← Book details Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 78

Sashe 9

Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Sunana Zuhra Ismail, nazo nan pre test. I just hope kema Haka?"

Na daga Mata folder nace

" Of course! I'm Unaisa Yahya"

Ta danyi Jim tace

" Usaina?"

Na girgiza Kai nace

" UNAISA! Unaisa"

" I've never heard of your name fa"

Nayi dariya a hankali nace

" Nima ni kadai na sani me sunan"

Ta kamo hannuna tace

" Wuce muje Yaya Man na jira mu tafi,  har na shiga mota yace min wai kalla wata kyakyawa, shi ne na dago se kawai na ganki."

Na danyi murmushi nace

" Wai kyakyawa"

Tayi dariya tace min ai ita ta Jima Bata ga me kyau Irina ba, inata dariya na Ciro wayata daidai lokacin da take cewa

" Kizo mu tafi Mana"

Na nuna Mata wayata nace

" Zan Kira Anna na fada Mata"

" Wacece Anna? Your Mom?"

Na gyada Kai Ina Kara wayar tawa a kunnena, Anna ta dauka tana fadin

" Adda kin gama?"

Kafin nayi magana ta kwace wayar a hannuna ta Kara a kunnenta tana fadin

" Anna Ina wuni? Sunana Zuhra, kin tuna min hadu daku a mota wancan month din?"

Banji me Anna tace ba Amma daga Murmushin da Zuhra keyi nasan ta samu,

" Yawwa Anna zamu taho da ita, na Miki alkawarin har gida zamu kawo ta nida Yaya Man"

Inata kallon ta Ina ayyana bazan iya abinda tayi ba, I'm not friendly sosae, ni din ban fiye sakin jiki sosae da mutane ba, shiyasa ko a secondary banyi kawaye ba, Babu wata wadda zatace ita din kawata ce shakikiya, karatu kawai nakeyi tunda shi aka kaini nayi. Shiyasa Anna kullum na yimin fadan na dinga sakin jiki da mutane, kalli yadda ta saki jiki da dai zakai tunanin ni da ita munsan juna ko Kuma irin mu Saba dinnan sosae, ta saki jiki sosae damu.

" To Anna nagode se nazo "

Haka ta Miko min wayar ta ja hannuna muka nufi wata Ash din Benz, Kai ba se an fada maka ba, kana kallon kayanta kana kallon ta kasan Yar masu kudi ce. Kuma kana kallo kasan arziki a cikin shi ta tashi, Dan kuwa Wanda ya tashi cikin arziki ya jiku dashi zakaga bashi da girman Kai Amma Dan talaka se karya da hura hanci. Su biyu ne a motar dukkan su a gaban mota, daya Yana sanye da black trouser da Ash top, fuskarshi sanye da brown shades, dayan Kuma clad in Ash shadda se maiko takeyi, Kan shi Babu hula Amma Kuma tana aje Akan dashboard din motar. Ina Zama na gaishe su dukda a dadare nake, Suka amsa

" Wannan shi ne Yaya Man, he's Yaya Suleiman"

Na danyi murmushi nace

" Sannu Yaya Man"

Ya juyo tare da cire shades din fuskar shi yace

" Sannu! Ya exams din?"

Nace alhamdulillah sannan ta dubi dayan tace

" He's Yaya Saif, shi nake bi"

Nayi murmushi na gaishe shi sannan muka dauka hanya, sunata Hira Kuma duk ciki se ta saka ni a ciki Dan na ware Amma still nayi shiru Ina jin numfashi na Bai Gama daidaita ba. Seda muka shiga Kano nayi Masa kwatance har kofar gida, na dubi Zuhra nace

"Zuhra nagode sosae, ku gaida Mama. Yaya Man nagode"

Wani kallo tayimin tace

" Tare zamu je, se na gaida Anna ai. Yaya Man just five minutes"

Saif ya dubeta yace

" Wallahi zamu tafi mu barki banza uwar shishiggi"

Ta bata Rai Amma taki sakin hannuna tace

" Yaya Saif Babu ruwanka! Yaya Man Bari na Shiga na fito"

Bata ma jira su ba su amsa Mata ba ta bude muka fice, da sallama muka shiga ciki, dukka suna zaune Anna na buga lissafi cikin karamin littafi yayinda Nuzla ke dama fura. Da murmushi Anna ta tare mu, Zuhra ta rungume Hunainah bayan ta gaida Anna, tace

" Hunainah kin tuna ni?"

Ta girgiza Kai tana tsotsan alewa, Zuhra ta dubi Anna tace

" Anna Kinga Bata gane ni ba Wai"

Anna tayi dariya tace

" Ai halin Unaisa ne da ita, zauna Kisha fura"

Ta kalli Nuzla tace

" A'a jirana ake Anna, Zan dai dawo na yini"

Anna ta tada Nuzla ta dakko jug ta juye Mata furar ta kulle a bakar Leda sannan aka dakko flask an soya awara nasan saboda ni ne, ba karamin so nake yiwa awara ba, tayi Murmushin jin dadi tace

" Anna nagode Ina son awara wallahi. Kai Anna nagode"

Anna tace

" Banda abinki Zuhra wa kikaga Yana yiwa uwarshi godiya"

Ta mike na rike flask din ita Kuma ta rike jug din furar, Nuzla da Badi'a Suka biyo bayan mu har mota muka rakata mukai exchanging contact ta wuce na dawo gida. Se lokacin na zauna na mimmike kafa nace

" Anna Kinga tana da kirki ko?"

