← Book details A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 93

Sashe 12

A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ke ruhe min baki, yanneman me shegen iyayin tsiya, wahala dai ke ta aura ba Lamishi ba, Kuma wanga karatu da ki ke ta faman wahal da kan ki walle nasan ba albarka zai ba, to ki ta yi, Kar ki fasa hita, ki tai ki debo min ruwa na Sha kahin ki fita yawon, ko a makarantar taku an Hana Yi ma Iyaye bauta?"

Hawaye ne ke gudu sosai a fuskar Mubaraka, a fakaice fa Lamishi ta debewa karatun ta albarka ne, miqewa ta Yi daga tsugunnon da ta Yi a gaban su, ta kalle su ta ga hirar su suke kamar ba abinda ya dame su, hirar gaba dayan ta gulmar mutanen unguwa ne.

Jug Mai kyau ta samu, ta dauraye ta debo ruwan sha, ta Kai musu, amshewa Lamishi ta Yi,ba sannu balle Allah ya sawaqe, sai wata mummunar kalma da kullum ta ke hada Mubaraka da ita, wato ,

"GANTALALLA"

Da baqin cikin Lamishi Mubaraka ta bar gidan, a makaranta ta Yi tambaya akan yanda za ta ci gaba da Yi ma mahaifan ta biyayya ba tare da ta gaji ba.

Da misalin qarfe shida da rabi Mubaraka ta dawo gida, kaca-kaca, kamar ba sai da ta gyara ko Ina ba ta fita,hijabin ta ta cire ta ninke,ta dora asaman wani Dan farin bokitin Lamishi da takan dama kunu, sannan ta dau buta ta zaga bayi, ko da ta fito gani ta yi an Yi wurgi da hijabin a qasa, bokitin ba ya nan, murmushi ta Yi, da ta fahimci Lamishi ce ta dauke bokitin ta, ta Kuma Yar Mata da hijabin a qasa, kamar bokitin ta ya fi hijabin mahimmaci.

Dauka tayi ta Kade, ta shiga daki, ta cire Kaya, sannan ta nufi dakin Mai Buruji ta Gaishe su, qoqarin fita take Lamishi ta ce

"To GANTALALLA an dawo Kuma sai a dau tsintsiya, in kin qare shara ki Tai zuwa Dora abincin dare, wancan uban naku Mara zucciya, ya je ya canye abincin da mu ka rage na dare shi kad'ai"

"To Umma "

Kitchen ta fara sharewa, ta dora ruwan tuwo, da ya kusan tafasa ta wanke shinkafar tuwo ta zuba,sannan ta tafi tsakar gida ta fara shara.

Sai da shinkafa ta dahu lubus, ta tuqa, gani ta yi ya Yi ruwa,sai ta debo gari zata zuba Lamishi ta fita, ganin Mubaraka na shirin yin talge a tunanin ta kenan, hakan sai ya sa ta zabga uban ashar, sai da Mubaraka ta saki muciyar da ta dakko dan sake tuqa tuwon a qasa Dan tsoro,garin ya Dan zuba a qasa kadan.

"Tuwon wahalar naki Zaki tuqa muna? To walle bamu cin tuwon wahala miyar bala'i gidan ga, bakki da aiki sai tuqa Muna tuwon gari, ga gumi (shinkafa)Allah ya hore Muna, ga sure da alanyahu,(yakuwa da alayyahu) Amma ki Yi Muna tuwon gari, ke San dai ba son shi muke ba"

Da alamar gajiya da halin Lamishi, cikin yanayi na rashin mataimaki Mubarakah ta ce,

"Ni fa ba tuwon gari bane, shinkafar tuwon ce bata isa ba tuwon ya yi ruwa shine zan daure da gari,"

Dik da hakan Bata tsira ba, sai da Lamishi ta bude tukunyar miya, zata fara masifa, ta ga miya na zabalbala, Mubaraka Bata ce komai ba, komai na cikin miyar na hadin miyar sure ne, ganyayyakin ne Bata samu yankawa ba, saboda aikin ya Mata yawa.

