Sashe 65
A Garin Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Me ye laifi na dan na je neman abinda zan ci? Ashe ba su da kuddin da za su iya ciyar da dika mutanen unguwar mu ma ba ni kad'ai ba? Ashe ba su da kuddin da za su iya daukan nauyin rayuwa ta ta kyautatu kamar yanda suka yi wa nasu 'ya' yan? Ashe ba za su iya ciyar da ni domin Allah ba tare da sun koyar da ni mugayen abubuwan da sun ka koya min ba a yanzu? Ashe ba su da halin taimakon mutanen qasar su sun ka fito siyasa? Ba su da zuciya da kishin qasar su sun ka ce za su mulke mu? Ashe su din azzalumai ne, shedanu ne, mayaudara ne, maqaryata ne? Ashe kan su kawai suke so da iyalan su da abokan su, babu ruwan su da tallaka, ko tallaka ya ci abinci, ko tallaka ya sha Magani, ko ya sha ruwa, ko ya ga hasken wutar lantarki, ko kar ya samu wadannan abubuwa duk ba damuwar su ba ne? Idan na rantse da Allah, Allah ba zai kama ni da lehi ba, mutum guda a manyan 'yan siyasar ga ya na da kuddin da zai ciyar da unguwa guda, ya basu kuddin yanke talauci, amma ba za su yi hakan ba, sun gwammace su maishe mu lalatattu, su yi anfani da mu dan cikar burin su, sun gwammace su juyar mana da basirar da Allah ya mana dan kar mu amfanar da kanun mu komai, mu amfanar da wasu, sun gwammace mu lalace mu haukace da shaye shaye da kashe junan mu, daga yau ina musu albishirin su fara qirga lalacewar tasu rayuwar,wannan alqawarin Lawwali ne"
A guje ya bar wajen ya shiga dajin wajen, da qafa yake keta dajin cikin kuka, da hawayen shi, da Muryar shi,ya na jin yanda qayoyi ke huda kafar shi, amma bai tsaya ba, sai da ya koka duk wani baqin ciki, da bacin ran da yake ji, sai da ya fitar da duk wani qulli da ya dabaibaye masa zuciya, ya hana shi samun cikakken farin ciki.
A qasa ya zube da guiwowin shi, ya kifa kan shi cikin yashin da yake fitar da hucin zafin ranar da ya sha, sama ya kalla ya ga yanda hasken farin wata ya wadatar da dajin, sakamakon duhun dare da ya yi,ajiyar zuciya kawai yake saukewa mai qarfi, cikin wata iriyar murya ya ce,
"Na dau alqawari da Allah daga yau na ajiye duk wani abinda ni ke aikatawa mara kyawu, na kashe bayin Allah da qona gidaje da garuruwan su, na daina shaye shaye kuma zan yi hani da yin shi a sansani na, na dau alqawari da Allah da sani na ba za a qara aikata zina a sansani na ba, na dau alqawari da Allah sai na ga bayan duk wanda ke da hannu a lalacewar mu, na dau alqawari da Allah zan kawo qarshen ta'addanci a nahiyar nan tamu ta Zamfara da kewaye"
Motsi yaji, cikin duhun dajin, juyawa ya yi bayan shi,dan ganin me ne ne ke tahowa, ba ya ganin komai daga nesa, cikin itatuwan akwai duhu, inda yake kuwa fili ne fallau yashi ne sosai a wajen.
Da dukkan alamu koma me ke tahowa ya na ganin shi,amma shi baya ganin komai..........
*Hummmmmmmmmmmmmmmmmmmmmmmmmmmmmmm*
💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻
BY HAERMEEBRAERH
PAGE 48:
Motsin na sake matsowa, Lawwali na sake yin shirin ko ta kwana, duk da ya na da tabbacin cewar wannan wajen dajin shi ne, hatta da namun daji masu cutar wa duk babu, sun kashe su.
Mazaje ne guda biyar daga cikin matasan da ke sansanin shi, kewaye shi suka yi, kowanen su. dauke da makamai, mamaki ne fal zuciyar shi.
Ta ya akai ya ke tare da mutanen da za su cutar da shi be sani ba? Har ma yake basu horo da kan shi.
Bai gama tunani ba, daya daga cikin su ya kai mishi wani irin sara, cikin rashin sa'a kuwa ya same shi a dantsen hannun shi.
Cikin kwarewa da jajircewa ya murde hannun shi wuqar ta fadi qasa ya dauke ta ya yanka wuyan shi.
Fada ne sosai ya kaure tsakanin Lawwali da matasan nan, sai dai ko minti biyar ba a cika ba Lawwali ya gama da mutum hudu, ya raunata na qarshen, wuyan matashin na hannun Lawwali, ya ke tambayar shi, wanda ya aiko su, cikin kakari da azaba ya ce,
"No 5 ne Oga, shi ya ce in mun ka yi nasarar kashe ka, zai maishe mu mu zam na kusa da shi, gwamna ya yi muna alqawarin manyan kudi"
Ya na gama jin bayanin da yake so ya ji ya murde wuyan shi, makaman da suka zo da shi, ya diba, ya nufi sansanin nasu, hannun shi na zubar da jini.
