← Book details Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 78

Sashe 34

Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Kayi hakuri, nasan ban fada ba kawai zakace zaka zo shiyasa"

Ya danyi dariya yace

" Dadi na dake kina da amsar laifin ki, to duk da hakan gani a kofar unit din"

Na zaro idanuna nace

" Dan Allah! Wayyo Yaya Ahmad sannu da hanya"

Yayi murmushi yace

" Da Ina da kudi Zan aureki ko dan na dinga ganin shagwabar ki"

Na turo bakina nace

" Zaka fara ko? Bari yanzun zamu taho munje muyi wanka ni da Nuzla"

Se yace

" Me Zan fara? Wasa nake ai kinsan nace Miki ke ba matar yaro bace, se Wanda ya tara ya tada kai. Ki tsaya zanzo na dakko ku"

Se na fada Masa plaza baayi mintina biyar ba se gashi gaban plaza, na bude gaban motar na zauna, Nuzla ta koma baya ta zauna Ina ganin ana exchanging glances na dauke kaina, bayan sun gaisa da ita sannan ni muka gaisa, ya tambaye ni yadda muke da me jiki nace Masa alhamdulillah, sannan ya dauki hanya zuwa asibitin munata Hira ko nace musu, shima mun Saba dashi sosae ba me se na Kara fada muku ba Kun sani. Tare muka shiga ciki dashi, Baba Fiddau ta hada tea me uban kauri tana Sha, Nuzla ta tabe baki tace

" Banza ta Fadi"

Na Harare ta, tayi dariya ta wuce gaba,

" Alhaji yazo ya gaida jikin ka, sunan shi Yaya Ahmad"

Ya Mika Masa hannu na zata ko.zaiju tsatsani Amma se Naga akasin hakan , ya Mika Masa sukai musabaha suka gaisa ya Masa godiya da saka Masa albarka akan ziyartar shi da yayi, daga nan Bai se sukai Dan taba Hira Baba Fiddau na tsoma Baki. Bai Jima ba ya mike ya Masa sallama tare da  aje Masa kudi, nayi saurin girgiza Kai na dauki kudin nace

" Dan Allah Yaya Ahmad ka barshi, zuwan da kayi ma is very ok, Kuma I truly appreciate"

Ya kalleni ya kalla kudin yace

" Baba waye Mai maida hannun kyauta baya"

Alhaji ya kalleni Yana murmushi yace

" Shaidan ne, Unaisa karba"

Na Dan buga kafata nace

" Kai Dan Allah Alhaji"

Na kalli Ahmad nace

" Nagode Allah ya saka da alkhairi, Nuzla"

Da ta jiyo se na Mika Mata kudin, ta kalla ta Masa godiya sannan muka fita Dan na raka shi, seda ya shiga mota sannan yace

" Aseey tace min wai kinyi wani saurayi kina son shi sosae!"

Na gyada Masa Kai Ina murmushi, yayi murmushi yace

" An kada ni kenan! Anyways Zaki bani Nuzla to?"

Na Dan kankance idanuna nace

" Like for real?"

Yace

" Duk Yan matan da nake ce Miki nayi kinyi tunanin I was serious? Ba Haka ba Ina tunanin yadda zance ki bani Nuzla ne"

Nayi murmushi nace

" Amma kasan she's not easy going ko?"

Yace

" Haka nake so, in har I can get your support!"

