← Book details Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 78

Sashe 2

Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na furta da karfi, na nufe shi shi dinne a kwance ya rasu, farin cikin rayuwata, haskena, savior Dina ya rasu. Anty A'isha ta riko ni kowa a gurin na bani hakuri, se kallon tausayina suke dan Anty Aisha ta fada musu kwanan mu uku da aure, to duk sun sani ma, tunda yawanci sun ganeshi, idan ka kalla hannuna lalle ne, jikian kamshi amarci yake, Haka fuskata haibar aure a tattare da ita. Ya rasu! Se asthma Haka aka Jani mutane sun taru kowa na maida yacce akai, aka nebulizing Dina Amma da kyar ta sauka aka min allura Wanda da kyar na tsaya Danni gani nake mafarki nake, gani nake hakan bazai yiwu ba, a lokacin imanina baya kusa Dani. Da kyar Anty Aisha ta zaunar Dani tana lallashina itama hawaye na bin fuskarta. Ya Rabbu wannan wacce irin kaddara ce me zafi ka jarabceni da ita? Nasan baa questioning Allah Amma a lokacin banma San me nake fada ba, nayi nisa da hankalina. Ina nan na fara addua

" Allah Dan Allah kasa na farka a wañnan mummunan mafarkin da nake! Allah Dan girman Allah kasa ba gaske bane"

Funny ko? Yadda nayi adduar na yadda duk Wanda Bai taba wannan adduar ba Bai shiga masifa yadda ya kamata ba.

Love and fighting
Accusing denying
I can't imagine a world with you gone
Drawing and choas, demons we're made up
I feel so lost when you left me alone
Can you hear me screaming please don't leave me
Hold on I still want you
Come back I still need you
Lemme take your hands I'll make it right
I swear to love you all my life!

UNAISA is not free, pay N300 to 3091721807, A'isha kwalam Hassan first Bank of Nigeria and send evidence of payment to 09063467258

[5/11, 5:55 AM] Hauwa Galadima: 🧕 UNAISA 🧕

*B*

✍️ Ayshatuuu

Mijin Anty Aisha yazo, aka Kuma sanar da Governor se gasu an aiko daga fadar shi, aka dauki gawar da taimakon masu zaman jinya harda staff din da securities, sannan aka rike hannuna muka fita, na jingina kaina da headboard din kujera motar Ina jin wani irin abu na bin jikina, I was scared, I was hoping ya tashi yace min April fool! Wasa yake Babu abinda ya sameshi, how I wish a movies ne ace ya shiga cardiac arrest ne! But wannan da gaske ne na rasa shi, shi din ya mutu. Wayar shi Dake hannuna ta fara Kara se Naga " Daughter" nasan Aseey ce hakan yasa na dauka na Kara a kunnena, cikin kuka take fadin

" Unaisa a wani asibitin kuke zamu taho?"

Hawaye ya cigaba da gangaro min nace cikin dashewar murya Dan ta riga da ta Jima da dashewar saboda kuka nace

" Ya rasu!!"

Seda tayi shiru na kusan mintina daya, either she's in shock ko Kuma kokarin digesting abinda na fada take, se kuwa ta saki kuka tana fadin

" That can't be Unaisa! Ki duba carotid artery din shi. He can't die just like that"

Allah sarki ita ta fini sakin layi, Jin bance komai ba se ta Kara sautin kukan Wanda ya Kara dagula min lissafi na jiyo ta tana fadin

" Mamaaa wallahi Abiey ya rasu! Unaisa tace ya rasu. Innanlillahi wa inna ilaihil rajiun!!"

Na kashe wayar Ina Kara sakin kukan rashin sanin halin da nake ciki, rashin sanin madafa. Kafin wani lokaci Kira ya dinga shigowa Amma bazan iya dauka ba, se Kuma Wanda suke da number ta Suka ta Kira na Amma na mutum daya na dauka wato mahaifiya ta

" Unaisa me ya faru da me gidan ki?"

" Ya rasu!"

Na fada Mata a hankali, ban Kuma Jin me tace ba, na rutse idanuna se Kuma ga Kiran Dada, uwata wadda ta kasance tare dani a dukkan halin da nake ciki, na dauka Amma banyi magana ba se sheshekar kuka da nake, hakan yasa ta saki salati tana fadin

" Yallabai da gaske ya rasu, ku Kira zuhra mu tafi"

Anty Aisha ta karbe wayoyin a hannuna, duk Wanda ya Kira se ta dauka ta bada amsa, a wañnan halin muka karaso Kano. Allah yasa nasan gidan shi Haka na kwatanta muka Isa, an taru sosae abinka da Dan siyasa da yake akan mulki. Aka shiga Dani ciki shima Haka gawar tashi. A makeken parlon kasa Mata ne a zazzaune kowanne da carbi a hannunsa, I began to think Ina Suka samu ko dama sunsan zai mutu ne, already Dada da Zuhra da Badi'a har da Yaya khulthum sun karaso, Zuhra na ganina ta mike ta nufo ni ta rungume ni, Haka kukan mu ya tsananta, seda Dada ta janye ni ta rungume ni tana buga bayana a kunnena tana fadin

" Sabr Unaisa"

Na kankame ta inajin kamar zuciyata zatai bindiga Dan abinda nakeji yafi gaban misali. zaunar Dani tayi aka dakko min hijab na yaye mayafin Dake jikina, Allah kadai yasan tururin da zuciayata take. Babu jimawa har an Gama shirya shi, aka shigo dashi akan muyi masa addua, kafata har sarkewa takeyi saboda jiri da nake ji. Na tsugunna gefen shi, ga Mamaa wato First Lady, Asiya, Muhammad da Kuma Ahmad se ni, mune ahalin nashi. Banda kuka Babu abinda nake Yi seda Mamaa ta dubeni tace