Bata samu kammala girkin Nan ba sai gab Isha'i, ruwan wanka ta dora, sannan ta je ta zauna, ta na hutawa, a wajen gyangyadi ya fara daukan ta.

"Mubaraka, mi kikai a Nan zaune?"

"Ba komai Baba, wanka zan shiga, ruwan nika jira shi tafasa,"

"Tau ya Yi, a bada himma"

Kitchen ya fara leqawa, be bayar da ko sisi ba Amma ya na Neman abinci, Lamishi kuwa ta sa kowa ya dauki na shi, an kai Masa nashi dakin shi.

Ko da ya ga alamar an Yi girki murmushi ya Yi, ya shige dakin shi.

Mubaraka na fitowa daga wanka aka dauke wuta, alwala ta Yi, ta nufi dakin ta, sabo da zaman duhu, harta San inda komai yake a dakin ta, a haka ta shirya, sannan ta tada sallah.

Ta na tsaka da sallah ta ji qarar Gen, ihu su Jameelu suka saka, su na rawar murna, ta na sallame sallar ta itama ta saki murmushi Mai qayatarwa, murmushi ne da ke Nuna tsantsar farin ciki, da shauqin son ganin abin qauna.

Ta na tafe ta na azkar a bakin ta, ganin su Jameelu ta Yi da Leda sun nufi dakin Lamishi suna murna.

Da damar wasu gidajen ana tsoron yayu maza, wasu saboda suna son qannen su, ba su son su ga a abinda zai Bata rayuwar su, wannan dalilin ke sa su tsare gida, har qannen su dinga tsoron su.

Wasu saboda Basu da gaskiya, ba su aikata abin kirki da qannen wasu, shi ya sa suke matsawa na su, tare da Hana su zuwa ko Ina, a Yi ta musu tsawa, sai su Saba da tsoron yayun nasu.

Lawwali da qannen shi duk babu kalmar tsoro a tsakanin su, sai girmamawa, domin kuwa ya ja su a jiki, Jan da iyayen su ma ba su masu irin shi,ya na son qannen shi sama da yanda yake son kan shi, da mutum ya taba qannen shi, gwanda ya rungumi tiransuhoma da damuna,Dan zai iya kawar da ko ma waye akan qannen shi, musamman Mubaraka .

Sai da ta kwankwasa sannan ta jira neman izinin shiga, Dan murmushi ne Mai sautu ya fita daga bakin Lawwali ,izinin shiga ya Bata, ta samu waje kusa da shi ta zauna, cikin murna sosai.

Hannu ya sa ya dafa kan ta, ta na jin hannun shi akan ta ta rintse idanun ta, da suka cika da hawaye, Nan da Nan kuwa ya fuskanci damuwar da ke cikin ran ta, miqewa ya Yi tsaye, da alamar a bige yake ma, dan tsayuwar tashi ba wani sosai ya Yi ta ba.

"Wane Mai qarar kwanan ne ya Bata ran ki? Waye lahira ke son Tai bago yanzun ga, wa ya taba ki? Hwada min ko wane ne, rayuwa tai ta baci"(ran shi ya baci)

Dan tura baki gaba ta Yi, cikin shagwaba ta kama hannun shi, ta ji yanda ya ke rawa,

"Yah Auwal ni fa ba Wanda ya taba ni, na Yi kewar ka ne kawai, Kuma ka min alqawarin daina irin wagga rayuwa, Amma ka kasa cika min, ba ka taba daukar min alqawari ba ka cika ba, Yah Auwal Anya kuwa zaka sauya?"

Sai a wannan lokacin ne ya ji kwamciyar hankali, zaro Mata ledar kayan kwalama dangin su sweets yayi,ajiyewa ta yi a gefe ta na kallon shi, shi kuwa shiru ya yi, ya na tunani, gaba daya tunanin da yake a zuciyar shi ya tattara ne akan cika Mata burin ta.