Nace Masa zanyi tunani sannan na Kara Masa godiya ya dauka hanya, ban koma ciki ba se kawai naje na samu karkashin bishiya na zauna, my greatest fear shi ne nayi late marriage, ina Jin tsoron ita ma Nuzla tayi aure ta barni jangwabe a gida, Amma Kuma hakan ba zai saka naki bawa Nuzla damar kula Ahmad ba tunda kuwan Ahmad ai mutumina ne nasan halayen shi Wanda yayi displaying, wayata ta katse min tunani Ina dagawa Naga Cànîm ke Kira na dauka muka gaisa ya tambaye ni jikin Alhaji nace masa jiki da sauki se yace to zai kirani anjima, Bai ma jira amsar da Zan bashi ba se ya kashe, kwana biyu kawai Ina jin something smells fishy tare da shi, like idan Muna waya ba kamar ko yaushe ba kullum Rana he sounds not energetic Kuma se Yana barina ni Zan ta surutu Ina ganin instinct Dina na fada min tabbas akwai abinda yake faruwa da Bai son maganar shi Kuma Yana boye min. Na dawo cikin dakin Ina kallon Nuzla da suke tafka musu itada Baba Fiddau, na zauna ganin Alhaji yayi bacci nace

" Ina son magana dake"

Ta mike ta biyo bayana, Baba Fiddau tace

" Ni Unaisa waccan da yazo ko shi ne Wanda Zaki aura?"

Nuzla tace

" Bashi bane! Ina ruwan ki"

Ta ja hannuna muka fita, Ina dariya nace

" Be going easy on her, Dan Allah matar nan ki dinga Mata mutunci"

Bayan ta zauna tace

" Ke wallahi Adda Ina fada Miki bazan iya ba, ni fa ko Adda na tsane ta wallahi bana sonta, saboda sun dinnan basuda kirki ko kadan, ai Haka Allah yake mu da aka wulakanta, aka Mana rashin mutunci gashi mu dinne dai ke amfani"

Na Yi murmushi nace

" Ba wannan ba, kinada saurayi"

Ta min wani kallo tace.

" Ban gane wani saurayi ba? Bani da shi, me ya faru?"

Nace

" Ahmad yace Wai Yana sonki..."

Ta kwalalo idanu tace

" Wanne Ahmad? Wai Ahmad din ki? Brother Yaya Aseey?"

Nace Mata eh, tayi dariya tace

" Lallai Adda, to mu Kuma a dangin su zamu Kare? Ta Yaya sun auri Badi'a su ce zasu aureni, a'a ban yadda ba"

Na gyada Mata Kai bance komai ba se naji muryar Baba Fiddau tana kwalla min Kira,kafin na juyo nace

" Innanlillahi wa inna ilaihil rajiun!"

Na juya a hankali saboda yadda gaba na ke ta faduwa nace

" Me ya faru? Baba?"

Tace

" Kizo Yahai lokaci yayi, Yahai ya rasu!"

Kaina yayi wani irin sarawa, kaina ya buga se echo kawai na dinga ji na abinda aka fada, na karaso ciki na samu har an rufe shi da farin spread, na karasa na Dan bude fuskar shi, Alhaji ya rasu lokaci yayi! Baba Fiddau se kuka take Amma dukka mu biyun Babu abinda ya zubo daga idanun mu, sede har jikina Ina jin abin, Ina jin wani yanayi marar Dadi, kasancewar kwana biyu munyi sabo dashi Dan zaman da mukai dasu. Wayata na Ciro bansan ma Ahmad na Kira ba, kasancewar shi last person Dana kira, Yana dauka nace

" Anna Alhaji ya rasu!"

Ahmad yace

" Wai Baban naku?ya rasu"

Se lokacin na fahimci Ashe shi na Kira, na saki ajiyar zuciya nace Masa uhm, se yace na zauna baiyi nisa ba Dan dutse yaje gidan Zuhra Kuma Yana hanyar dawowa gurin mu. Na kashe wayar nayi hanyar fita waje nurses din suka Kira ni Suka zaunar Dani suna bamu Baki, se nace musu

" Dama Haka rayuwar take, kowa Dan Haka ne, min gode for all your services, I'm very grateful!"

Daga Haka na fita zuwa kofar unit na zauna Ina jin kamar na rufe Baba Fiddau da dukan kukan da take, ta Tara jamaa se ihu take ni kuwa takaici ya Hana nace komai. Nuzla ta zauna tana cemin

" Adda ya zamuyi?"

