← Book details A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 93

Sashe 85

A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tausayin Hajiyar ne ya sa ta miqe da kyar, marar ta na murdawa, ta nufi hanyar parlour, za ta hado mata tea, wani irin jiri ne ya ɗebe ta, ta kusan faduwa, daddafe jikin bango ta yi, Hajiya Ikee da sauri ta isa wajen ta,cikin kuka ta ce,

"Dan Allah samu waje ki zauna, ko me ki ke so za a miki,dan Allah kar ki sa wa kan ki damuwa ke ma na rasa ki, ba zan iya daukan rashin ku ba,"

Kuka Hajiya Ikee ke yi sosai, Sultana kasa bata hakuri ta yi, sai da wasu 'yan uwan Hajiyan suka sa baki, sannan ta rage kukan.

Zama suka koma suka yi,tace a hadowa Hajiya Tea, da kyar aka tursasa ta ta sha, jin shi ta yi kamar mad'aci, amma haka ta daure ta sha.

A haka, a haka dai har sai da akai sadakar bakwai,sannan mutane suka tattafi gidajen su, dan yanda suka saba in sun zo a ci a sha a raqashe da kaji babu, duk da ana kawo na sadaka, amma ba kamar da gwamna na da rai ba.

*******************

A kwana na goma sha biyu, Lawwali ya je gidan Gwamna,dan gaishe da Hajiya, yanzu ya na bata girma sosai, saboda tausayi take bashi.

Ya na nan duqe gaban ta, ta na ta bashi labaran yanda tsohon gwamnan yake kyautatawa iyalan shi, da yanda ya ke matuqar son su, su Lamishi suka yi sallama, amsawa Hajiya Ikee ta yi, cikin d'an sakin fuska .

Zama su Lamishi za su yi a qasa, da sauri Hajiya Ikee ta ce,

"Dan Allah ku tashi daga qasa, rayuwar ga duk labari ce watarana, dan Allah mu yahe wa juna, abubuwan da sun ka hwaru a baya,"

"Allah Sarki Hajiya komi ya wuce, ya hankuri?"

"Alhamdu lilLAAHi,"

"Allah shi jiqan gwauna, shi mai rahama, Allah shi gafarta mai"

"Ameen Allah shi bada lada"

Mai Buruji, Mubaraka, duk sai da suma su ka bada gaisuwar su wajen Hajiya,da Sultana.

Sultana ce da ta fito daga ciki, ta je yin alwala, ta ga su Lamishi, da sauri ta je ta durqusa gaban su, suka gaisa, suka mata ta'aziyya, Mubaraka ce ta zauna kusa da ita, ta na sake mata ta'aziyya,

"Ameeen na gode, amma dai nan za a bar ki ko? Sai an yi arba'in"

Kallon Lamishi ta yi, ta na neman izini, da ido,daga baya ta maida duban ta wajen oga Lawwali, ta dire shi akan Sultan,da ya kafe ta da ido ya na jiran jin amsar ta, kowa ya yi Mamakin yanda Lamishi ta yi sanyi, ta koma kamar ba ita ba,

"Ki zauna, ba ya da komi, ai duk ɗaya ne"

A tare Mubaraka da Sultana suka ce

"Na/na gode Ummaa"

Wani qayataccen murmushi ne ya bayyana a fuskar Lawwali, miqewa ya yi, ya ce in sun gama su masa magana, zai maida su gida

Duk wani motsin Mubaraka na kan idon Sultan, duk ya sa ta ta kasa sakewa, qarshe sai da suka hau sama yin Sallah, sannan ta samu ta ji kamar an zare mata wani abu da ya takura walwalar ta.
Sun kai kimanin awa guda,kafin Baraka ta raka su waje.

A bakin motar shi ya tsaya, ya na jiran su, da kan shi ya budewa Lamishi mota, ta shiga, ta na mai jin dadi, da da suke tsananin maitar mota ma ko kusa da ita ya hana su zuwa, amma yanzu gashi shi ke bude musu su zauna.

Sallama suka yi da Mubaraka, ya ce zai debo mata kayan ta, in ya kai su Lamishi, nan ta fara shagwaba, ita Umman ta ne za ta debar mata kayan, ta yi ajiya ba ta so ya gani, yafitar ta yayi, ta kai kunnen ta saitin bakin shi,

"Na hwa san mi ki ke boye min, yo ni ma mata ta ta na da su, ko d'azu a gida sai da na wanke mata su, mi na na acciki to dan na gani, ni ne fa Yah Auwal d'in ki"

Dariya take son ta yi amma dole ta daure, dan ko ba komai gidan rasuwa suke

Shi kuwa fita ya yi da mota ya na dariya,.

Lamishi kuwa cikin ran ta, ta na jin wani irin dad'i na ratsa ta, a baya haushi take ji, ta ga Lawwali na fifita Mubaraka akan su, amma yanzu sai ta gane hakan ba wata matsala bace da zata sa ta dinga jin haushi, hakan na nuna su din su na son junan su, da bawa juna kulawa.

Bayan sun Isah gidan, ya sha mamakin ganin Icce da gawayi buhu uku, a aje a rumfar da Dan Talo ke ta yi da kan shi, juyawa Lawwali ya yi bayan motar ya ce ma su Lamishi,

"Wa ka sai da ic-ce a unguwar  nan?"

"Baban ku ne, ya ce yanzu in shaa Allahu ba zai sake zaman banza ba,da kuddin da ka bamu, ya samu ya siyo komai da shika bid'a, abokan shi  na masa dariya, shi ko ko a jikin shi, sai da ya qare ya siyo motar icce guda an ka juye mai, ya sa gawaiyi, har da barahuni (kananzir)yaka sayarwa"

"Ikon Allah"

Daga haka bai qara magana ba, fuskar shi dauke da murmushi ya qarasa rumfar.

