← Book details Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 78

Sashe 66

Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya karaso wajen, yadda yake tafiya Se nake ganin kamar Abiey ke tahowa, Allah se bayan Abiey ya rasu sannan nake ganin kamar shi da Ahmad, na saki murfin motar lokacin da ya karaso ya tsaya gabana, nace

" Ina wuni?"

Yace lafiya Lau Suka gaisa da Zuhra yace min

" Fita zakiyi?"

Na gyada Masa Kai se yayi murmushi yace

" Ba'a fita idan ana takaba, Hala Baki sani ba?"

Se na kalleshi da kyau nace

" Na fadawa Mamaa ai Kuma batace komai ba"

" May be she got carried away, idan Abu kike so lemme do it for you, amma ki koma ciki"

Jikina ya Kara yin sanyi, shiyasa Ashe Abba yace da zai nema alfarma wajen aikin da na daina zuwa na zauna gida. Na juya ba tare da nace komai ba, Zuhra ta biyo ni tace

" Menene ba kuka dai zakiyi ba ko?"

Na danyi murmushi nace

" Kai kamar wata Baby"

Se tace min

" Ai Abiey ya shagwaba ki ne"

Kawai se taga idanuna sun ciko da kwalla, Yes Abiey was beyond enough, Abiey ya min abinda ban sani ba ko akwai me kwatanta hakan. Na wuce parlor na samu Mamaa na sakkowa, tana ganina ta saki ajiyar zuciya wadda na iya gani ta yadda kirjina yayi relaxing, tace

" Ba'a fita Unaisa mantawa nayi, ki koma daki kinii Kamar yau ne kin haihu"

Na gyada kaina Amma bance komai ba, se ta juya zuwa sama Nima nabi bayanta, kowa ya nufi inda yake, straight bedroom na wuce na kwanta Wanda nasan ba bacci ma zanyi ba, tunda laasar ta wuce. Karshe Zuhra ta tafi ita daya ni Kuma na zauna. Ko da dare yayi gidan yayi shiru kowa ya kwanta, na dauki wayata Ina kallon wasu videos din mu ni da shi se kuka, bansan yaushe Zan Saba da rashin shi ba, bansan yaushe zanji it's ok lemme move on, bana tunanin akwai wannan ranar a kundina, na Jima Ina kuka idanuna sukai jawur na kwanta Ina sauke ajiyar zuciya, zuciyata raguwa ce tuntuni Amma rashin Abiey yafi komai tarwatsa ta, ta Ina Zan kawo zai rasu ya barni, ban taba kawowa ba, ban taba tunanin hakan ba.

_When I'm by myself, looking at photos and videos that we took_
_I've been keeping for so long, with my broken heart, I see all the pictures of myself_
_living without you just feel so wrong_
_I want you to be here with me, I know it sounds crazy_
_I miss your laugh and I miss everything we used to be_
_And even if it is just for a while, then please God give us the time_
_I can't deal with the reality, bcuz there's nothing more I can do_
_and my heart is missing you..._

Washegari Dana tashi nayi sallah se na koma na kwanta banma fito ba, ni ba bacci nake ba ni a kwance kawai nake, duk wannan rayuwar ta ishe ni, Ina Yi ne kawai cikon umarni tunda bazan iya kashe kaina ba, Kuma bazan iya rokar na mutu ba, Amma komai Babu dadi I find pleasure in nothing, I'm broken and shattered beyond repair, Allah ma yasa akwai masu lallashi na, da may be tuntuni na zauce na haukace sannan Kuma addua tana sanyaya min zuciya. Se takwas nayi wanka na saka Kaya har yanzun dai bana saka Kaya masu haske ko kwalliyya, dukka yawanci plain materials ne masu bubu ko A shaped gown. Na taje kaina na daure shi, na kalleni a madubi, Ina shafa Kan Ina tuna ranar da ya fara taba gashin yace a kunnena

" Duk wannan naki ne?"

Dake bana cikin nutsuwa ta sosae saboda hannun nashi ba iya gashin ya tsaya ba, na gyada Kai yayi kissing gashin yace

" I love it, I should have known my beautiful is hairy"

Na cigaba da shafa shi a hankali Ina lumshe idanuna, I missed you Abiey, Allah ya maka Rahma, ya kyautata zuwana. Cikina da yayi motsi nayi murmushi Ina maida hannun nawa Kan bump, ni daya kawai nasan cewar twin gestation nake dashi, kowa dake maganar cikin yayi girma Babu Wanda na fadawa sede nace ance Haka cikin fari yake, ko Anna Bata sani ba. Knocking a kofar bedroom din yasa na saka hula na lulluba veil a saman jikina na fito, Baba Asabe ce fuskar ta dauke da murmushi tace

" An tashi lafiya"

Na gaishe ta sannan na Bata waje ta shiga Dan ta gyara dukda na gyara gadon, na kawar da dukkan kayan shafa kawai ta rage min. Parlon tas se kamshi yake, na wuce parlon Mamaa na gaishe ta sannan na koma daki Ina jiran abinci, banyi minti biyar ba se naji sallamar Aseey, na amsa Mata ta shigo tare da Zama, na dubeta Ina ayyana ya kamata na Dan kula su Haka, kada dai na Bari a koma daidai Kamar da Amma na musu uzuri kamar yadda na Saba wancan lokacin. Na Dan saki fuska muka gaisa tace

" Me Zaki ci?"

