← Book details Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 78

Sashe 59

Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nayi sauri na gyada Kai na, cikin muryar lallashi yayi ta bani baki sannan yace min

" Saboda Babyn jikin ki, Zaki developing PTSD, kina so?"

Na girgiza Kai yace

" To ki dinga mishi addua and take care of yourself"

Se na tuna wani lokaci da yace min

" As long as you're alive stay positive"

Hawaye Shar suka Kare wanke min fuskata, Abiey da na so, Abiey dake so na Wai Babu shi. Karshe dai aka dudduba ni sannan yace ba wani matsala mu tafi Dan idan na zauna Kuma Zan iya cigaba da damuwa gwara mu tafi. Na mike na shiga toilet na wanke fuskata sannan na fito na Kara gayra zaman mayafi na, nayi musu godiya Muka fito, key Dina na mikawa Al'amin dake tsaye jikin motata nace

" Nagode sosae, ka aje min idan Muka dawo Monday se na karba"

Ya saka hannun shi ya karba Yana Mana Allah ya kiyaye Hanya, Baba Asabe ta dakko duk abubuwan mu na ciki, na riga na shiga motar Noor akan cinyata, motar shiru se radio dake faman yi, a Haka Muka cigaba da tafiya wajen Gaya na dubi Baba Asabe nace

" Ina abincin da na taho dashi?"

Ta Miko min ledar Baki daya, na dauka stick daya na bawa Noor sannan na fara ci, Zuhra ta juyo tace

" Kurmusu kuke yi? An manta damu"

Na danyi murmushi na Mika Mata ta dauka sannan ta tambayi Yaya Khalifa ko zaici yace a'a ya koshi, una Gama ci bacci yayi gaba dani. Ban farka ba seda muka iso kano, Ina bude idanuna nace

" Zuhra Ina wayata? Bari na Kira Abba"

" Ya Kira kina bacci yace Wai ki wuce can gidan ki"

Har Raina gidan Anna nake son Zama Amma Kuma Babu yadda zanyi Dan bazan iya musu da Abba ba. Jin nayi shiru ta juyo tace

" Ta kikai shiru?"

Nace

" Ba komai"

Daga Haka bamu Kara magana ba, seda muka je gidan, Yana nan yadda yake sede Babu securities dinnan masu yawa da zasu bude maka idanu, na girgiza Kai Ina ayyana rayuwa kenan! Na sakko kafafuna har suna kokarin kumbura, hannuna rike da na Noorham muka shiga, kofar parlon na tura bakina dauke da sallama, Babu kowa a zaune, na shiga na zauna, Zuhra da Baba Asabe Suka shigo suma, nace

" Zuhra Dan hau sama kiga ko tana can"

Zuhra ta hau sama Babu jimawa se gasu sun dawo tare, tunda ta sakko take kallona har ta karaso ta zauna, na Dan risina na gaishe ta

" Barkan ku da zuwa ya hanya?"

Nace

" Alhamdulillah!"

Se duka mukai shiru Kuma, se tace min

" Ya jiki jiki? Babu matsala '

Nanma na amsa ta, Zuhra ta mike tana fadin

" Mamaa my zamu tafi, se mun dawo gobe Inshaaa Allah"

Ta dubi Zuhra dake kokarin daukar Noor tace

" Ki gaida Hajiya Zainab"

Ta amsa da to ni Kuma na mike na fita raka Zuhra, tace min

" Ki koma Haka nan, se munyi magana kafin na zo goben, ki Kara hakuri Dan Allah, take care of yourself"

Na gyada kaina na Bata sakon ta gaida Dada da Abba da Hunainah! Na dawo ciki na tarar Babu Baba Asabe din, se kawai na zauna banyi kokarin zuwa ko Ina ba, ni nasan bani da daki a gidan, wancan zaman ma da nayi temporarily na zauna me yasa Abba zaice na dawo nan na zauna. Se ga Baba Asabe ta sakko, tace

" Hajiya na Kiran ki"

Na mike tana min fadan na saki raina Haka nan, Amma duk ba zasu gane yadda nake ji ba. Tana zaune a parlon ta, na zauna Dan nesa da ita Kan cushion tace

" Kinga yadda lokaci ke gudu gashi har Zan fita takaba"

Na Dan kalleta se Naga kuka take, hakan ya karyar min da zuciyata, tace

" Kullum idan na tuna bamuyi ma wani rabuwa me dadi ba hankalina tashi yake, ban kawo Masa mutuwa ba Unaisa, ban taba kawowa zai tafi ba Unaisa, da duk abinda nayi da bazan Yi ba, dukda nasan bashi da riko, duk abinda nayi a lokacin ya kanyi min uzuri tare da cemin yasan kishi nake, Amma dukda Haka na Bata muku Unaisa, bani da damar yin magana dashi se ke, kiyi hakuri!"

Na girgiza Mata Kai nace

" Ba komai Mamaa, komai a rubuce yake shiyasa komai ya faru a Haka. Allah ya gafarta mishi ya kyautata zuwan mu"

Ta amsa da Amin sannan mukai shiru abin mu, har ta daina kuka, tace

" Nasan kin gaji, na saki gaba Ina kuka, kije can ki zauna"

Inda ta nuna min dakin shi ne, na mike tsaye na bi bayanta, parlor ne da bedroom da Kuma dressing room a ciki se toilet da Dan karamin library, na zauna saman kujera ita Kuma ta juya ta fita, lallai da gaske mutuwa tana nutsar da mutane, tabbas mutuwa yare ce Dake ladabtar da zuciya, wacece ni da zaa bani bangaren Abiey na zauna, akwai lokacin da tace mijinnta baya son hayaniya, nayi murmushi Ina shigewa bedroom din, Babu wani memories tunda bansan shi a gurin ba, na cire kayana nayi wanka sannan na saka doguwar riga royal blue na daure gashina da karamin Dan kwali na dawo parlon Ina jin cikina Yana kugi, Baba Asabe tace

