Sashe 86
A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yanayin yanda ta yi maganar ya so ya bashi tsoro, cikin zuciyar shi ya fara tsoron kar dai Hajiya har yanzu ba ta dena qin jinin talaka ba? Bai san ya zai da rayuwar shi ba in ta ce ba zai auri mubaraka ba.
Juya baya ta yi, Sultan na nan tsaye ya kasa magana, saboda rashin sanin me ne ne a zuciyar Hajiya Ikee game da zabin shi..........
💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻
BY HAERMEEBRAERH
PAGE 62:
"Dan Allah Hajiya kar ki qi wannan auren, Mubaraka alkhairi ce a gare mu baki d'aya in shaa Allahu, ban ga wata mace da zan iya aura na ji dad'in rayuwa ta ba sama da ita,Kuma na ga yanzu ki na son ta, ko?"
A hankali Hajiya Ikee ta samu waje ta zauna, idanun ta sun sauya kala, daga farare tass zuwa jajaye, saboda hawayen da ke barazanar sauka mata, hancin ta ta ja, sannan ta dora idanun ga a saman fuskar Sultan, da ke a tsugunne a gaban ta, kamar me neman gafara, ya na jiran ya jin kalar hukuncin da za ta yanke.
"Wato Sultan na koyi darrussan rayuwa a qarshen shekarar ga, ba kadan ba, na koyi abubuwa kala kala, ciki ko har da sanin darajar Dan Adam, a baya ba kalar wulaqancin da ban yi wa iyayen yarinyar ga ba, da ita kan ta, amma ka diba ka gani, a yanzu ita ka qoqarin kwantar muna da hankali, saboda halin damuwar da muke ciki,ita ke qoqarin ganin na san wane ne mahalicci na, na shekara d'ai d'ai har shamshin da shidda amma ban iya karanta qur'ani ba na bata rayuwa ta a banza ban san wanene ubangiji na ba, ban taɓa karanta kalma ɗaya ta alqur'ani ba tsabar rashin rabo, boko kuwa ko da baturiyar qasar Amurka sai mun buga, ka diba ka gani, a wata d'aya yarinyar ga ta hwara sawa ina iya karanta wasu kalmomi na larabci, na qara yarda da cewa, kyawun huska, ko wani kyau na halitta, ba shi kad'ai ne kyau ba, kyau shi na cikin kyakkyawan hali da d'abi'a, wanda ya rasa su, komai kyawun huska shi mummuna ne, ina goyon bayan auren ku, dubu bisa dubu ma Sultan, Mubaraka ita ce ta hi dacewa da rayuwar mu baki daya,Allah shi yi muku albarka"
Hannun Hajiya Ikee Sultan ya riqe a nashi gam gam, sannan ya sumbace su, cike da murna, ya dinga godiya,a haka su Sultana suka tadda su, Mubaraka kuwa tun da ta ji Hajiya na yabon ta taso guduwa, amma Sultana ta riqe ta, sai da suka gama, magana sannan Sultanan tai gyaran murya, ta ce,
"Mu shigo an bamu izini? Kar ku ce mun yi maku labe, mun ji shiru ne shi na mun ka taho mu ji ko lahiya?"
"Ku shigo, 'yan sa ido, kun dai taho ku ji mi muka fadi, to kun dai jiya, Hajiya ta amince na auri B love di na"
"Tauuuu mi na na kuma B love?"
"Sultana ba kyau sa ido, ba ruwan ki, ni kadai na san me na ke nufi da hakan,kalla yadda Mubaraka kanta ta baza kunne ta na so ta ji ma'anar B love, ban fad'i to, yarinya rufe kunnuwan,"
Cikin jin kunya ta sa hannayen ta ta rufe fuskar ta, tabbas kuwa ta tsaya ne ta ji me ye ma'anar B love din, kuma ya gano ta.
Juyawa ta yi da sauri za ta fita ta ji ya kira sunan ta, da wata iriyar Muryar da ta sanya ta tsayawa cak ba tare da ta shirya ba, daga Hajiya har Sultana ba wanda ya qara magana, dan su ma za su so jin me Sultan zai fadi da mahimmanci haka, har da sauya murya.
Takawa ya yi zuwa gaban ta, ya tsaya, kallon idon ta yake so ya yi amma ta maida kan ta qasa, kunyar Hajiya take ji, amma ta kula su ba ruwan su,
"Kalle ni Mubaraka,"
Da kyar ta d'aga kai ta kalle shi, idanun su na haduwa da na juna, ta ji kamar an kafe nata, kasa kauda kan ta tayi daga barin kallon shi,
"Mubaraka za ki aure ni? Za ki taimake ni ki tausaya wa Maraya Sultan ki aure shi? Ki sani ba ni da dukiya, ba ni da aikin yi, amma ina tare da dimbin soyayyar ki, wadda na ke jin ta ishe ni qarfin guiwar zama komai da na ke so na zama a rayuwa, da izinin Allah, so Mubaraka za ki aure ni?"
Wasu irin hawayen farin ciki ke mata gudu a kunci sai qaiqayi suke mata, gashi ta kasa daga hannu ta sosa kuncin nata, jikin ta ya mace murus, yau wai ita namiji had'add'e kamar Sultan ke neman aure ta wannan sigar? A gaban mahaifiyar shi, da qanwar shi, ita d'in wace ce? D'iyar tallaka, qanwar tallaka,sannan ita kan ta bata mallaki komai ba, ita ba wani kyau na a zo a taru a sha kallo ba, Sultan ya fita komai, kyawun shi ma abin kallo ne, kyawun shi ma kyakkyawa ne, ga kyawun hali, da d'abi'a, anya bai fi qarfin ta ba, ta sani ba wani namiji da take wa so irin na soyayya bayan shi, amma a yau sai ta ji gaba daya bata cancanci zama matar shi ba.