"Yah Auwalll"

"Na'am sarauniya Baraka ta, Baraka Ina so na daina wadannan abubuwa, musamman yau, min fita operation an kusan yin nasara akan mu,kin ga Nan, harsashi ne ya gogi naman wajen,abubuwan rashin nasara na ta bin mu"

Kukan Mubaraka ne ya katse Masa labarin shi , cikin kulawa ya kalle ta, gani ya Yi, ta na kallon ciwon,da Bata kula da shi ba, sai daga baya.

"Kwantar da hankalin ki, kin manta Yayan ki jarumi ne? Ba fa yau na Saba karbar harsashi ba."

"Yah Auwal ka cika min alqawari na ka bar aikin Nan"

"Zan bari, Amma da sharadi"

"Sharadin me???"........

*Zan so jin wannan sharadi Nima*

A GARIN MU

WRITTEN BY HAERMEEBRAERH

PAGE 13:

Idanun shi ne Suka fara rufewa, cikin mayen bacci, da mayen shaye-shaye ya ce,

"Diyar Gwauna ni ka so Baraka"

Dafe qirji Mubaraka ta Yi, tare da zaro idanun ta farare waje,

"Diyar Gwauna ?"

Kallon shi ta Yi daga sama har qasa, da ace baya harkar shaye-shaye, da mugayen laifuka irin Wanda yake, da ace shi din mutumin kirki ne, Mai ilimi, Mai Neman halal ko da ba yawa, da ace shi din ba Mai kashe mutane bane, ba tare da haqqin su ba, tabbas da ta San in dai kyau zai sa a so mutum Yah Auwal din ta zai zama zabin sultana, amma a yanda yake dinnan inaa, ba ta hango komai da zai hada su ba, sai ma raba su, hanyar ba ta da mabulla.

Tsugunnawa ta Yi, ta cire Masa manyan takalman shi, Wanda suka kusan Sanya ta amai, domin kuwa jini ne a jikin su, idanun ta hasko Mata abinda Bata gani ba suka dinga Yi game da jinin, sai ta ke ganin kamar wani ya kashe ya fadi a qafar tashi.

Kuka take sosai, zuciyar ta na radadin halayyar da Yayan ta ke ciki.

Tunawa ta Yi da hukuncin Wanda ya kashe Rai, kashe shi za ai, Kuma zai dawwama a wuta, wani sabon kukan ne ya kwace Mata, zama ta yi a qasan wajen, ba zata iya daukan wannan baqin cikin ba.

Ta na gama cire Masa takalmin ta wurga su bakin qofa, ta miqe, ta fita waje cikin sauri, ruwa da tsumma ta dakko, ta goge takalman, sannan ta debo ruwan dumi Mai kyau da dankwalin ta wankakke, ta dinga jiqawa ta na goge Masa ciwon shi da ke fidda  jini.

Ta na Yi ta na kuka, kukan ta ne ya tada shi, idanun shi kamar ba za su bude ba, saboda baccin da ya ke ji, amma ganin hawaye idanun ta sai ya tada hankalin shi, da hanzari ya miqe,

"Barakana mii na na?"

Fadawa ta yi jikin shi ta na kuka, sake rikicewa ya yi, ba ya son kukan ta kuma ta sani, amma ta ke yi.

"Amma dai ke san bani son kukan ki ko?"

Daga kai ta yi,sannan ta fara qoqarin share hawayen ta, taya ta sharewa ya yi, sannan ya kalle ta da alamar ya na son sanin meye ya sanya ta kuka, shiru ta yi, cikin Muryar lallashi ya ce,

"Haba likita na, ko dan kin  ga wanga dan ciwon ne kk kuka? Ke da kk Saba ganin ciwon da ya hi wanga a jiki na? Me ne na  kuka, ashe da nake  hwadin zaki karatu ki kai matakin likita dan ki na kula da ni ba zaki iya ba"

"Yah Auwal da zafi ?"
Chapter 12 · 0% Book details