Sashe 2
A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Miqa masa kwano Lamishi ta yi da abinci, tini ya rufe bakin shi, ya karbi kwanon ya yi waje, ya na fadin,
"Ina zuwa, bari na isuwa cin abinci za ki maimaita abinda ki ka hwada"
"Haka nan aka iya,namijin hotiho"
Lamishi da ta dawo daga ajiye abincin yaran su ne, ta dangwara kwanon nasu abincin a gaban Mai Buruji ,ta zauna, tare da fadin ,
"Ke dai ba ki gajiya da jayo mana wancan dan na gaji jininin (mita) shi zo shi aza mana cin mutunci, se rai ya yi ta ɓaci"
Dariya kawai Mai Buruji ta fara, ta na kai lomar shinkafa bakin ta, sallama aka rangada, tare da fadin,
"Mutanen gidan na nan kuwa?"
"'Yakkwadai(kwad'ayayyiya) , ke duk san muna nan daidai wanga lokaci, shigo mu ci"
"Ba ka qi ta mutum ba ai, abinci abokin kowa na wallah"
Ba Bismillah ba komai,haka matar da ake kira da 'Yabbuga ta danna hannun ta a kwano, ta fara kai lomar shinkafa bakin ta, ta na ci ta na qoqarin basu labari .
"Dan Allah dai ki bar d'umin ga, ki na maisuwa mana na baki,"
"Akwai labari"
"Ai mun san ba a rasa nono a riga"
Fatali ya yi da butar da ke saman hanyar shiga cikin gidan , cikin maye da kirari, da kuranta kan shi ya ke magana, daga qarshe ya zabga wani ihun da ya sanya 'Yabbuga kwarewa da shinkafa,tsabar tsoro, sai tari ta ke son ta maqale ya qi maqaluwa,
"Lawwali yanzu tsakanin ka da Allah hwashe min buta zakai ka tafi ka barni da sayen sabuwa? Ka..."
"Ina abinci naaa...yunwa nake ji...ciki na ba komai kamar tekun da ta qafe haka nake ji na"
"Shi na kici tai ka dauka, lalataccen banza"
Wata zabura ya yi, kamar ba shi ne ya shiga a bige ba, ya zaro wata sharbebiyar wuqa,ya goga a qasa, tare da zuba wani uban ihu, 'Yabbuga ta zabura ta runtuma dakin Lamishi a guje ta na fadin,
"Tsautsayi ya kawo ni gidan ga, Lawwali na gari, da na san ya na gari da ban zo kwadan banza ba, yau bone ya ci ni, Allah ka taimake ni na hita gidan ga lahiya,"
Jikin ta sai rawa ya ke, zufa na karyo mata, a rayuwar ta ko Allahn da ya halicce ta bata tsoro kamar yanda take tsoron Lawwali,tunda ko salloli biyar basu dame ta ta tsaida su ba, yanda take tsaida gulma da munafurci a unguwar, Lawwali ya farke mutum ya bace a neme shi sama ko qasa a rasa ba wani abu bane a wajen shi , ko da an kama shi, ba ya kwana a cell , a ranar ze fito, kuma wanda ya sa aka kama shi, ya jawa kan shi masifa.
Shi ya sa ma, mutane suka hakura da kai shi qara wajen hukuma.
Abincin shi ya dauka, ya fita zuwa dakin shi da ke zauren gidan, ya na fito,wata ajiyar zuciya 'Yabbuga ta sauke, tare da qarasa sude hannun ta da ta ci abinci, leqe ta ke ta window dan ganin shin ya tafi ko yana nan? Ta na ganin fitar shi ta yi wuf ta fito itama, takalman ta a hannu, ta bar gidan, cikin sanda kar ya fita su gamu, Lamishi na mata magana, akan ta tsaya ta fesa masu me ya faru a shiyya da basu nan, ta ce su same ta a gida.
Kwata-kwata bata son dik wani abu da zai hada ta da Lawwali, saboda Lawwali
na da daurin gindi matuqa a wajen manyan mutane sosai,saboda rashin tsoron shi, da cika masu duk wani aiki da suka saka shi.
Sun dauke shi a matsayin wata kadara tasu mai amfani da mahimmanci,da suke kula da ita da dukiya, da qarfin mulki da ikon su, dan kar wani abu ya same shi.
Lawwali shi ne babban d'an Lamishi wadda ita ce uwar gidan Dan Talo, masu bi mashi mata ne guda uku, Rakiya, Ashibi, da Lami, dikkanin su suna dakin mazan su, sai autar Lamishi mai suna Mubaraka.
Mai Buruji na da yara biyu maza, Kamilu da Jamilu.
Dik yaran gidan ba wanda ya yi makarantar islamiyya balle ta boko, in ba Mubaraka ba, ita kadai ce ta ke zuwa islamiyya da kuma boko, da kyar ta samu Lamishi ta amince, tare da sanya bakin Lawwali, dan ya na mutuwar son qanwar shi, ba ya son dik wani abu da zai taba ta.
Duk abinda ta ke so,sai ta bi ta hannun shi ta ke samu, ba dan komai ba sai dan ban-bancin ra'ayi da d'abi'a da ta ke da shi da mutanen gidan.
Shekarar ta sha shida, amma ta matsu ta yi aure itama kamar sauran yayun ta, ta bar ma su Lamishi gidan, su yi ta jahilcin su.
Kusan kowanne gida ana samun irin wannan, yaron da ya fi biyayya, ya fi sanin ya kamata, da ciwon kan shi, ya fi shan wahala, tsangwama wajen iyaye da 'yan uwa, ya fi shan aiki, da kuma rashin samun kulawa, balle a kai ga gode masa.