Nace

" Ahmad zai dawo ya dauke mu, Bari na Kira Dada da Anna, ki Kira Baffa da Abba please!"

Wayata na duba azahar ce kawai, na mike na Kira Anna har sau uku Bata dauka ba, na Kira Dada itama Bata dauka ba se kawai na Kira Badi'a, ta dauka tana fadin

" Adda ya jikin Allaji!"

Nace

" Badi'a ya rasu, I'm sorry"

Tace

" Innanlillahi! Allah ya jikan shi Kuna Ina?"

Nace

" Zamu tafi Masaya yanzun, se kin karaso"

Daga Haka na kashe wayar naje nayi sallah, Ina idarwa Sega Ahmad ya karaso, su suka dauki gawar sannan muka tafi Masaya, kukan da Baba Fiddau keyi ya Bata min Rai nace

" Dan Allah ki Mana shiru, Dan Allah da me kike so Muji?!"

Se tayi shiru tana matsar kwalla, Amma Kuma Babu hawayen, Muna zuwa Masaya na tuna ban fada ma Al'amin ba, na fito da wayata na tura Masa short message, Muna Isa aka fara Shirin janaiza da komai, Ina daki Ina zaune nayi shiru Ina ayyana idan da ace Anna ce ta rasu kilan mutuwa zanyi, ko jinina ya hau na samu paralyse, wayata ta fara ringing nayi saurin sata a silent sannan na dauka

" Babes message din ki na gani?"

Nace

" Uhm! Har mun dawo Masaya ma"

Yace

" I'll be coming, Allah ya jikan shi Babes Allah ya Masa rahma!"

Kawai se na fara kuka a hankali, ya kashe wayar na kifa kaina cikin cinyata Ina kuka marar sauri.

Al'amin

Kwana biyunnan abubuwan suna Dan yawa, matsawar da Mummy keyi ta fara yawa, kamar yadda tace Masa zata saka ayi bincike shi dai Bai sani ba ko anyi kawai dai ta kirashi daki tace Masa ya rabu Dani. Amma se baice Mata komai ba, yanzun da yayi receiving message Dina ya shigo hankalin shi a tashe, ya shiga yayi wanka sannan ya fito zuwa dakin Mummy tana zaune sanye da eye glasses tana karatu cikin tab, ya zauna yace

" Mummy baban Unaisa Allah yayi Masa rasuwa"

Tayi saurin dagowa tare da zare glasses din ta tace

" Ya Rabbu Allah ya Masa rahma, can zaka je?"

Yace

" Eh!"

Tace

" Bazan hanaka ba tunda abin samun Lada ne, Allah ya kiyaye Hanya ka Mata gaisuwa"

Daga Haka ya fito ya dauki Hanya se Masaya, kafin wani lokaci har sun Anna sun karaso, su Dada dasu Badi'a, Haka Yan hadejia a takaice anyi Mana Kara anzo suturar shi, akai Masa wanka aka kaisa makwanci se a lokacin Al'amin ya shigo ya Mana gaisuwa ya tafi Dan na mike na raka shi Anna ta girgiza min Kai, Ahmad ma dasu Yaya Man sunzo tafiya Suka shigo Ahmad ya kyauta, akalla da nasan Abiey mahaifin su ne bazan fara son shi a farko ba, saboda su din sunyi min mutunci ba kadan ba, gaba dayan su mutane ne masu karamci gare no, to Amma ya kamata na fara Baku labarin abinda ya raba ni da Al'amin kafin nazo Kan Baku labarin Hafiz, se Kuma Abiey ya Zama na karshe!

Unaisa is not free pay N300 to 3091721807 A'isha kwalam Hassan first Bank of Nigeria and send evidence of payment to 09063467258.

[5/31, 7:24 AM] Hauwa Galadima: *D_D*
Chapter 34 · 0% Book details