← Book details Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 78

Sashe 16

Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na saki hamdala tare da durkusawa nayi sujudus shukr, na fito da murnata Ina fadawa Anna dasu Nuzla, duka Suka rungume ni suna Taya mu murna tare da Mana adduar Allah yasa ta gaba ma mu ci.

Mun koma makaranta an cigaba daga inda aka tsaya, Babu laifi na fara sakin jiki da mutane mussamman Wanda suke zuwa gurin Zuhra, nasan ni din me wuyar sabo ce Amma a Haka Husna ta shiga jikina, bayan Zuhra bani da kamar ta, kusan ko da yaushe tana dakin mu ko Kuma ni Ina nasu, tana da kirki sosae da sosae. Wani safiya Muna daf da zamu fara exams, Dan har an Gama revision , munje karatu ni da Husna da Zuhra min dawo, na kwanta akan gado ko takalmin kafata ban ma cire ba, Zuhra ta Harare ni tace

" Dan Allah ki tashi ki Mana girki"

Cikin sauri na tashi Ina kallon ta nace

" A'a Dan girman Allah Zuhra ki Bari mu huta, daga dawowar mu"

Ta bata fuska tace

" Wallahi Yunwa nake ji Unaisa, just cook ko da noodles ce"

Nayi tsaki Ina Mata gorin acici, ita bata son girki ni Kuma I find pleasure and joy in cooking. Husna na Mana dariya ta Mana sallama ta tafi duk yadda muka ce ta tsaya taci taki Wai ita noodles taci da safe. Cikin kankanin lokaci na Gama dafawa se Kuma muka fahimci bamuda ruwan Sha, na girgiza Kai na dauki kudi da hijab Dan naje shop na siyo Zuhra tace

" A'a ki zauna na siyo"

" A'a Bari naje kawai ki fara ci, yadda kike langwabewar nan ai se ki Fadi"

Tayi dariya ni Kuma na fice bayan na harareta. Na fito na samu wata dalleliyar bakar mota wuluk a wajen Caf din hostel, na kalleta one glance sannan Kuma na wuce na siyo ruwan a shop na dawo Naga me motar ya fito, yana tsaye jikin mota, I wonder yadda zaka tsaya a wañnan ranar Dake burning skin din mutane, ta kwalle har zakai mistaken lokacin da karfe Sha biyu na Rana, a gaskiya Kuma karfe goma ne kawai, ba tareda na kalla inda yake ba na cigaba da sauri Dan na koma kada ta illata min fata ta da nake tunkaho da ita, Ina zuwa gefen shi yace

" Dan Allah!"

Sanin ni kadai ce ke tafiya Se yasa na tsaya na juya na kalleshi, Yana sanye da kananan Kaya, idanun shi sanye da glasses, fuskar shi looks a bit familiar Amma Kuma na kasa fahimtar a Ina na sanshi. Na gaishe shi yayi murmushi yace

" Kema student ce anan ko?"

Na gyada kaina bance komai ba se yace

" Nazo wajen Zuhra Abdullahi, I dunno ko kin santa? Na kirata wayar ta Bata shiga"

Se daya fada sannan na fahimci Kama suke shida Yaya Saif, na saki fuskata nace

" Zan fada Mata, Amma wa zance Mata?"

Yace

" Ahmad Aminu Zaki ce Mata"

Ikon Allah akace ikon gaske, wannan ne karon farko da muka fara haduwa da Ahmad, na juya na nufi hostel, na shiga daki na samu har ta fara ci abinci, na janyo cooler na zuba ganin Bata min magana ba nasan haushi taji na Dade, seda na juye sannan nace

" Someone Ahmad Aminu yazo gurin ki"

Cikin sauri ta aje fork din hannunta kamar zata kware tace

" Ya Ahmad! Yana Ina?"

Na fada Mata inda yake ta dau hijab ta fice, na zauna naci abinci sannan na clearing gurin na koma na kwanta, se bayan da nayi azahar sannan ta shigo, lokacin har bacci ya dauke ni, daden da tayi min yasa na farka a firgice Ina turo Baki, tayi dariya Dan tana yawan cewa Wai idan nayi pouting kyau nake, na zauna Ina mirtsika idanu nace

" What again?"
Na tambaya bayan ta zauna gefena, hannuna ta ja tare da fadin

" Kizo muje ku gaisa"

Nasan ko naki ba zata yadda ba Dole na wanko fuskata muka fita, har ya tada mota da muka karasa, tun da muka taho yake kallon mu Wanda yasa naji haushi a cikin Raina Amma ban nuna ba. Muna karasawa muka gaisa tunda wancan haduwar bamu gaisa ba

" Yaya Ahmad ita ce first daughter sister Dada Dana baka labari, she's Unaisa"

Yayi murmushi yace

" I like your name"

Na Masa godiya sannan yace

" Ga Kaya na kawo Amma nayi tunanin ke daya ce, I'm sorry ana Bina bashin sauran"

Tayi dariya tace

" Babu komai we can share ai, beside baka San da ita ba"

Ya gyada Kai sannan tace

" Nagode Yaya Dan Allah ka gaida Abiey da Mamaa'

" Sure! Shi Yaya Muhammad me yayi?"