" Kiyi Masa addua Unaisa ita yake bukata"

Na kalleta, she sure is a strong woman, na saukar da kaina Kan gawar shi Sannan na fara nema Masa gafara, ina saka ran zai huta a kabarin shi saboda shi din mutumin kirki ne. Muna kallo Haka aka fita dashi zuwa makwanci, na saka kaina cikin hijab kamar Raina zai fita, ban taba sanin Haka zafin ka rasa wani yake ba, ko lokacin da mahaifina ya rasu naji Babu dadi nayi kuka Amma Bai Kai ko kwatan abinda nake ji yanzun ba. Ana Kiran sallar maghrib Anna ta karaso hankali a tashe, suka shigo Muna hada idanu da ita na Kara sakin kuka, ta janyo ni jikinta tana fadin

" Kiyi hakuri! Ki Masa addua"

Seda nayi shiru sannan ta matsa gefen Mamaa suka yiwa juna gaisuwa, Suka gaisa da Asiya sannan Dada da sauran Yan uwan shi Suma, a hakan se kallon banza ake wurga Mata. Se bayan ishai aka sarara, ya rage bamu da yawa. Dada tasa aka kawo Mana abinci, Amma Babu yadda batayi ba naki naci, se kuka kawai nake na rashin madafa da Kuma tausayin kaina. Wannan yasa Mamaa rike hannuna ta fara kuka itama, tunda nazo Naga tana hawaye daga baya se ta daina, she's trying so hard to be strong for us. Asiya ma se ta biye mu, Haka Muhammad da shigowar shi da abokan shi zasu Mana gaisuwa. Dada ta dinga Mana nasiha da matan gurin, Sega wata dattijuwa me Kama dashi tasa mu da fada tana fadin

" Idan bakuyi hakuri ba ya zakuyi? Kowa yaji mutuwar nan Amma kukan ya Isa Haka, ke Hajiya Talatu idan kina kuka Unaisa da Asiya su mutu kenan? Dan Allah kuyi hakuri"

Aka taru ana bamu Baki se kukan ya lafa, Anna ta mike tace zata tafi gobe zata dawo, Dada da Mamaa suka ce basu San magana ba, Dole ta zauna dan a wañnan lokacin Ina bukatar support, Dole Anna ta zauna ga Anty Aisha, se kannena Mata su biyu Nuzla da Hunainah, Dan Dada tace ma Badi'a ta tafi gidan ta tunda Yaya Man yazo tafiya da ita. Acan bangaren muka koma, duka Suka fara Shirin kwanciya Amma Ina zaune saman carpet nayi shiru tare da tsirawa guri daya idanu, Anna ta zauna gefena itada Zuhra ba tareda tace komai ba, wannan Daren guangyadi kawai nayi. Da safe labari ya bazu sosae cikin kawayena da Yan uwan Kai kasar Baki daya, ko Ina ka duba hoton mu ne na ranar daurin aure, Yana sanye da bugaggiyar shadda blue wadda akai riga da Yar ciki, se katuwar babbar riga ta farar shadda, ni Kuma Ina sanye da dandatsetsen lace Blue irin shaddar shi, nayi kyau har na gaji, fuskar mu dauke da madaukakin annuri, Wanda ganin shi kawai se ya saka murmushi, hoton ma iya soft copy ne ya karaso Dan hardcopy Bai zo ba, "he died after three days of wedlock" shi ne caption din.

Tun asuba nake kuka bayan nayi sallah, Anna ta dinga bani Baki da Anty Aisha, yayinda Hunainah da Zuhra ke tayani kukan. Anty A'isha tasa nayi wanka Amma Babu ma kayan da zan saka, se kawai na maida Wanda na cire Dada ta shigo lokacin Ina saka socks a kafata saboda bana son iska a kafar, ta zauna gefena na gaishe ta cikin dasashiyar murya

" Ya hakurin mu? Allah ya jikan honorable"

Ta fada na amsa da Amin Nima na Mata gaisuwa, ta dubi su Anna Suka gaisa sannan aka shigo da abinci, tea ta hada min me kaurin gaske tace na daure nasha, se na fara hawaye Amma yadda take min bazan iya Mata musu ba, Haka na kafa Kai na Sha baifi rabi ba na aje, ba Wanda ya sani se na karasa Suka barni sannan ta kamo hannuna muka dawo can parlon Dan karban gaisuwa. Haka har seda akai kwana uku sannan Anty Aisha ta tafi, Anna da sisters Dina ma Suka tafi tunda Zuhra na nan, Dada Kuma na zuwa. ya rage daga mu se shakikan shi, nawa dangin da kawayena sun min Kara nasha waya kowa na min taaziyya, wasu ma nasan Basu Gama warware gajiyar bikina ba.

Da yamma Ina zaune a daki ni da Zuhra, a Rana na hudu, Asiya na parlor zaune tana waya Mamaa ta fito daga daki tana fadin

" Ku saka hijab zaa shigo"

Nikam dama da hijabina a jikina Dan Haka Asiya kadai ta zura nata, Anty Uwa ta dubeni tace

" Unaisa Banga Hajiya ba?"

Na dube ta nace

" Ai ta tafi tun dare Baku hadu ba?"

Tace

" Ina can Ina magana, Amma ai da ta zauna dake"
Chapter 2 · 0% Book details