Sultana na nan tsaye a bakin dajin, ta kai ta dawo, ta kai ta dawo, su Barirah na tsaye a gefen ta, suma cikin damuwa,
Ta na jin motsin tafiya ta nufi wajen da gudu, ganin Lawwali cikin jini ne ya sanya ta sanya kuka mai cin rai, ko kallon inda take be ba, No 5 na ganin Lawwali ya dawo ya diba da gudu zai bar wajen, wuqa daya Lawwali ya zaro ya saita bayan No 5 ya wurga masa, qara ya saki, tare da gantsare wa.
Lawwali ne ya isa gaban shi ya zare wuqar da qarfi, sannan ya shaqe wuyan shi, filin da suke taruwa Lawwali ya ja shi a qasa ya kai shi wajen ya wurgar.
Nan da nan ya bada umarnin kowa da kowa ya taru a wajen, cikin abinda bai kai minti hudu ba kowa ya hallara, mamaki da tsoro duk ya cika su, hasken fitilar su na solar na haske ko ina na wajen.
Sultana na gefen su Barirah a tsorace, Ita dai wannan rayuwa ta zubda jini ta fara sanya ta jiri.
"A cikin ku akwai wanda ke jin haushi na? Akwai wanda ya yi saura da ke so shi ga baya na? A cikin ku akwai wanda ya ke ganin zai hada kai da gwaunan da ya cutar da rayuwar mu dika, sannan ya yi sanadin zaman mu 'yan ta'adda, kuma ya cutar da rayuwar mu duka, akwai wanda zai taimaka masa wajen kawar dani saboda na gano gaskiya? ina so kowa a cikin mu ya samu 'yancin shi, kuma mu bar zama bayin su mu ci gashin kammu, ku na ganin akwai me so ya kauda ni saboda wannan manufar tawa? Wane ne ya yi saura? Kar na bincika daga baya na samu wanda ya yi saura,"
Shiru wajen ya dauka, damqo No 5 ya yi, ya shaqe shi da kyau, sai da ya ga idon shi ya fara alamun dauke baqi sannan ya sake shi, cikin wani irin wahalallen nunfashi yake tari, da kyar ya daidaita numfashin shi,
"Fada wa mutane me ya faru, da ka ganni ka ke so ka gudu"
Shiru ya yi kamar ba zai magana ba, Lawwali na daga hannu zai make shi ya fara bayani.
"Oga ka yi hakuri, sharrin shaidan ne wallah, tun ranar auren ku mun ka haɗa da gwamna zan kashe ka, na gaje ka, ya yi min alqawarin manyan kudi, ya kuma yi min alqawarin in na kashe ka zai aura min diyar shi, ya......"
Jinin Lawwali ne ya tafarfaso, da jin kalmar wani zai auri sultana ba shi ba, No 5 bai gama magana ba, Lawwali ya sa wuqar hannun shi ya yanke wuyan shi, jini ne ya yi tsartuwa, sultana kuwa ta zube a wajen a sume, bayan ta kwalla wata iriyar razananniyar qara.
Lawwali ne ya wurgar da wuqar a wajen, ya bada umarni a binne shi, a je can inda sauran yaran suka mutu a binne su.
Durqusawa ya yi a gaban Sultana ya dauke ta da hannu daya, ya nufi dakin su da ita.
A saman gado ya ajiye ta, ya debi ruwa ya watsa mata, zubewa ya yi a qasa, idanun shi na lumshe wa, saboda jinin da ke zuba a jikin shi.
Ko da ta farfado ta ga baya motsi, sai hankalin ta ya tashi, taimako ta nema a wajen, nan da nan masu kula da lafiyar mutanen wajen suka zo aka duba shi, aka yi ma wajen ɗinki ,sannan suka masa allurar da zata kashe masa zafi, sai magunguna na kashe zafi da aka bawa Sultana suka fita, suka barta ta na kallon ikon Allah.
Nan kuma Allah ya kawo ta, ba komai da sanin shi, zata yi hakuri da qaddarar ta, fatan ta Allah ya bata ikon cin jarabawar nan.
Ta na nan zaune ta tuna da bata yi isha'i ba, a hanzarce ta fita, ta yi alwala, ta koma dakin, ta hau sallah.
Ta na idar da isha'i ta yi shafa'i da wutiri, sannan ta dora da nafilfilun da bata san adadin su ba, ta na sallah ta na kuka, tare da roqon sauqi akan lamurran da ke faruwa a kowacce sujjada.
Fatan ta Allah ya shirya mata mijin ta, ya kawo qarshen wanan zubar da jinin da ya dauka kamar ba komai ba.
Sai da ta ji idon ta ya mata nauyi ta kasa bude shi sannan ta hakura ta dena sallah, ta kwanta a gefen Lawwalin da ke qasa,kwantar da kan ta tayi a qirjin shi ta yi lufff kamar yaron da ke jin sanyi.
Hawayen ta na diga cikin baccin da ya dauke ta mai nauyin gaske.
Lawwali ne ya bude ido a hankali, jin kamar an danne shi ne ya sanya shi kallon saman qirjin shi, ganin ta ya yi ta haye jikin shi ta yi lufff,hawaye na sauka daga idon ta, duk da cewa bacci take.
Cikin tsananin tausaya mata ya rintse idanun shi da suka kada suka yi jawur.
Ba zai kyale Gwamna Halliru ya qara rayuwar farin ciki ba, in ma ya bar shi ya yi rayuwar farin ciki bai haifu ba cikin asararrun iyaye kamar Dan Talo da Lamishi ba, wanda ke haifawa duniya annoba, kuma su ci gaba da rayuwa cikin kwanciyar hankali .