← Book details A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 93

Sashe 61

A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin dare ya tashi zai zaga, ya gan ta a qasa,  bai tashe ta ba sai da ya zaga can wajen yaran shi, ya ga kowa na lafiya, masu gadi na aikin su, masu bacci na baccin su, sannan ya koma daki, a inda ya barta nan ya same ta, tashin ta ya yi, cikin magagin bacci  ya taimaka mata ta kwanta a gado, suka ci gaba da baccin su.

Da asuba Sultana bata tashi ta ga Lawwali ba, sannan ta yi mamakin ganin ta a gado, dan dai ba zata iya tuna sanda ta hau da kan ta ba.

Lawwali bai shiga dakin ba har takwas na safiya ya gota, sultana ta yi wanka, ta gyara gadon da suka kwanta, ta dauke ledar da suka ci nama ta leqa waje ta wurgar, ta na hango yanda mutanen wajen ke ta mu'amalar su, kamar ba abinda ya dame su, ba alamar tsoron wani abu, ko fargaba a tattare da su, daga nan inda take, ta ke hango yanda suke bin layi su Barirah su na zuba musu abinci, wasu kuma na zaune a dandaryar qasa, sun kama kai, da alama a wajen suka kwana, sun shawu sun yi tatil, sun kuma tashi da ciwon kai.

Daga nesan ta hango Lawwali da wasu zaratan mazaje a wani fili, ya na koyar da su fad'a, kura ma jikin shi da babu riga ido ta yi, daga baya ta sauke ajiyar zuciya, ta juya za ta  koma ciki, d'an dakatawa tayi, a daidai lokacin da ta kula ba ita kadai bace ke kallon surar jikin Lawwalin, wasu 'yan mata ne zaune riqe da plates da cups na abinci da suka karba,sun Qura wa jikin mijin nata ido, kamar su jawo shi gare su .

Sultana tunda take bata taɓa jin wani abu mai zafi da ciwo a qirjin ta mai kama da wannan ba, da sauri ta fada dakin ta, ta dauki mayafin rigar ta, ta zira takalmin ta, ta tafi inda Lawwalin yake,tafiya take  cikin sauri, ta na kartar qasa da takalmin ta, saboda yashin da ke wajen, bata saba da tafiya cikin yashi haka ba, har qoqarin faduwa take amma haka ta isa gaban Lawwali, duk idon mutanen da ke wajen ya koma kan su.

Cikin tura baki ta ce mishi.

"Ina ta neman ka tun dazu ban gan ka ba, ashe ka na nan ka na bude musu qirjin ka su nata kalla ko?"

Dan had'e girar shi ya yi, cikin rashin fahimta, su wa ya budewa qirjin shi? Juyawa ya yi, ya ga yanda wasu matan ke kallon shi, to indai wanan ne ai ba yau aka fara ba, shi be ma dauki wannan wani abu ba, kallon yanda take ta tura baki, ta na babbata fuska yake, a hankali murmushi ya fara maye gurbin hade fuskar da ya yi.

Hannayen shi biyu ya sanya ya daga ta sama, ita kuma wata iriyar kunya ce ta kama ta, sai da ta yi da ta sanin zuwa wajen shi, da ta sani ma aikawa ta yi aka kira mata shi, yanzu wannan abun kunyar da ya ke qoqarin ja mata fa?

Dariya wajen ya dauka, dan ganin yanda take ta dukan qirjin shi, ta na wutsil wutsil da qafa, Ita dai ya sauke ta qasa ya saka rigar shi, shi ne burin ta,

"Ran ki shi dade, nan wajen da ki ka gan  su, duka qanne na ne, ba wadda nika so, ko ta ke so na, su na d'ai so na a matsayi na na shugaban su, kuma yaya a wajen su, ki kwantar da hankalin ki, jikin ga naki na ke dai,"

A hankali suke magana, wanda ba lallai ne na gefen su ma ya ji me suke fad'a ba, iya burgewa kawai sun gama burge mutanen wajen.

Kwantar da kan ta tayi a kafadar shi, ya sassauta riqon da ya mata, su na dariya, baki ta dan tura, ta daga kai ta kalle shi ta ce,

"Ni dai ba na so ka na zama ba riga,ko vest ne ka na sawa pls"

"Ok"

Ajiye ta ya yi, ya dau rigar shi, ya rataya a wuya, ya ja ta, zasu koma ciki, matasan da ya ke horar wa sun zaci tafiya za su yi, suka ji ya ce,

"A ci gaba sai 10am, a tashi"

Ba bata lokaci kuwa suka ci gaba, shi kuma ya shige dakin su da matar shi, mai kishi.

Matan wajen wasu sun ji haushin yanda ta dauke musu shi, wasu kuwa ta burge su, yanayin yanda take shagwaba da jan ra'ayin ogan nasu ya basu sha'awa, basu tab'a ganin shi a irin wannan yanayin ba.

Su na shiga ya jingina da bakin qofar ya wurgar da rigar shi, ya tokare qofar wajen da hannun shi daya, dayan kuma ya sa shi a qugun shi ya na kallon ta.

"To Sultyn Lawwali, ga Lawwali gaban  ki, ki kalla har sai ke ce ya isa haka nan"

Rufe fuskar ta tayi, ta ce,

"Ni fa ba haka na ke so ba"

Takawa yayi gaban ta, ya zauna daf da ita, ya na kallon fuskar ta da ta rufe, ya zare hannun ta ya dora a qirjin shi, ya ce,

"Haka ki ke so to?"