Na Dan langwabar da Kai na nace

" Noodles nake so"

Ta mike tace

" Tohm Bari na dafa Miki"

Har ta Isa kofa nace

" Wai Baki tafi ba, shi Abban Ayaan Kika Bari shi kadai"

Ta juyo fuskar ta da murmushi tace

" Wallahi ban ma Yi niyyar hakan ba yace Wai na zauna ko Mamaa zata bukaci Abu"

Na gayda kaina Ina fadin ya kyauta kuwa, daga Haka ta fice ni Kuma na cigaba da zamana. Se a ranar Yan Jahun suka zo, Ina daki can cikin bedroom na ji sallamar Anty Salma, nayi saurin sakkowa a duk Yan uwan Abiey Ina kaunar matar nan har cikin zuciyata, na fito tana tsaye, muna hada idanu da ita sakar min murmushi, na karasa na zauna na gaida ta tace

" Alhamdulillah, ai bana son ganin ki a wani mawuyacin Hali shiyasa naki zuwa wallahi, Amma nagode Allah da Kika murnure"

Na danyi murmushi Ina Wasa da yatsun hannuna tace

" Allah sarki Yaya, ko ya zaiji da Yana da Rai yaga kina da ciki, Kai mutuwa!"

Su Basu san indai zasu ambace shi sosae ba to se nayi kuka, aikuwa na saka ta a gaba nayi ta kuka, gaba daya hankalin ta ya tashi, taji inama batayi maganar ba. Seda nayi shiru na wanke fuskata sannan mukaje can parlon Mamaa na gaida sauran, anan naci abinci sannan na dawo dakina ni da Anty Salma, tana tayi min Hira Bata Kara kuskuren sako sunan shi ba. Da sassafe Ahmad ya dauke ni , tun dare Abba ya fada Masa shi zai maida mu can Dutse, Dan Haka Ina idar da sallar asuba na saka uniform na daura katon hijab a sama sannan na hada sauran kayana, na yaye su bedsheets da waye, nasan Zan Dade ban dawo ba, na kashe komai sannan na fito parlor bayan na rufe bedroom din. Shida na safe ya hayo sama muka sakko har Mamaa da ta rakani, gidan Abba muka tsaya ko Shiga banyi ba Zuhra ta fito da Noorham muka dauki Hanya, tunda muka fara tafiya nake bacci har muka zo dutse Dan Haka hirar ma tsakanin shi da Zuhra ne. Muka Masa godiya ya juya Kano muka fara aiki, Dan da zamu tashi mun ma Gama ganin client dinmu na ranar, matron tace nazo Nima ayimin awo, nace Mata to, ni da ita muka shiga palpation room tayimin, sannan na fada Mata me scan din yace, ta gyada Kai tana Kara min addua, Ina fitowa fuskata da murmushi akai na gan shi zaune suna magana da Zuhra, ya dago idanun shi ya kalle ni na karasa inda suke muka gaisa briefly ya Miko min key yace

" An dawo da ita, Allah ya Kara tsarewa"

Na amsa da Amin Ina Yi Masa godiya ya juya ya tafi, muka tashi anan Naga dukkan gyaran an gyara motar tas an wanke ta Kal, hatta ciki Babu datti, I felt impressed Haka motar shi take fa,duk lokacin da zakaga motar shi to kyalli take saboda shi me tsafta ne. Message nayi Masa na godiya sannan na cigaba da rayuwa ta.

A hankali kwanaki sukai ta shudewa Nima Ina Kara Zama jaruma, kamar bani ba Zan iya Zama nayi labarin Abiey ba tare da nayi kuka ba, Ina ganin hoton shi ba tare da naji wannan kuncin na kamar Zan mutu ba, Amma wasu lokutan Kuma idan na kebe se naji kamar rayuwa batai min adalci ba,se naji komai yayi min tsauri Haka Zan zauna nayi kuka na hakura. A hankali cikin jikina Yana Kara girma Ina kokarin kula da jikina da lafiya ta. Su Anna da kowa suna supporting Dina tareda kawo min ziyara akai akai, Aseey ma da Yaya Ahmad har da Yaya Muhammad sun zo. Ranar wata asabar Ina gida tunda ban fita aiki ba, ranar na tashi naji duniya funkaso nake son naci, Baba Asabe ta kwaba min, Tasnim da tazo hutu tana tayani Yan kananan aiki, na hada miyar da kaina sannan na dawo nayi wanka nasha tea, kawai se hi nayi ana knocking, na aika Tasnim ta bude Amma ta tambaya, Dan nayi wata makwabciya Maman Akram, to ta iya zuwa da sassafe dukda Sha daya har tayi. Na wuce daki na zauna Ina shiryawa, cikina yafi wata takwas Bai karasa Tara ba. Kayan nawa ma da kyar suke shiga ta Dan uniform ma seda na sake dinka wasu. Na saka na yafa veil na fito, duk na Dan kumbura, Tasnim ta shigo tace nazo nayi Baki, na biyo bayan ta kawai se Naga Yayan Abiey ne Suka zo, da murnata na zauna muka gaisa dasu, Yaya Muhammad nata min sannu, nayi murnar zuwan su Kuma Yana daya daga cikin abinda yasa muka shirya dasu. Saboda zuciyata is soft bana Raina kind gesture even the smallest of them. Aseey bayan mun ci abinci mazan sun fita tace min

" Kurkur kike shafawa ne?"

Na girgiza Kai Ina dariya, wanne kurkur ana zaune lafiya nace

" Ko daya Nima Haka Naga Ina wani yellow yellow"

Tace

" Wallahi kinyi kyau Kuma kin fada"

Nace

" Ciwon ciki nake ga kaikayi hannuna da kafata, Zan dai je nayi complain idan na shiga ranar Monday"
Chapter 66 · 0% Book details