← Book details Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 78

Sashe 61

Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na danyi dariya kadan nace

" Ayya mana kwana nawa ne ma ya rage ka dinga ganina kullum har se na isheka"

Yace

" Wayace Miki Zaki ishe ni, kamar kina underestimating soyayyar da nake Miki, karki damu Allah ya bamu taawon Rai I'll show you"

Nace

" To Allah ya kaimu, King Dan Allah ki fada zakai kada kayi sosae kaji?'

Yace

" Naji, se munyi waya'

Daga Haka mukai sallama, Nuzla Dake kallona tace

" Burgeni kuke wallahi, Amma kinsan ni fa mamaki kuke bani, ta Yaya zsku dinga son juna har Haka, I really can't love someone so deeply hakanan'

Nayi dariya nace

" Kinsan me yasa kike ganin Haka, Baki taba son wani so sincerely bane, da a ranar Zaki fahimci how deeply love can be, ni ban yarda soyayya kike ba kawai Kuna shirme me"

Tayi dariya tace

" Se kaji kamar Zaka haukace idan ka rabu da mutum shi ne soyayya?"

Na girgiza Kai nace

" Ko kadan ba Haka bane, soyayya shi ne ki manta da dukkan wasu protocols din ki, ki manta wanne kalar mutum kike so, ki kalla flaws din mutum kiyi overlooking flaws dinnan...zamu iya kwana Ina fada Miki kawai dai Ina fatan kin dandana me akeji Zaki gane!"

Wanda Bai taba so ba bazai gane menene so ba, gashi dai kalma biyu ce Amma ita din tana da girman gaske, ni na yadda da so na Kuma yadda it can do and undo. Ko da yaje gida suna zazzaune ya same su, sallamar shi tasa suka Mike tsaye kamar yadda suka saba, ya dube su suna Masa sannu da zuwa ya amsa, Ahmad ya karaso zai karba briefcase din shi daga hannun security din shi, Abiey ya daga masa hannu yace

" Muhammad karba"

Yaya Muhammad ya karba yabi Bayan Abiey sama, Ahmad yayi shiru yana Jin wani irin abu na rashin jin Dadi a zuciyar shi, me yasa Abiey zaiyi Haka ne. Seda ya watsa ruwa sannan ya sakko ya San Mamaa Bata dawo ba, suna zaune har da Bilkisu, idanun ta a warwaje Dan ita Haka kurum take tsoron Abiey, gashi Muhammad Bai San tayi hakan ba. Ya zauna Yana kallon su daya bayan daya kafin yace

" Ina jinki Asiya, ya akai?"

Ta kalle shi sannan ta kalli Yan uwanta, to me zatace? Ita dai tasan Bata da abin fada

" Nayi tunanin Nima Zaki ce Zaki dakeni ne, Ashe ban Isa daku ba kenan? Kuna ganin abinda kuke Yi bazai dawo kunnena ba? Na Tara ku na fada muku zanyi aure saboda bana son kuji a wani gurin kuji rashin jin Dadi Ashe ni bansani ba na Baku license ne na ci Mata mutunci ko? Asiya ke da Bilkisu har kunje zaku daketa ko? Ai ni nace Zan aureta ni zaku daka, Kuma ku sani duk abinda kuka Mata ni kukai yiwa, Kuma from now henceforth I'll not tolerate any shit from anyone of you. Ai na lallaba ku, Amma tunda abinda kuke so kenan, I'm equal to the task"

Yayi ta fada kamar zai Ari baki, duk sukai shiru kamar ruwa ya cinye su, Babu me magana a ciki, Yana gamawa ya mike tsaye dama yasan halin yayan sa, ficewa yayi daga parlon Baki daya zuwa can baya, ya zauna Yana duba news headlines cikin wayar shi. Yafi minti talatin sannan yaji sallamar Ahmad, ya dago ya kalle shi ya watsar ya cigaba da karatun shi, Ahmad ya saka gwiwoyin shi kasa yace

" Abiey kayi hakuri! Abiey nayi laifi Dan Allah ka yafe min, kayi hakuri"

Ya dago ya kalleshi yace

" Get up ka zauna, waye zaka zo Kan durkusawa"

Jiki a sanyaye ya tashi ya zauna ya cigaba da rokon shi yace

" Ahmad ya wuce, ba dai ni kukai ganging against me ba, Kuna ganin yin hakan zai sa na fasa? Mu zuba no daku zanga Wanda zai janye"

Ahmad yaki tashi ya cigaba da rokon Abiey har seda ya saurare shi sannan ya tafi, a parlor Muhammad ya mike bayan fitar Abiey ya dubi Bilkisu

" Abinda kikai kenan, Ina ruwan ki? Ina ruwan ki da harkar gidan mu? Meye matsalar ki da auren shi, kinji Allah ko ko kallon banza ki Kara Mata Zaki tafi gida, Babu Wanda ya Isa Raina min ubana, ke ba wancan satin baban ki ya Kara aure ba, kije ki Masa rashin kunya Mana. Tashi kije ki bashi hakuri!'

Ta kuwa mike tana bubbuga kafa, ta nufi wajen Abiey ya dubi Aseey da kamar ruwa ya cinye ta yace

" Da auren mu da Bilkisu auren baban ta uku, Kuma kowacce yarinyar ce da Bata kaimu ba, ta taba gayyatar ki kije ki Daki matar baban! Se ke da kika raina naki uban so you invited her ku dauki Unaisa, you're mad, you're selfish meye matsalar Unaisa? Ita taga Abiey tace tana son shi? Ko Kuma shi yayi making move akan ta? Kiyi abinda ya dace kafin lokaci ya kurr miki, kizo kiyi kukan da ba zai Miki amfani ba!"

