← Book details A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 93

Sashe 73

A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani baqar fata Isah ya gani, da uniform din 'yan sandar qasar, cikin yaqe Isah ya yafice shi, ya na washe baki,

"Yauwaa ga na gida nan, bawan Allah, dan Allah zo kai mana tafinta, ka fada musu goro kawai na kawo, yasin ban san koken din waye ba, ni ma yanda suka gan ta haka na gan ta, dan Allah fassara musu, ni na yarda su karbi goron su zubar, ai dama haka ake yi ko, amma kar su hukunta ni da laifin da ban aikata ba"

Sai da Isah ya gama jawabi, ya kalli baqar fatar nan, ya kalli larabawan nan, ya na jiran ya ji baqar fatar na zuba Hausa, sai ya ga baqar fatan na kallon shi ya ce masa,

"Ana la afham ma taqool" (ban fahimci me ka ke fada ba)

"Bawan Allah me ka ce? Dan girman Allah in ka iya hausa ka yi min mu fahimci juna,yasin ba kaya na bane,"

Tafiyar shi baqar fatar ya yi, Isah na ta kiran shi ya na fadin,

"Malam musulmi fa dan uwan musulmi ne, ka zo ka fassara musu, ba kaya na bane, goro ne kawai nawa"

Qarshe dai dole suka sa Isah yin shiru.

Isah ba baki sai hawaye, dan kuwa ya riga ya san hukuncin masu shigar da ƙwaya musamman manyan miyagun kwaya irin wannan shi ne kisa.

**************************

Hansatu kuwa bayan sun koma gida,hankalin ta kwance ta yi wanka, ta yi wa Ahmad da Bilkisu, Ameenatu ta yi, suka yi alwala, suka shige ciki, sai da suka yi magariba, sannan suka ci abincin da suka je da shi daga gidan Hajiya.

Suka yi hirar su har isha'i, ta riga ta san ba zai kira ta ba kamar wancan karon,amma bata san me ya sa ba, ta nace ta saka rai, ta ke jiran kiran shi,kallon wayar ta tayi, ta sauke ajiyar zuciya, daga qarshe dai ta tashi ta kai Ahmad dakin su, sannan ta koma ta tashi su Bilkisu.

Rufe ko ina ta yi, ta koma cikin yaran ta ta kwanta, ta yi nisa a bacin ta, ta yi mummunan mafarkin da ya sanya ta tashi a firgice kuma a tsorace............

*Kun dai san mafarkin wasu bayin Allahn na zama gaskiya ko😂🤭🙏🏼*
💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻

BY HAERMEEBRAERH

PAGE 54:

Addu'a Hansatu ta yi ta ce,

"A'uzubi kalimatillahi taamat, min galbihi, wa iqabihi, wa sharri ibadihi, wamin hamazatisshayadin,wa'an yahdhurun"

Sai ta juya daga ɓangaren dama da take, ta koma hagu, ta sake cewa,

"A'uzu billahi minas-shaidhanir-rajeem,"

Ta tofa dama da hagu, ta rintse idon ta, bacci fa sam ya gagari idanun Hansatu, dan haka tashi ta yi, ta yi alwala, ta hau yin nafila ba qaqqautawa, ta na neman tsarin Allah akan abinda ta gani cikin mafarkin ta.

Sai da ta ji bacci ya mata yawa a ido, sannan ta yi sallama, ta sanya alarm ta qure volume din wayar, dan kar ta makara sallar asuba.

**************************

Cikin nasara da taimakon Allah, Lawwali ya fara rage mutanen da suka yi garkuwa da su, su na maida su wajen ahalin su, da kudin fansar da suka karba, ba qaramin tanadi Lawwali yayi ba, dan gabatar da hakan.

Mubaraka ta zama mai ban hakuri a duk inda suka je, kusan saboda ita ake kyale su Lawwali, dan kuwa Mubaraka Allah ya hore mata baiwar iya kalamai, masu sanya nutsuwa, Allah ya mata suffar mutanen kirki, ta yanda duk wanda ya kalle ta zai ji ta shiga ran shi, sai dai in mutum ya kai qololuwa a hassada.

A cikin sati biyu, kudi sun fara gazawa, sai da Sultan ya bada gudun mawar shi, Lawwali da ya qi karba, a cewar shi, dole a koma wajen Gwamna Halliru ya biya, ai shi suke bawa kudin ya sammu su.

Sultana kuwa ta ce,

"Daddyn da bai san wa ke kan shi ba, ai ba yanda za ai shi ba da kuddi, a dai yi anhwani da nawa da na Sultan"

Barirah da masu yin girki a wajen, sun kafe su dai za su zauna anan, tunda dama can su an qi sakin su ne saboda ba wanda ya biya kudi a dangin su, ba kuma wanda ya damu da neman su.

Lawwali ya ce sam ba za a yi haka ba, su zauna a daji, a na cikin haka wasu daga cikin matasan wajen maza suka amince za su aure su, Lawwali ya yi farin ciki da hakan sosai.

Dan haka sun yanke shawara za su shiga gari, su nemi wani babban malamin ya daura musu aure.

Sultan kuwa ya musu alqawarin wajen zama a cikin gari.

Ranar an yi wata yar kwarya kwaryan walima a wajen, saboda murnar yanda komai ke tafiya musu cikin sauqi.

Yamma ta yi liss, ana zazzaune a harabar wajen da suka saba zama, Lawwali na tunanin yanda za su yi da makaman nan nasu, shin ma jami'an tsaro za su miqa, wanda tun asali su Gwamna Halliru ke aikowa su kawo musu, ko kuma siyarwa za su yi, ko kuma lahanta su za su yi kar kowa ya amfana da su?