Cikin murya mai cike da rawa, ta ce,
"Yah Sultan ka dai san kai ba sa'an aure na bane ko? Ka hi ni komi da komi a rayuwa, ba...."
Sultana ce ta katse ta, ta hanyar sanya hannu ta share mata hawayen ta, sannan ta ɗan ja kumatun ta, ta ce,
"Kar na ji kalmar rejection ta fito a bakin ki, zan qi komawa gidan Yayan ki, Hajiya mu basu waje, wataqila kunyar ki taka ji, ke ko kin zauna dirshan ki na kallon su awa ke samu TV"
Dariya sosai Sultan da Mubaraka suke, Mubaraka na dariya hawaye na qara saukar mata, yau rana ce mai cike da farin ciki a wajen ta, ina ma ace Yah Auwal na nan, yaji yanda Namiji kamar Sultan ke bayyana mata ra'ayin shi akan ta.
Bayan fitar su Hajiya Sultan ya sake roqon Mubaraka, akan ta amince da auren shi, dan tura baki ta yi, cikin shagwaba ta ce,
"Ni dai ka dena roqo na haka, dan kuwa ba ni da wani abun baka,mutum guda na zai iya baka amsa, shin zan iya auren ka ko ban iya wa,"
"Ni dai dan Allah kar ki had'a ni da Auwal"
Cike da dariya Mubaraka ta ce,
"Ashe ma ba ka so ka aure ni, wajen shi za ka je wallah, in yace shi na baka niii, to zan aure ka, in yace ba zai..."
"Ya isa haka nan, zan je wajen shi,kuma na tabbata, in da zan je da sadaki na a lokacin zai aura maki ni, "
"Me zai hana ka tai da sadakin gaba ɗaya, domin na mallake ka a matsayin miji na cikin gaggawa"
Yanayin yanda ta yi maganar ya kawar masa da komai, na tunanin ko dai bata yi da shi,zuciya bata da qashi, dan har ya fara tunanin ko Taheer take so, sai ya ji kalamai masu ɗauke da gaskiyar abinda ke zuciyar ta.
Cikin jin kunya ta bar dakin nashi, shi kuma ya bi ta har bakin qofa ya na murmushi, har ta sauka qasa gaba daya bai bar wajen ba, ya na nan tsaye ya na murmishi.
Sultan kuwa bai bata lokaci ba, da daddare ya sha wankan shi, da manyan kaya, ya nufi gidan Lawwali, ya tarar da shi ya na waya da Sultana, sallama ya mata, ya ce zai sake kira ya yi baqo.
Sai da suka gaisa, Lawwali ya sake yi masa ta'aziyya, sannan Sultan ya kalli gidan, ya ga yanda Lawwali ya qayata shi, ya gyara shi, kamar gidan sabuwar amarya.
"Lallai ka na ji da matar ga taka, irin wanga gyara kamar za a kawo maka sabuwar amarya? "
"Ka gyara kalaman ka, dan kuwa Sultana sunan ta kin fi amarya"
Sultan kuwa langwabe kai ya yi, ya yi kalar tausayi, sanan ya ce,
"Allah Sarki,mu gamu mu na son a bamu tamu amaryar amma ba wanda ya damu da halin da muke ciki, har yanzu an kasa gane mun isa aure, a aurar da mu, sai mun aje kunya a gehe mun roqa a muna aure"
Lawwali me zai yi in ba dariya ba, shi ma Sultan d'in dariya ya dinga yi, cikin dariya Lawwali ya ce,
"Yanzu dai ka ce aure ku ke so, kuma maganar neman aure ta kawo ka ko?"
Gyara zama Sultan ya yi ya ce,
"Gaskiyar kenan, ni na rasa iyakar son da Mubaraka ke yi ma, wai na yi na yi ta amsa min buqatar auren ta da na je mata da shi,ta ce sam sai ka amince"
Murmushin jin dadi Lawwali ya yi, sannan ya ce,
"Indai ni ne na amince, na baka goyon baya ka ci gaba da saye zuciyar qauna ta, har sai ta amince ba wani namiji sama da kai a rayuwar ta,"
"Tabdijam, ka dai ce ba wani namiji da zata so da aure sama da ni, amma har duniya ta tashi kaine namijin farko kuma na qarshe da take so, na gode sosai da amincewar ka"
Nan dai suka yi ta hira, Lawwali na bashi labarai akan Mubaraka, abinda take so da wanda bata so, har qaddarar da ta fad'a mata tsakanin ta da No 1,Sultan ya tabbatar masa da cewa, ba namijin da ya dace ya auri Mubaraka sama da shi, ta sanadin Daddyn su haka ta faru, dan haka shi ke da alhakin auren ta, ko da ace ma ba ta sanadin Daddyn su bane, shi dai ya ji ya kuma gani ya na son ta a duk yanda take, ita yake so ba jikin ta ba,shi ma Sultan haka ya dinga fadawa Lawwali abubuwa akan sultana, daga qarshe Lawwali ya kira Mubaraka, ya fada mata amincewar shi, cikin jin kunya ta yi masa godiya.