takawa, duqawa ya yi kadan ya mata rad'a a kunne, daga kai ta yi, a lokaci daya ta fashe da wani irin kukan farin ciki, hannun ta ta sanya bakin ta ta na zubar da hawayen farin ciki, ba kowa ta gani ba illa qawayen ta da suka yi karatu da ga na nan gida Nigeria har turawa na can qasar waje, sai tsirarun abokan Sultana da Sultan din kan shi, sun yi ankon baby pink din wani tsadadden material, larabawa da hausawan mu na nan sun yi rolling kan su da mayafai masu adon duwatsu.

Turawan cikin su kuwa an musu dinki daidai da yanayin su, an gyara gashin nan sai sheqi yake, an ci dogayen takalma masu tsini.

Yau kwanan su biyu a Nigeria, Sultan ne ya gayyace su, tare da tsara komai da ya kamata, duk da cewa a qurarran lokaci ne ya samu nasarar tsara abubuwan yanda ya kamata, a hotel din City king hotel Gusau, ya musu masauki.

Nan da nan kuwa suka dinga zuwa daya bayan daya suna gaisawa da Sultana, ana rungume rungume ,da sumbace sumbace irin na gaisuwar mutanen qasashen turawa.

Sai da suka gama tsaf ta taka zuwa gaban Sultan,ta rungume shi da kyau, ta na kuka tare da yi masa godiya.

Share mata hawaye ya dinga yi, ya na girgiza mata kai, shiru ta yi, ta na murmushi, basu shiga main wajen taron ba, sai da suka je wani daki a hotel din da ake taron, aka gyara mata kwalliyar ta, sannan qawaye suka fara shiga aka sanya amarya da ango a tsakiya, ana tafe  Hamisu breaker na waqe su.

Ranar su 'Yabbuga an yi ciniki, dan duk kudin da iska tai gangancin kawo shi wajen zaman su, to fa b'atan dabo yake, ba a sake ganin shi .

Biki ya yi biki, Hajiya Ikee da qawayen ta, sun samu abinda suke so, an ci, an sha, an raqashe, an watsa kudi,su Asshibi, sai kallon turawa ake ana musu hoto, Mai Buruji da Lamishi kuwa sai fad'i ake wa mutanen unguwa ana tinqahon bikin d'an su ake.

Lawwali kuwa can qasan ran shi kewar Mubarakan shi yake, ana hidimar bikin shi amma bata nan, da gwamna bai mishi abinda ya masa ba da tuni, auren nan, da zuciya daya za a yi shi, ba wata boyayyar manufa, da tuni masoyiyar shi, kuma qanwar shi abar qaunar shi na wajen, in ma ya kyale gwamna bai rama abinda ya masa ba a rayuwa ai bai cika dan halak ba.........

*Wai ni dan Allah ba za a hakura da wannan daukan fansa bane??*

💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻

BY HAERMEEBRAERH

PAGE 43:

An tashi taro lafiya, babu wani wanda ya tafi da qorafin bai samu abun biki ba, ko bai ci ya qoshi ba.

Bangaren su Lamishi kuwa ta so su gaisa da Hajiya Ikee da qawayen ta, ko dan ta qara kankaro wa kan ta aji da mutunci, wajen mutanen unguwar su, amma haka Hajiya Ikee ta dauke kai, ta na yatsina ta ce musu ta na zuwa, ko da ta tafi sallama tai ta yi da qawayen ta da suke komawa gidajen su, ta na gama sallamar su, ta tafi ta ta motar, aka ja ta sai gida.

Haka su Lamishi suka gaji da jira suma aka kwashe su sai gida, Sultana ranar a hotel din da qawayen ta suke ta kwana, duk da Lawwali ya so ya maida ta gida,amma ta nuna masa rashin dacewar hakan, tunda dan ita suka zo.

Ai kuwa kwana suka yi su na hira, suka ci suka sha, suka yi games kala kala, irin na al'adun wasu qasashen.

Basu suka kwanta bacci ba sai bayan sun yi sallar asuba, su na idarwa kuwa suka hau baccin gajiya.

Sha daya na rana suka tashi, suka hau wanka, da shirin tafiya gidan Gwamna, yau za a Daura auren Sultana da Lawwali, masu gyaran jiki da kwalliya sun hallara, nan da nan amarya da qawayen ta suka sha gayu, ankon purple din yadi suka sanya, amarya ta saka nata kalar golden da milk, qamshi sai tashi yake ko ta ina, in ka kalli wannan sai ka ga kamar tafi kowa kyau a wajen, da ka kalli 'yar uwar ta sai ka ga ta doke ta farkon kyau , kowacce na ji da kyau, aji, ilimi, da gayu.

Manyan motocin da suka je daukan su abun kallo ne, cike da nutsuwa ake tuqa su har zuwa gidan Gwamna halliru, tin daga farkon layin unguwar har qarshen shi motoci ne, na alfarma, matan manya ne danqam a cikin gidan, wasu daga wasu garuruwan suka zo, wasu a cikin garin suke.
Chapter 57 · 0% Book details