Sallama suka wa juna, Dan Talo ya dinga neman afuwa da gafarar Lawwali, ya ce ya nemi gafarar sauran yaran shi, ya kuma yi alqawarin zai zama uba na gari

"Allah shi bada iko baba, ni ma ka yahe ni, in shaa Allahu, sana'ar ga sai tayi albarka, yanzu mi ka ke buqata a qaro?"

"Babu komi, in ma akwai ina da kud-din siye, yafe min da ka yi ma ya ishe ni, ban san cin iyali na ba, ban san shan su ba, ban san suturar su ba, balle wajen kwanan su, ba su da lahiya, ko su na cikin b'acin rai, da quncin rayuwa duk ban sani ba, a da ji na nikai kamar wanda an ka d'ebewa tunani,amma yanzu hankali na ya dawo jiki na, na san fari na san baqi yanzu, da yardar Allah sai iyali na sun yi farin ciki da ni kamar yadda kowanne iyali ke jin dad'in mai gidan su"

Lawwali ya kasa cewa komai, sai murmushin jin dad'i kawai ya ke zubawa, nan ya zauna su ka yi ta hira da mahaifin shi, daga qarshe shi ma ya yanke shawarar Kano zai dinga zuwa ya na kasuwanci, duk qarshen wata ya na dawowa.

************************

Zaman mubaraka da su sultana ya sa sun rage kewa kadan, dan kuwa, tare suke haduwa, da Sultanan su yi ta karanta qur'ani, Hajiya Ikee ba a iya karatu ba, ita daga qulhuwallahu sai Fateeha su ma a sallah take yin su, da mutum zai saurara zai rantse da Allah Yaren mutan China take ba larabci ba, rayuwar ta kafff ta qare ta ne wajen neman duniya, amma harafin alif da baa na mata wuyar haɗawa, balle ta kai ga karanta qur'anin sukutum.

Mubaraka ta kula da hakan, dan haka ta qudirta a ranta, za ta taimaka wa Hajiya, dan ganin ta samu tagomashin alkhairi da ladan da ake samu, wajen karanta littafin Allah.

A hankali kuwa Hajiyan ta fuskanci me Mubarakan ke so ta yi,da sauri ta ajiye girman kan ta, ta na koya, Mubaraka ta yi amfani da koyar da Hajiya ta na rage mata kewa, da yawan tunani.

Da ta gilma ta gan ta tana kuka, ko tunani, za ta ce,

"Hajiya, in an had'a, ba'un da fataha, da mimun da fataha, me zai baki?"

Sai ta yi shiruuuu ta na nazari, can sai ta washe baki ta ce,

"Bama"

"Yeeehhh Hajiya za ta ci Bama"

"Yannema ni dai a dinga  yi min kad'an kad'an, kar karatun ga shi yi min yawa, in taho banni gane komi"

"Ganewa ki kai inshaa Allahu, kahin Ramadan mai zuwa ke zaki zanka ja wa Aunty Sultana baqi, ita kau ta na fassarawa,tafsirin cikin gida za mu yi"

Dariya sosai suke yi, in Mubaraka na musu irin wannan barkwancin.

Sultan kuwa da ya gan ta zaune da su Hajiya, shi ba ta masa hira kamar ta su Hajiya, sai ya yi ta bata rai,ya na wani abu kamar qaramin yaro, ya na sane sai ya zubar da ruwa, ko tea, ko ya b'ata waje,ya kwala mata kira, Ita kuwa ta gane me yake nufi, ba ta kula shi, sai dai ta je ta gyara wajen, fuskar ta dauke da Murmushi, kallon ta zai ta yi, kamar ya samu TV, da ya ga za ta tafi, zai qara yin wata barnar,dan kawai ta tsaya.

Watarana suna can sama su na hira, Hajiya na basu labarin yanda ta hadu da Daddy, har suka yi aure.

Sultan ya zubar da tea, ya kwalawa Mubaraka kira, tare da sanar da ita ta je da abun gogewa.

Har za ta miqe Hajiya ta ce,

"Zauna, baki zuwa, ni bari na je, na goge masa, in ba ze zo ya ce  Hajiya aramin ita ni ma muyi hira ba,ba ki zuwa yi mai aiki, danneman rainin wayo kai, ya zaci ban gane komi ba, tunda takkwala na ke, na hi kowa qaramar kwanya gidan ga"
(Tunda daqiqiya ce ni na fi kowa karamar ƙwaƙwalwa a gidan nan)

Da kan ta ta shiga dakin na shi, Sultan an sha wanka da wata shadda da akai wa d'inkin half jumpa, kan shi ba hula, sai qamshi yake zubawa, ya na tsaye jikin TV, ya na rage volume Hajiya ta shiga, ba tare da ya juya baya ba, ya fara magana,

"Mubaraka, ki yi hankuri da aikin da ni ke saka ki, ta haka ne kawai zan gan ki, dan na kula yanzu ke hi son su Hajiya akai na, jiya Daddy ya cika kwana arba'in da rasuwa, ina fatan nan da wasu kwanaki mu bayyana wa h......"

Maganar shi ce ta maqale da ya juya suka yi ido hudu da Hajiya, fuskar ta ba wani emotion a jiki, ji ya yi gaban shi ya yanke ya fad'i, dube dube ya fara yi, ya na neman Mubaraka, bai gan ta ba,

"Ha...haaajiya Mum, inaa Mubaraka?"

"Dama kenan ta san ka na son ta?"
Chapter 85 · 0% Book details