Haka ce ke faruwa da Mubaraka a cikin gidan su, wajen Lawwali kawai take samun yabo, da soyayya ,har ma da kyauta, lokuta da dama, har mamaki take, anya Lamishi ce mahaifiyar ta? Amma kamannin su kad'ai sun tabbatar da hakan,Mubaraka, irin yaran nan ne, baqaqe masu madaidaicin kyau, ba ta da wani shahararren kyau, amma saboda kyaun hali da d'abi'un ta, mutum ba zai gaji da zama da ita ba.
Sallama ta yi, tare da murmushi mai annuri, ta shiga gidan, ba komai ya sa ta murmushi ba, sai ganin yayan ta a gida.
Har sun gaisa, ya bata tsarabar da ya kawo mata,ta littattafai da biskit, da alawowi, ya na bata, ya rufe dakin na shi da ke soron gidan ya yi gaba, dama ita ya ke jira.
Ba tare da sun amsa sallamar ta ba, Lamishi ta kalli sabuwar ledar da ke hannun ta ta ce,
"Ke mi nana wannan ga hannun ki?"
Cikin doki da murna Mubaraka ta ce,
"Tsaraba ta ce da Yah Auwal ya kawo min"
"Kawo ta nan,Lawwali ka bata yarinyar ga wallah, bashi da aiki sai bannar kudi nai a harikar banza, ai ta siyan takardun da ba su da anhwani"
Da fari ko kadan Mubaraka ranta bai ɓaci ba da Lamishi ta ce ta kai tsarabar, dan dama ko bata ce ba, ba zata ci komai ita daya ba, amma zagar mata takardu da karatun ta, anan ake samun matsala da ita, nan da nan kuwa ta tura baki, alamar ran ta ya baci.
"Kina barin turo shegen goshi awad-diyar jakka, bani nan"
Amshe ledar ta yi, ta wurga mata littafan ta a qasa, ita kuma ta na bi ta na kwashe wa, cikin qunar rai, ko biskit din bata tsaya amsa ba t shige dakin su.
A nan take suka rabe har da qawayen su da suke nunawa kalar azziqin da suke da shi a unguwa, yamma kawai suke jira ta qarasa yi, kafin nan,kowacce daki ta shiga babu sallah babu salati, suka kwanta,suna jiran la'asar ta yi...........
*A GARIN MU*
WRITTEN BY HAERMEEBRAEH
PAGE 3:
Allah ya halicci duniyar nan kusan komai guda biyu ne, misali,da ya yi duniya sai kuma ya yi lahira,mace da namiji, mutum da aljan, mai kyau da mara kyau.
Unguwar TUDUN FAILA itama ta qunshi mutane kashi-kashi, akwai mutanen kirki, akwai na banza, a kuma kwai 'yan ba ruwan mu da kowa.
Mutanen kirkin da ke unguwar TUDUN FAILA sun fi na banza yawa, amma ya na daga d'abi'ar dan Adam, bayyana mummuna, ya boye kyakkyawa, wannan dalili ne ya sanya mutanen kirkin unguwar suka ware kan su daga cikin irin su Dan Talo, da matan shi.
Bahaushe ya ce, wake d'aya ke bata gari.
Lamishi ce ta fito, cikin wata atampa, mai kyau, da hijabi kalar kayan ta, takalmin ta baqi, sai 'yar wayar ta a hannu, ta kalli qofar dakin Mai Buruji ta yi tsaki, sannan ta ce,
"Kedai akwai malalaciyar mata, komai saurin da ake sai kin bata wa mutane lokaci, Allah shi cece ki kar a tashi tahiya Makka ki makara, walle jirgi tahiyasshi zai shi barki, ba ruwa nai, dan ba ya jiran kowa"
Cikin dariya Mai Buruji ta fito sanye da ta ta shigar kamar wadan da za su biki, ko suna.
Kallon ta Lamishi ta yi, ta miqa mata hannu suka tafa, sannan suka sanya dariya kamar wasu yara.
"Mika saki dariya halan?"
"Idon mutuniyar nih-hango, dut ta walqita taga tuwahin (kaya) ga sai hankalin ta ya tashi"
Sake sanya dariya suka yi, suka sa kai za su fita, Kamalu dan Mai Buruji ne ya dawo, ya yi fururu da shi, dika dika ba zai wuce sha uku ba, shegen yawo ne da shi,baya son zaman gida sam, dan Uwan shi Jameelu mai shekara sha biyar tun tuni ya koma ya ci abinci, ya kwanta, har wannan lokacin ya na ciki ya na bacci, amma Kamalu zai iya kaiwa sha daya na dare a waje, watarana shi ke rufe gidan.
"Ja'iri,yunwa taddawo da kai gida, da ka samu inda kacci abinci ma na san sai dare aka ganin ka,"
Duqar da kan shi yayi, ya kauce wa dukan da Lamishi ta kai masa, ya na dariya.
Ciki ya shige su kuma suka fita, tun daga nesa suke hango wasu mata guda biyu zaune qasan wata bishiyar darbejiya mai yalwar ganye, da ni'ima, zazzaune suke saman duwatsun da ke wajen.
Daga nesa 'Yabbuga ke wara ido dan ganin sunan atampar da su Lamishi suka sanya,bata samu nasarar ganin qasan ba, saboda an kalmashe an dinke, su na zama kuwa ta kai hannu jikin Mai Buruji da tafi kusa da ita, cikin dabara ta shafi atampar ta na masu sannu da zuwa.
"Sa'idawa, shahwa da kyau wallah, super ta ba komi ba, sabuwar ta mun ka sanya ba kwance ba, ko ita ma ki na saye ne?"
"Yo in da kudin kuturu alkaki ai sai na qasan kwano ko?" cewar 'Yabbuga da ta qule saboda gano ta da suka yi.