Unaisa is not free, pay N300 to 3091721807 A'isha kwalam Hassan first Bank of Nigeria and send evidence of payment to 09063467258.
[6/23, 10:15 PM] Hauwa Galadima: *A³*

Bayan maghrib ya kirani Yana fada min yadda sukai dasu Ahmad, duk ban ji Dadi ba musamman sanin da nayi Ahmad ko zagina baiyi ba, yadai Yi cutting duk wani relationship tsakanin mu. Nace

" Ayya Abiey shi fa Yaya Ahmad Babu abinda yayi fa"

Yace

" Waye ya fada Miki? Wai Unaisa yaron nan har yayi girman daina min magana?"

Naji wani irin rashin jin dadi, ya cigaba da fadin

" He wanted a project badly, da kyar na sama Masa project dinnan, could you believe yaron nan yace min wai baya so saboda zanyi aure, haba Beautiful ko karuwa Zan kawo ni ban cancanci Haka daga gurin yaran nan ba, I thought na Isa dasu ban sani ba Ashe mahaifiyar su ta fini power, I'm not tolerating any shit, ni na haife su Basu Suka haife ni ba"

Ganin dai ran shi Babu dadi na dinga lallashin shi, na Masa Hira me dadi da na tabbatar zata faranta ransa, tabbas na yadda da son da yake min, ya ware muka Sha hirar mu me dadi.

A hankali ranaku suka dinga tafiya suna komawa sattittika, a kalla seda mukai sati bakwai bamu hadu dashi ba, abinda bamu taba ba, nasan bamu haduwa akai akai Amma Kuma Bai Kia yawan wannan ba. Yayi tafiya yaje London yayi sati biyu da ya dawo Kuma an fara kokarin yin zabe suna ta kaiwa da kawowar yadda zasu daura wani Dan yace min shi Kam he's ok da abinda yayi, yayi 2 tenures to gara ya dawo gida ya zauna ya saka ni a gaba Yana kallo, if only munsan zai rasu, Kai jamaa Haka muke tafe ba tare da sanin mu din gawa bane, bamu San cewar mutuwa na jiran mu ba. Ya Allah ka gafarta Mana, ka kyautata zuwan mu, ka jikan Wanda suka gabace mu. Ko a mafarki, ko a Wasa ban taba kawo Masa mutuwa ba, Kai bashi kadai ba kowa ma, mutuwa was the last thing cikin zuciyata, I was too engrossed and busy cikin soyayyar shi, Ashe Ashe komai da yake bankwana yake min. Ya Allah!

A safiyar da nake kokarin tafiya kano saboda na Gama duty na, nayi wanka Ina kokarin Shan tea wayata tayi ringing, na dakko se Naga Naima ce, colleague Dita ce unit dinmu daya. Na dauka muka gaisa sannan tace min

" Anty Unaisa kin tafi kuwa?"

Nace

" A'a Naima Ina nan, akwai wani Abu ne?"

Tace

" Dan Allah Anty Unaisa ki fita min morning idan ban takura ki ba, Dan Allah inada babban uzuri"

Nayi shiru Ina tunanin yadda zaayi, na Gaya ma King Zan dawo, tun shekaran jiya yake daukin dawowa ta, na hadiyi yawu, se tace

" Idan da wani abun kawai ki bar shi se na duba naga was Zan samu"

Na girgiza Kai na nace

" Karki damu Zan fita Miki, ki Kira chief ki fada Mata"

Tayi ta min godiya, na mike jikina a sanyaye na nufi wardrobe na Ciro blue din uniform na saka, na dawo na Kira Abiey Bai dauka ba hakan ya tabbatar min bacci yake, na tura Masa message din bada hakuri da Kuma abinda ya faru sannan na Sha tea din nayi wrapping brown yam cikin foil paper na fito, Anty Yusra na zaune tana ta kwabe leave, ganina da uniform tace

" Ba off kike ba?"

Na Dan zauna na Mata bayani, to duk sun San Naima, na girme ta Amma tana da kirki tana yawa zuwa gurina, a sati se tazo sau you gidannan, wani lokacin anan zatayi har dinner sanann ta tafi, Dake wajen Jakarta take zaune Kuma irin zaman ba wani dadi yake ba. Tayi min Allah ya tsare na tafi, ina zuwa muka fara aiki Babu jira. Idan kana aikin asibiti kana Kuma tare da Mata anan zaka fahimci yadda duniya take ciki, a aure har yau na kasa fahimtar inda matsalar take Amma abinda na sani Mata suna Shan wahala, musamman ace matar kauye suna amsar azaba kamar Babu gobe, dukda yadda ake dahuwa a Nigeria Amma akwai abubuwan da baa kamanta adalci kwatakwata! Kamar abinda ya faru a lokacin, na Gama conducting delivery na wata mata, Bayan na Gama gyara wajen inata tsokanar ta

" Wata Tara Ina jiran ki ki dawo"

Tayi murmushi tace

" Na bar Miki, wannan azabar har Ina se na huta tukunna"
Chapter 61 · 0% Book details