Shawara dai suke ta yi, ba su samu matsaya ba, Mubaraka kuwa tunanin da ke cikin zuciyar ta daban, ta na zauna gefen su, shiruuu ta na tunani, Lawwali ne ya bar cikin yaran nashi ya zauna a gefen ta.

Murmushin yaqe ta masa, shi kuma ya kalle ta da kulawa,

"Barakana me ne ne, ban ganin fara'a ga huskar ki? Ba haka ki ke so ba, na ajiye komai na zama mutunen kirki? Shin ba burin ki ba kenan?"

"Alhamdu lilLAAH, babban buri na ya cika, amma ina da wani burin bayan wanga, kai kuma b'acin rai ne a gare ka, ni kuma ba na so na aikata duk wani abu da zai b'ata ran ka,"

"Barakana me ne ne burin ki? hwada min ko menene, zan cika maki shi, indai bai hi qarhi na ba"

Kauda kan ta tayi, ta share kwallar idon ta, nan da nan kuwa hankalin Lawwali ya tashi.

"Barakana me ne ne, me kike so?"

"Ummana"

Sai ta fashe da kuka, sakin qaramar bindigar da ke hannun shi ya yi a qasa, ya kama ta a gefen hannun shi, ya na lallashin ta, kwata kwata bai da plans din komawa gida wajen lalatatun iyayen su, ya san dama ita kadai zata kawo masa cikas, ta sanya su a rai over,shi kuwa ba sa gaban shi, kamar yanda ya tabbata ba su gaban iyayen nasu.

"Ki dena kuka, zan maishe ki duk inda ki ke so, amma ba yanzu ba"

"Yah Auwal to dan Allah ka kai ni na gan su,tunda na zo na ke tunanin su, yau ji nake kamar ba zan iya ci gaba da numfashi ba in ban gan su ba"

Cikin bacin rai ya kalle ta ya ce,

"Shin ban hana maki maganar mutuwa ba? Mi sunka tsinana maki a rayuwa banda lalacewa da tagayyara? Sun san inda ki ke? Sun damu da ke ne? Ko kuwa ni me ne ne bana maki da ba zaki tattare soyayyar da ki ke musu ki min ita ba?"

Ya na gama fadin haka ya bar wajen rai a bace, mubaraka kuwa kuka ta sanya ta na kiran shi, bai koma ba.

Sultana da Taheer da Sultan ne suka hau rarrashin ta, cikin kuka ta ce,

"Aunty Sultana ki roqar min shi dan Allah,I want to see my parents ,I love them so much, duk da na san ba sa son mu, lokuta da dama ina mamakin me ya sa to suka haife mu in ba sa son mu? Amma ba zan iya dena son su ba, iyaye na ne, komai lalacewar iyaye dole su na da mahimmanci a wajen d'an su, dan Allah ki fahimtar da Yah Auwal, ba wai ba na son shi bane, ina son shi sama da yanda nake son komai da kowa a rayuwa ta, ban da abu mafi mahimmanci sama da shi, amma ina so na ga iyayen mu, na jima kwarai rabo na da su"

Kuka take ta yi, gwanin ban tausayi, su na ta lallashin ta, Lawwali ne ya kutsa tsakiyar su ya rungume ta, ya ce,

"Ni ma ina son ki sama da komai da kowa a rayuwa ta Barakana,ki shirya gobe zan kai ki ki gan su,kalar tarbar da za su miki ita zata sa na barki wajen su, ko na dauke ki gaba d'ai"

Murna ta fara yi sosai, Sultana na taya ta dariya.

Lawwali ne ya kalli Sultana da Sultan ya ce,

"Ku ko jibi in mun dawo, ku na iya zuwa ku ga su Hajiya, amma sai kun min alqawarin ku na dawowa"

Wani tsalle Sultana ta daka ta d'afe su daga shi har mubarakan, sai da suka fad'i cikin yashin wajen,

"Mun maka alqawari mu na dawowa,"

Dariya mutanen wajen sukai ta yi, lokacin sallah ne ya yi, suka tashi dan gabatar da Sallah .

Kowa ka gani fuskar shi dauke da nishadi, banda No 4 dan ya kula da irin kallon da Sultan ke bin Mubaraka da shi,shi kuwa ba ya so.

Bayan sallar Isha'i ne kowa na d'akin shi,  sultana na kwance ta fara bacci a jikin Lawwali, ya kwantar da ita a hankali, ya sauka cikin sand'a ya bude wata locker, laptops guda biyu ya dakko, sai wasu qananan qundin ajiya, da disk din CD guda uku, sai Camera da waya d'aya, sanya su ya yi a gaba, ya na kallo, ya na hawaye.

Sultana da ta farka tun sanda ya sauka, ta Qura masa idanu, cikin ranta ta na ayyana ba zata bari ya aikata abinda yake da niyya ba, ba zata bari ba sam.

Washe gari da safe, Mubaraka tun da ta yi asuba ta kasa komawa bacci, sai murna take, wajen Taheer ta je, ta na ta masa hira, a can ta tarar da Sultan, su na shan dumi, a wutar da suka kunna.

Cikin hasken wutar Sultan ke kallon yanda kwayar idon ta ke fitar da wani irin haske, a zuciyar shi ya ke ayyana dama kar gari ya qarasa waje wa, ya tsaya a haka, dan ya dawwama ya na kallon cikin idon ta.

Taheer na kula da haka kuwa ya hade fuska ya ce ma Mubaraka.
Chapter 73 · 0% Book details