Nuzla tace

" Wallahi ni na fara sonta, she's very wise kiga kamar ta Dade da sanin mu"

Anna tayi murmushi tace

" Dama hakane ai, Allah ya Mata albarka daku Baki daya. Adda oya kici abinci"

Na bude flask din na zauna naci sosae sannan nayi wanka nazo mukai ta Hira. Se dare sannan Anna tace min na Kira zuhra naji yadda taje gida, na dauki wayata nayi dialing number dinta bugu daya ta dauka

" Unaisa!  Yanzun nake bawa Dada da Abba labarin ki, shi Abba ya manta ki Wai"

Nayi murmushi nace

" Zuhra kenan! Ta Yaya zai tuna Dani. Come-on ya kikaje gida"

Karshe dai seda ta kaiwa har Abban ta muka gaisa dashi Haka ma mahaifiyar ta Dada.

Unaisa is not free, pay N300 to 3091721807 First Bank of Nigeria and send evidence of payment to 09063467258
[5/12, 10:10 PM] Hauwa Galadima: 🧕 UNAISA 🧕

*I*

Ayshatuuu

Lokuta da dama mukan dauka cewar choice din mu ne haduwa da mutane, Amma idan muka nutsu mukai tsam da ranmu zamu gane cewar komai a rayuwar Dan Adam is destined, it's written. Kuma dukkan Wanda aka hadu dashi akwai manufa da Kuma hikimar hakan. Haduwata da Zuhra na dauka kawai choice Dina ne da na kulata har ta Zama kawata,  Amma Bayan lokaci me tsawo se na fahimci through her akwai abubuwa da Allah ya tsara Wanda ni ban sani ba. Zuhra mutuniyar arziki ce. Bayan Anna ita ce mutum ta farko da na fara bude Baki na Kira da kawata, duk da halayen mu by far sun banbanta nesa ba kusa ba, ita din mutum ce carefree and friendly yayinda nake akasin hakan, ni mutum ce me wahalar sabo kamar inada kin yarda, ko Kuma Ina tsoron been attached to someone Kuma ya tafi ya barni. Kullum Rana idan na tashi to se Zuhra ta kirani Wai kawai taji yadda nake, sede nayi dariya kawai nace ai lafiyata kalau, wani lokacin Kuma idan ta Kira se ta ce min wai banji komai ba Akan exams dinmu, har ranar nace ta jira Zan Kira Yaya Yusuf na tambaye shi, ko Dana Kira shi se yace min ai Yana Hanya zai zo gidan. Dan Haka na fito na fadawa Anna, ta dubeni tace

" Ni Wai meye ne tsakanin ki da Yusuf din Anty Nanah ne?"

Na bude Baki da mamaki nace

" Anna menene tsakanin mu kuwa? Kawai na Kira shi naji maganar makaranta ne saboda Zuhra ta takura"

Ta nuna min gefenta alamar na zauna, na samu guri na zauna gabana nata faduwa, tace

" Unaisa ba takura muku nake ba, Amma kinsan yadda komai ya kasance a rayuwar ku, Ina son ki manta da zancen wasu samari ki maida hankalin ki kiyi karatu, lokacin aure zaizo, lokacin da zakiyi samari Yana nan zuwa. Ni ki kalleni shekara ta Sha biyar akai min aure ko yadda zanyi sallah daidai ban Gama sani ba, ki kalla irin abinda na tsinta a aure me naci riba, Dan haka kudinnan komai da nake jurewa saboda kune, ki daure kuyi karatu kinji Adda?"

Na gyada Kai na Ina goge hawayen fuskata da tuni na fara kuka nace

" Allah Anna ki yadda Dani Babu wani Abu tsakanina dashi, ban taba tsayawa da wani..."

Tayi saurin katse min rantse rantsen da nakeyi tace

" Na sani Adda, kawai dai Ina tuna miki ne. Kin gama girkim?"

Na girgiza Kai tace to naje na karasa, na Mike da sauri na fita kamar Zan kifa, na shiga kitchen na karasa stew din sannan na jujjuye na gyara kitchen din. Ina gamawa Badi'a da Hunainah na shigowa, na dube su duk sun gaji nace

" Sannun ku, kuje ku cire uniform kuzo kuci abinci"

Badi'a ta saki murmushi tace

" Kai wallahi Adda kamar kinsan Yunwa nakeji"

Hunainah ta tsaya tana hura hanci tana tambayata abinda aka dafa, nace ta wuce ta bani guri, ta tafi tana bubbuga kafar ta. Babu jimawa se gasu sun fito daidai shigowar Nuzla, Dake Shirin fara waec, shiyasa take dawowa daban da kowa. Ta dubeni

" Adda an Gama abinci"

Anna dake fitowa daga bedroom tace

" Haka dai kullum kamar kamun Yunwa"

Tayi dariya ta wuce ciki, tray na dakko na hada Mana dukka Dan yawanci tare muke cin abinci, dukka tare muka zauna muka fara cin abinci, Bayan mun Gama Anna ta zauna tana bamu labarin yarintar Nuzla dukda wani abun na sani, tunda Zan iya tuna yarintarmu tare, Muna ta Mata dariya ita Kuma ta hade Rai tana fadin

" Allah Anna so kike Badi'a ta dinga tsokanata ko"

Anna ta dubi Badi'a wadda har ciki take rikewa saboda dariya tace

" Kayya ba gwara kowa akan nata ba, ita me kukan Madara ma"
Chapter 9 · 0% Book details