← Book details A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 93

Sashe 40

A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Tauuu su na zasu nishadantar da mu yau,...kaii Yakubu, taho kai na alqalin wasa, kai zaka bada damar farawa, sharadi daya ne, banda halbi, amma komi ana iyawa, a yi dambe har sai d'aya ya buga qasa so uku, sannan za a qare"

Habaa mana waje fa ya dau harami, sai ihu da murna ake, su kan su wanda za su yi damben ba alamar bacin rai a tattare da su, nan da nan kuwa suka shirya, No 2 da No 3 suka shiga tsakiyar fili, Lawwali na zaune ya na taune cikin bakin shi, idan plan din shi ya tafi daidai, daga yau No 1 ze fara cin qaniyar shi a hannun shi.

Mai kula da wasa tini ya harba bindiga bayan ya sanar da wasan ba wani doka, ana iya amfani da komai dan kare kai, amma banda bindiga.

Kokawa kuwa da naushi, tare da harbi da qafa kamar 'ya'yan jakkai tuni ya kaure a tsakanin su,sun jima suna fafatawa kafin No 3 ya buga qasa ya na haki da fidda numfashi da kyau,

Ihu da murna tare da tafi ne ya kaure a wajen, No 2 ne ya je gaban Lawwali ya duqa ,shi kuma ya daki kafadar shi cikin jinjina, da karrama wa, ihu wajen ya sake dauka, a fuskar No 3 babu alamar jin haushi ko hassada dan an samu nasara akan shi, tabbas har cikin ran su wasa suka dauki abun.

No 4 da No 5 ne suka shiga fili, aka fad'a masu sharadin wasa, tare da harba bindiga, nan da nan suma suka kaure, ana yin nasu ne, wani  matashin da Lawwali ya radawa abinda yake so ya yi, ya fara bi d'aya bayan d'aya ya na fada wa mutane magana a kunnuwan su.

Cikin rabin awa No 4 da No 5 sun jigata, ba wanda ya samu nasara akan dan uwan shi,amma fa kowanne a cikin su ya daku, banda jini ba abinda ke fita a jikin su su dikan.

Cikin hargowa wajen ya dauki sunan, Oga da No 1, cike da mummunan tashin hankali No 1 ya fara kada kai, ya na ja da baya, kamar wani tsumma haka wani gabjeje a wajen ya wurga shi tsakiyar fili, No 1 ji ya yi kamar zai fitsari a wando tsabar tsoro, kowa ya san Lawwali a wajen, ba shi da na biyu a qarfi, ba shi da Mahadi a qarfi a wajen, to akan me za su hada su? Indai ba so suke a kashe shi ba.

Wani irin fushi ne ya bayyana a saman fuskar Lawwali na irin quncin da ke cikin ran shi, cikin qanqanin lokaci ya kawar da fushin ya fara nuna kawai a bar wasan, kar ya cutar da No 1, dariyar yaqe No 1 ya fara, tare da fadin,

"Oga ya ce a bar wasa haka nan, sai wani lokaci"

A gaggauce Lawwali ya kalli matashin da ya yi wa rad'a, ai kuwa matashin ya yi tsagal ya ce,

"Bamu jiya ba mu dai, mu na so mu ga hwadan manya, zai fi dadin kallo,"

"Muna so, mu ma mu na so, mu na son ganin fadan manya!!!!"

Shi ne abinda mutanen wajen ke ta ihu su na maimaita wa, har suka jawo hankalin mutanen da ke rufe a wajen, ta window da duk wata kafa da za su samu damar kallon me ke faruwa suke leqe, ai kuwa cikin daga hannu d'aya wajen ya yi tsit.

Lawwali ne ya isa gaban No 1 ya ce,

"Kar ka damu aboki na, kawai ka dage, wataqila ka samu nasara akai na, ka ga ba ni da wani qarhi Mubaraka ita ta qarhi na ka sani, gashi ban gane ta ba, za ka iya nasara akai na cikin sauqi"

Wata iriyar zufar saman hanci da saman lebe No 1 ke yi, gashi ya na jin wani ruwa na gangarar masa ta qafafun shi, be gama tantance shin fitsari yake a tsaye ba ko kuma zufa ce, ya ji ana karanta sharadin damben,kafin ya ja baya an harba bindiga, zare ido ya yi, ya na kallon Lawwali, wanda fuskar shi ta sauya, daga fara'a zuwa tsantsar bacin rai, hankalin shi ne ya sake tashi.

Kwasa ya yi a guje zai gudu, Lawwali ya cafke shi, wani irin naushi ya kai ma No 1 sai da ya juya, tare da kifewa a qasa, qoqarin buga hannun shi yake a tashi wasan dan ya san ba zai debi komai a jikin Lawwali ba, Lawwali ya bi hannayen ya taushe, ya hana shi buga su.

Dambe ya yi dambe, No 1 ya daku iya duka, duk wani haushin shi da Lawwali ke ji, sai da kaso mai tsoka ya ragu, sai da ya zamana hatta da tsayuwa No 1 ya kasa, baya iya d'aga yatsan shi ko d'aya, ballantana ya buga qasa, idanun shi sun kada sun yi jawur kamar ya yi taruwar jini a cikin su.

Lawwali da kan shi ya d'aga hannayen shi biyu, ya miqe daga saman No 1, ya tabbata dukan da ya masa sai ya sanya shi jinya ta aqalla sati daya,ya ga ta fita yawon cin amana.