" Matar tana da kirki"

Nayi murmushi na gyada kaina bance komai ba, nayi sallah sannan na fita zuwa parlon ta, na same ta tayi Baki, har Zan juya tace

" A'a shigo Mana ku gaisa"

Na karasa shigowa fuskata da Dan murmushi akai muka gaiggaisa, wasu na min kallon kurilla, wasu suka watsar Dani wasu Kuma Suka saki fuska kamar yadda na saki tawa, a zuciyata nace a banza man kare, aikin Gama dai ai ya riga da ya gama. Ta gabatar min su matsayin kannen ta da wasu yayunta da matan Yan uwanta, na sake musu sannu da zuwa sannan nace

" Yunwa nakeji"

Tace

" Na Manta fa, akwai abinci a kitchen Amma Zaki iya sauka?"

Nace

" Zan iya"

Daga Haka na juya na sauka kasa na samu karamar warmer na zuba abincin, se ga me aikin ta wadda tun Yana da Rai na santa, na gaishe ta mun danyi sabo zaman da nayi Bayan rasuwar Abiey, tace

" Ai yanzun nake Shirin kawo Miki abincin, ya Hanya ya jiki jiki?"

Na danyi murmushi bump Dina sosae ya fito ko baka San inada ciki ba da ka kalleni zaka San ciki ne dani, na amsa se tace min naje zaa kawo na juya Ina fitowa mukai kicibis da Ahmad, da dukkan alamu dawowar shi kenan daga aiki, muka Dan kalli juna briefly sannan nace

" Ina wuni?'

Yayi murmushi Yana karasa Zama yace

" Anty Unaisa Kun karaso ya Hanya?'

Nace

" Alhamdulillah!'

Daga Haka ban Kara cewa komai ba na nufi staircase, ya bini da kallo baiyi tunanin ina da riko har Haka ba,ya mike ya fita, kokarin gani yake ya daidaita duk wannan rift din dake tsakanin mu, to Amma ni Kuma bana tunanin Zan Kara sakin jiki dasu kamar komai Bai faru baz gwara shi Akan Aseey, gwara shi his was magana Amma ita taje beyond limits dinta. Babu jimawa aka kawo Mana abinci naci nayi makil, hannuna ma ban wanke ba baccin ya daukeni, yanzun abinda nake yi kenan, da naci abinci se bacci shiyasa bana cin na koshi idan ina wajen aiki. Se maghrib sannan Baba Asabe ta tashe ni hannuna har ya bushe, nayi sallah sannan nazo na Kira duk Wanda ya dace, anan Naga calls din Al'amin, I can't ignore his call Amma bana son Kuma wata tarayya dashi musamman da har yanzun takaba nakeyi. Amma na dauka muka gaisa

" Ya Hanya?"

Nace

" Munje lafiya"

Yace

" Allah ya Kara lafiya, a gaida su Nuzla"

Na amsa da Amin daga Haka mukai sallama. Da wurwuri nayi Shirin kwanciya, har na kwanta se ga Kiran Mamaa a wayata, na tashi na zauna na dauka, tace

" Abban ki yazo zai ganki Zaki iya sakkowa"

Nace

" Eh gani nan'

Na dubi jikina na samu katon hijab na saka, na dauki wayata na fito, Yana zaune da Ahmad da Mamaa, na karasa na zauna saman carpet Ina gaishe shi, ya amsa yace

" Me ya sameki aka cemin kin suma"

Se na fada masa duk yadda akai, ya Kara min nasiha akan komai zai wuce na cigaba da hakuri, seda muka je bakin mota no dashi ya bude zai shiga se yace min

" Wai Ahmad yace Wai Baki Masa magana"

Na kalla Abba dake murmushi nace

" A'a Allah Abba Ina Masa magana, ko dazun mun gaisa"

Se yace

"Wai Yana so kiyi hakuri ki dawo yadda kuke da"

Nayi murmushi nace

" A'a Abba! Kawai dai mu cigaba da gaisawa yafi"

Ya gyada Kai ya min sallama ya tafi na dawo gida, na hau sama nayi bacci, washegari muna tashi nayi wanka na sakko ko zaayi aiki tunda nasan zatayi Baki masu zuwa Mata murna da taaziyya. Seda na shiga na gaida ita sannan nace Mata

" Akwai abinda zaayi yanzun?"

Tace

"A'a ki koma ki kwanta"

Nayi murmushi nace

" Ai idan bana aiki jikina ciwo yake"

Tace dukda Haka na koma daki dai, se na tafi na dauki wayata Ina dudduba slides Dina Dan min kusa exams, ban Jima ba naji sallamar Aseey a parlor, na kashe wayar na kwanta na juya baya, Haka kurum ba na son ma magana da ita, Ina jin tana cewa Baba Asabe tayimin magana, Baba ta shigo ta Dan tsaya a kaina se Kuma ta juya tace Mata bacci nake, ni Kuma kawai bana son fitowar ne. A Haka har azahar tayi Sega su Dada dasu Anna, seda Suka fara zuwa can sannan Suka taho nan. Da murnata na tare su mukai ta Hira wajen laasar suka tafi ya rage ni da Zuhra da zamu fita zuwa gidan Husna ta haihu. Na shirya tsaf muka fito se lokacin Muka hadu da Aseey, tana tsaye da robar kunun Aya a hannunta, tace

" Anty Unaisa ya gida? Dazun nazo kina bacci"

Nace

" Ayya an wuni lafiya?"
Chapter 59 · 0% Book details