Ta Bata fuska tace

" Seriously fushi nake dashi"

Yayi dariya kawai ya Mana sallama seda ya tafi sannan muka koma ciki, sosae shopping yayi, na zauna na jera kayan ta Kira Abba da Dada ta fada musu, Ina jin Dada na Mata fada ta yadda take amsawa, seda ta Gama tace min

" Kin tuna Yaya Muhammad? Brother shi ne, cousin dinmu ne"

Na gyada Kai anan take fada min wai shi ne best cousin dinta ya dawo daga Manchester inda ya Gama medicine. A hankali ranaku suka shude muka fara exams, ranar mun fito a PHC Ina dawowa na tarar da jerin Calls da nayi missing, number da ta yimin Kira har uku ta dauki hankalina, na Danna dial Amma tana fara ringing aka katse Sega kiran ya shigo, na duba na dauka muryar shi na dokar kunnena nace

" Yaya Ahmad! Ina kwana?"

" Lafiya Lau Unaisa, ya makaranta"

" Alhamdulillah"

Na bashi amsa, muka gaisa sannan yace

" Ina son zuwa na dauke ku idan kun Gama exams jibi, I hope Babu matsala"

Na danyi Jim nace

" I'll talk to Zuhra about..."

Ya katse ni da sauri yace

" Nop! That should be a surprise to her!"

Nayi dariya Dan idan har wani mahaluki na tunanin I can hide something from Zuhra yayi kuskure,

" Me yasa kike dariya? I'm not welcome?"

Kafin na bashi amsa Sega Zuhra ta shigo da murnarta, alamar exams tayi Mata Dadi, ganin Ina kallon ta ta karaso ta warce wayar tana fadin

" Waye Kika samu? Allah yasa wani ne ya sace min zuciyar ki"

Na fara dariya ganin yayi disconnecting kiran, na zauna nace

" So kike a raba ni da zuciyata nufin ki? A hanani sukuni irin naki?"

Tayi dariya ta zauna tana jujjuya wayar tace

" I want you to taste love, Ina son kiji menene soyayya? Ina son ki fada kiji yadda akeji"

Na tabe baki nace

" That your cousin called.."

" Yaya Ahmad? Ko dai"

" Dallah! Yace Wai zai zo daukar mu ne"

Ta Bata fuska tace

" Shi ya sani, na zata zaice Yana sonki ne"

Nayi dariya Ina Mata kallon batada Kai sannan na tambayar ta abinda zamu ci, ita ta dafa Mana. cikin kwanaki biyu muka kammalla exams, da wurwuri yazo kamar yadda yayi Mana alkawari, ya saka Mana kadan daga cikin kayan da zamu koma dasu gida. Ni ce a baya idanuna akan wayata yayinda suke gaba suna Hira, dukkan kokarin da yake na ganin ya saka ni a cikin hirar tasu naki, bansan me yasa naki sakin jikina dashi ba, se ya kyaleni bayan Zuhra tace ya rabu Dani I'm not the surutu type. Mun bar Ringim a bada Kiran Dada ya shigo wayata dake hannun Zuhra Ina nuna Mata wani thread a Tweeter se babbaka dariya take,

" Dada Ina wuni? Mun taho?"

Ta amsa min sannan tace min dukka su Anna na gidan ta Dan Haka mu zarto can. Na fadawa Zuhra ta dinga murna, kafin mu karsa gida se da ya tsaya a havilla ya karba mana ice cream da cake sannan muka karasa gida. Tun a gate na barsu tsaye Bayan na Masa godiya, Yana murmushi yace

" Yaushe zaku koma?"

Nace

" Nan da 13 days"

Ya gyada Kai se Zuhra ta Masa tayin ya shiga su gaisa dasu Dada, se yace Mata

" Da nace tafiya zanyi ban gaisa da Dada ba, Aseey fa ta dawo"

" Munyi waya!"

Ya Bata Rai ya shige gaba muka bishi a baya, suna sama Dan Haka muma saman muka wuce, Nuzla ce kana shiga zaka fara cin Karo da ita tana cin abinci, tana jin sallamar mu ta aje plate din tayo kanmu, tuni Suka hade gidan da ihu itada Zuhra, naja gefe Ina murmushi tareda kallon su gwanin shaawa, I dunno me yasa ni bana sahun yin hakan, nutsuwata tayi yawa, ni din inada sanyi bana ma cikin hayaniya . Na kalli Yaya Ahmad da ya harde hannayen shi a kirji Yana ma Nuzla wani irin intense kallo, ita Kuma Ina kyautata tunanin Bata masan da zuwan shi ba, ganin kallon is deep yasa na bubbuge su day fadin

" Wannan ya bar murna ya koma hauka Kuma"

Ta saki Zuhra ta zumbura Baki cikeda shagwaba tace

" Ko murnar ganina bakiyi"

Na riko hannunta Ina fadin

" Yaya Ahmad my immediate Firdaus"

Nayi hakan dan ta gane bamu kadai bane, aikuwa take ta shiga taitayin ta ta fara Jan rigar ta, ya Dan matso Suka gaisa, ta wuce simsim ciki Ina kallon yadda ya bita da idanu. Tare muka shiga ciki na fada jikin Dada a hankali ta buga bayana tana fadin

" Yan makaranta, sannunku da zuwa!"

Muka gaisa, na gaida Anna dake kallon mu admiringly ta Mana sannu da zuwa, Dada ta dubi Ahmad tace

" Likita bokan turai! Sannu da kokari"

Ya shafa kanshi yace

" Kai Dada, Bari na wuce"

Ta gyada Kai tace

" Ka gaida Hajiya Talatu"

Yace

" Mamaaa zata ji"

Daga Haka ya fice bayan ya ma Anna sallama, ni Kuma da Zuhra muka Kara Masa godiya. Dada ta dubemu tace

" Ubanwa yace ku Kira shi kuce yaje ya dakko ku?"
Chapter 16 · 0% Book details