Umarni ya bawa No 4 da ya yi jinyar No 1, cikin azama, No 4 da shi ma yake a jikkace, ya fara qoqarin daga No 1, wata qara ya saki mai qarfin gaske, da sauri no 4 ya sake shi, ko da ya duba sai ya ga ashe No 1 ya samu karaya ne, har hannun ya kumbure, da damar matasan wajen sun ji dad'in dukan da aka yi wa No 1 dama ya addabe su, ya ishe su, tunda Lawwali ya koma kwana da zama a cikin gari No 1 ke musu mulkin kama karya, yanzu gashi an yi musu maganin shi.

Lawwali bai kwana a wajen ba, gida ya tafi, ko da ya isa wanka ya fara yi, sannan ya ci abinci ya zauna a kujera, ya na kallon hotunan Mubaraka, da video da ya dauke ta.

Ya na kalla ya na murmushi, tare da jin dad'in sanin inda take, da kuma halin da take ciki,kulawa ta musamman No 4 yake basu,da taimakon Lawwalin.

Duba time ya yi, ya ga sha d'aya saura, bai wani dogon tunani ba kawai ya danna number'n ta, ta yi ringing sau biyu kamar jira take ya kira, ta dauka,

"Hello"

"Assalamualaikum"

Maida ido sama ya yi, kafin ya amsa sallamar da,

"Wa'alaikumussalam, ran ki shi dade baki kwana ba?"

"Ban yi kwana ba, kai mi ka kai da ba ka yi kwana ba har yanzu? Gobe akwai aiki fa, in muka tashi har wata unguwa za mu tai, last 3days an shiga an yi musu barna, ba kadan ba, mutan garin har wasun su sun yi hijira, qalilan ne ke zaune a garin, saboda basu da wajen zuwa"

Sarai ya san ko ina ne, duk da ba su suka yi aikin ba, amma dai abokan aiki, ai ba sa buya.

"Allah shi kai mu,"

"Ameen, me ya sa ka kire ni yanzu? Akwai wani abu ne?"

Shiru ya ɗan yi na wasu seconds kafin ya ce,

"Babu komi, kawai dai na yi kewar ki ne"

Kwanciyar ta ta gyara, tare da sake manna wayar a kunnen ta, ta na jin yanda Muryar shi ta cikakkun mazaje ke dukan dodon kunnen ta,

"Mun fa hadu d'azu"

"Ehh sanin haka ne ma ya sa na ji duk na yi kewar murmushin ki mai tsadar nan, yau baki yi min shi ba sai sau biyu kacal, gaskiya ban qoshi ba, a qara min,"

Wata iriyar siririyar dariya ta dinga yi, har zuciyar shi bai jin komai game da dariyar ta a yau d'in ,soyayyar da ya fara mata kafin ya san me mahaifin ta ya masa, yanzu ta fara sauya salo, ta koma soyayyar daukan fansa.

"Kaiiii ran ki shi dad'e gaskiya sai da sahe, wagga dariya zata hana min kwana"

"Me ya sa za ta hana ma kwana?"

"Saboda in na kwanta zan dinga tunanin ta, kuma zan ji ina son saurarar wata makamanciyar ta daga gare ki, gashi na sani har abada ba aure a tsakanin mu"

Da sauri ta gimtse fuska, tare da mamakin dalilin da zai sa ya ce ba aure a tsakanin su

"Mi ka ka nuhi? An haramta aure a tsakani na da kai ne ko mi?"

"Ba a haramta ba a musulunci, amma iyayen ki sun haramta shi, sanin kan ki na ba mai barin ki auren driver ko? Ban taba baqin cikin rashin ilimin boko ba da na arabiyya sai yanzu, da ina da ilimi da iyayen ki sun bani ke,......ina son ki sultana"

Tsigar jikin ta ce ta tsaya ta mimmiqe, ji ta yi bugun zuciyar ta na bugawa da sauri da sauri.

"Da gaske ka na so na?"

"Kwarai da gaske, ina son ki Sultana"

Rintse idon ta tayi, tare da cizon leben ta na qasa,cikin lallausan murmushi ta ce,

"Dan Allah maimaita in ji"

"Inda son ki sultana"

"Ka same ni kuwa, ba abinda zai hana ka aure na,"

"Akwai shi,"

"Me ne ne shi?"

"Iyayen ki, iyayen ki musamman Hajiya bata bari ki auri jahili, kuma driver,"

"Auwal ka dena kiran kan ka da wannan mummunan suna, in baka fad'a cewar baka je makaranta ba, babu wanda zai ce baka je ba, and na ji labarin har saukar qur'ani  ka yi, kuma ka fara Makarantar boko itama, to ka ga kenan kai ba jahili bane,"

"Hummm ba zaki gane ba, bari na bar ki ki yi kwana, amma fa ki sani iyayen ki ba za su bar ki aure na ba, ni dai abu guda nis-sani, ke kadai ni ke so, ke kadai nit-taba burin mallaka a matsayin matar da zan aura, bayan ke ban taba son kowa ba, .....Ina son ki Sultana"

Idanun ta a rufe hawaye na kwaranya a idon ta, ya gama zuba kalaman shi masu zafi da kuma dad'i a gare ta, ya kashe wayar shi  ya barta cikin yanayin da ta kasa fassarawa.
Chapter 40 · 0% Book details