Da sauri ta janye ta miqe tsaye, cikin shagwaba ta sa kukan da ba ko hawaye ta ce,

"Ni fa yunwa nake jiii"

Da sauri ya nutsu, sai a sannan ya tuna ba fa a kawo musu abinci ba, su Bareerah ya sa su dafa abincin da zata iya ci, kuma har yanzu shiru.

Ran shi b'ace ya sanya rigar shi ya tafi wajen su, su na tsaka da gyara cups din da suka dora musu a farantin ya isa.

"Mi da ba ku kawo abincin ba tun dazu?"

Cikin ladabi da kuma ban hakuri, suka masa bayani, ba ta iya irin abincin da ya ce a yi ba, sai da suka nemo wadda zata koya mata, sakin fuskar shi ya yi, ya musu godiya, ya karba da kan shi, zai kai, a tsorace Bareerah ta riqe farantin, ta na bashi hakuri ko da ta yi  wani laifin bata sani ba,

"Yaseerah da Barirah tsakani na da ku sai godiya, na dai hi so na kai mata da kai na ne, amma ba ku yi min lehin komi ba, na gode, ku tai ku ci abincin ku"

Godiya suka yi, ya tafi, hira suke a tsakanin su, Barirah ta ce,

"Walle na hankura, da gani nike kamar Oga na so na, tunda ba shi yi min hwada, kuma komi nicce ya na yi, ko ya bari, ban dai iya shiga tsakanin shi da matar shi, yanda ya ka son ta haka, kallo ma ba zan ishe shi ba"

"Ai na fada maki tun hwarko, da ya na son ki da ko so guda ne, da ya maki maganar, kin dai ga yadda kowa ke da budurwa wajen ga, a manyan nan, sai wanda suke da mata ne kadai basu da budurwa, ai da ya na da ra'ayi da ya yi magana"

"Kaiii mu je mu ci abinci yunwa ni ka ji wallah"

A can dakin su Lawwali kuwa sun ci sun qoshi, sai suka tsaya hira abun su, ranar dai ba wanda ya sake ganin Oga sai azahar.

Ya na ganin za ta yi sallah ya bar dakin, takaici duk ya dami Sultana, wato ba ma ya so ta masa maganar sallah ko? Ba komai za su hadu ne, shi ma abinda ta kula ya na kwadayi tsakanin safiya da azahar dinnan ba zai samu ba.

***************************

Da yamma motar gidan su Hansatu ta tsaya a qofar gidan su Isah, driver ne ya yi ta doka sallama, kamar an mintsini 'Yabbuga ko an kira ta haka ta bar majalisar su data cika da su Lamishi, ana hirar bikin Lawwali, da takura wa Lamishi ta kai su gidan Lawwalin su ga gida, yau ma Mai Buruji ce ta yanka qarya tace sun tafi qasar waje, fadawa gidan Hansatu 'Yabbuga ta yi kamar an aike ta, ta na ta kwala wa Hansatu kira,

"Ke hito, motar gidan ku ta taho, ana ta bidar ki,kin qule a qurya,"

Hansatu ce ta miqe daga kwancen da take, cikin duhu, share hawayen ta tayi sosai, yanda ba za a gane ba, ta daura dankwalin ta, ta gyara doguwar rigar ta, da Hajiyan ta ta dinka mata, ta fita.

"Wane na ka bid'a ta?" (Wa ke nema na)

"Nace maki motar gidan ku ce ta taho, ana ta miki sallama ba ki jiya ba"

"mu je, gani nan zuwa"

Hijabin ta ta sanya, ta bi bayan 'Yabbuga da ta qi tafiya, sai ta ga kwal uwar daka.

Bayan sun gaisa da driver ne ya ce Hajiya na gaishe ta, ta kuma bada saqo a kawo mata, ga takarda, ga kuddi, ya zaro ya miqa mata.

Fita ya yi ya dinga shiga da kayan da ya zo da su, sai daya gama tass, ya ce

"Ta ce ki na ganin bayanin komi cikin takardar, abinda baki gane ba ki mata waya"

"Tauu ya yi Malam Jafaru, ka gaishe ta, na gode"

Sallama ya mata ya tafi, 'Yabbuga kuwa majalisar da bata koma ba kenan,  Hansatu kuwa kayan da bata bude ba kenan, dan bata san mene da mene ba, kar ta bude gaban ta ya zamana bai kamata ta gani ba.

Har sai da suka ji Machine din Dan Jumma sannan ta fita a gidan ta na b'ata rai.

Ta na fita kuwa ta sa su Ameena suka shigar da kayan parlour suka rufe qofa, cikin ladabi Ameena ta tattare kan qannen ta suka bar  wajen, ta ji dad'in hakan sosai, albarka ta sanya musu, sannan ta bubbude kayan, har da akwati qarami.

Kaya ne na sanyawa kala biyar, sai rigunan bacci, da undies ,takalma biyu, da turaruka kala kala, har da musk.

Sai dabino mai kyau mai yawan gaske, sai kayan qamshi, da bagaruwar mataa danya, ganyen magarya, da lalle .

Kaiiii makaranta abubuwa ne masu tarin yawa Hajiya ta aiko mata, har da kayan abinci da nama soyayye.

Hansatu ta na dubawa ta na godiya ga Allah, tare da sanya wa mahaifiyar ta albarka, da yi mata fatan samun cikawa da kalmar shahada.
Chapter 61 · 0% Book details