← Book details Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 78

Sashe 50

Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yayi dariya Yana fadin

" I'm sorry Baby, just sleep zanzo na Miki lulaby"

Tabdi Ina ma Abiey yasan wani lulaby,  na kashe wayar, sosae nake jin bacci na lumshe idanuna Ina jin Murmushin shi na mini amsa kuwwa cikin kunne na, he's lovely. Nuzla ta shigo tana fadin

" Kinzo kin kwanta ko Hira ba Zaki Bari muyi ba"

Na gyara kwanciya ta nace

" Muyi hira,"

Ta fara bani labari abubuwan da suka faru da ba nan, banma maida hankalina ba saboda bacci Dake fuzgata, se taji ma na daina amsa Mata hakan ya tabbatar Mata da gaske nayi bacci. Kamar yadda yayi alkawari da asuba ya tashe ni, akwai wani sirri da idan kayi magana da mutum na karshe to tabbas kana tashi that person will cross your mind, he always make sure shi ne karshen Yi min magana kafin nayi bacci sannan Kuma shi ke  fara min magana da safe, so se ya zamana ya Shiga rayuwa ta da yawa. A wañnan kwankain bakwai da nayi kowa yasan nayi sabon saurayi dukda ban fada ma kowa maganar shi ba Amma dai kowa ya zuba min idanu. Ko Zuhra da tazo ma seda tayi maganar tace

" Hajiya kinyi saurayi ne?"

Na kalle ta nace

" Me Kika gani? Gani kike har hanji"

Tace

" Ina time din da kuke tare da Al'amin, to wallahi irin Murmushin kike"

Na rufe fuskata nace

" Ba wani nan, kawai I'm happy ne"

Tayi murmushi tana kallon yadda Noorham ta lafe a jikina tana Ommaah ta! Ni Kuma nayi cuddling dinta a kirjina tace

" You should be happy, kada ki bar kowa ya dauke Miki wannan farin cikin. Babban rabo Yana tafe!"

Se dare suka tafi bayan na huce gajiya na tattara tsarabar Yan hadejia na tafi Dan reporting zuwa wajen aiki.

" Anjima karfe nawa Zaki tafi? Should I send my securities su tafi dake?"

Nayi saurin girgiza Kai Ina zare idanu nace

" A'a ni dai Zan iya zuwa ni kadai fa"

" Komai nace see kice a'a. Na Dan Baki lokaci kiyi settling ne kafin na proceeding maganar auren, by the way Ina kike son Zama?"

Na danyi shiru Ina tunani se na tuna Yar uwata Dake dutse ita dakai, na tabbatar zata so mu zama mu biyu, Haka Kuma ko so nake na zauna a China to tabbas zai iya kaini, nace

" Dutse nake so, is that ok by you?"

Yace

" Of course ko Ina kike so, I'll transfer you daga hadejia se muyi zamna mu a dutse ko?"

Nace

" Eh"

Yace

" Inada gida cikin fatara estate, na Kuma saya fili a hybrid, wanne kike so?"

Nace

" Hybrid"

" Done Baby! Idan architect din ya Zama ready, se ki Masa bayanin yadda kike son plan din!"

Oh Allah Wai nice ake bawa zabi, min Jima muna maganar abinda nake so se can nace Masa

" I love flowers, plantation ma kawai, Ina son colors dinsu da fragrance dinsu, they're cool"

Yace

" I'm jealous!"

Nayi dariya sosae yace

" Ya Kanata na shuka su a jikina, so that I'll attract you!"

Na koma hadejia cikin aminci, idan akwai farin ciki a duniya da bashi da iyaka to soyayya ce, na yadda ita din ZUMA ce me zakin gaske wadda Kuma zata iya dallar ka yadda zakaji Babu wani zugi da radadi irin nata. Duk Wanda yake ganin soyayya ba komai bace to ya tabbata baiyi ba, Wanda yake ganin ta ya zanyi wannan abin to ba soyayya yake ba, it makes the impossible possible, idan ba Haka ba ta Yaya Abiey ya iya flirting Haka, he's so romantic and sweet to be. Ina ma dai ace na dawamma tare da shi, inama ace Bai mutu ya barni ba Amma Allah Bai nufa ba, ba Haka Allah ya tsara ba!

Unaisa is not free, pay N300 to 3091721807 A'isha kwalam Hassan first Bank of Nigeria and send evidence of payment to 09063467258

[6/16, 10:03 PM] Hauwa Galadima: *Q_Q*

Exactly wata daya da komawa ta hadejia Abiey ya riga ya zama bangare na jikina ya Zama wani jigo na cikin rayuwata, shi din ya Zama bango da nake jingina. Har lokacin ba Wanda na fadawa ko da Zuhra ma ban fada Mata ba, tsoro nakeji irin tsoron da Fatima wato Nanah taji lokacin da ta hadu da Abba Prof, lokacin da take son gabatar dashi ga Daddy Amma se ta kasa saboda tana Jin tsoro, Amma dukda Haka ta aureshi.  Ranar laraba ana gobe Zan koma kano, Ina zaune na Gama yanke farce na, Ina taje kaina da jiya nayi steaming din shi tunani nake ko kawai na Kira Zuhra na fada mata, ko kawai na fadawa Abba Kai tsaye se kawia na Kira Zuhra, Bayan mun gaisa na tambayi Azizaty Noorham nace

" Ina son fada Miki Abu ne"

Tace

" Kinyi niyya kenan? Ina jinki"

Nace

" Wallahi se na fasa"

Maimakon ta roke ni se cewa tayi

" Oho Miki dai, duk abinki ni daya kawai kike da, Dan Haka ki Gama tsilla tsillar ki ni din dai nice"

Na Bata Rai nace

" Lallai ma ji kike kamar bazan iya Babu ke ba ko?"

Tace

" A gwada Mana"

Nayi tsaki kawai, na fara fada Mata a hankali yadda abubuwan Suka faru, tundaga haduwar mu da komai da komai har zuwa yanzun, har sunan shi na fada Mata Amma bansan yadda akai Bata gane uncle dinta bane, ko Dan Allah Bai nufa ba

" Zuhra wallahi bansan ya zanyi ba da gaske"

Tayi murmushi tace

" Idan nace ki rabu dashi saboda shekaran shi Zaki iya?"

Nace

" A'a Ina son shi gaskiya!"

Tace

" To tsoron me kike? Idan har yadda nake ganin farin ciki a tare dake nasan tabbas Allah ya amsa adduar mu, inaga lokaci yayi, lokacin da muke jira ne ya karaso"

Nace

" Zuhra babba ne"

Tayi dariya tace

" Full package kenan, karki damu ba kina son shi ba, indai Abba yayi bincike know that na Miki alkawarin Zaki aure shi I'll convince kowa da kowa! Amerya"

Nace

" Ke kinada matsala"

Tayi dariya tana ta tsokana ta sannan ta karfafa min gwiwa ta. Se naji Dadi da sanyi a raina. Bayna munyi sallama se ga wani Kiran ya shigo, wayata Apple ce so kawai gani na yi an rubuta " Nag or Cànîm"

Gabana ya fadi, nasan lokacin can da muka hadu dashi Nag na fara saving number din shi dashi, Haka daga baya na maida Cànîm, shi kadai na taba Kira da hakan ban taba fadawa wani wannan sunan ba. Na kifar da wayar, na mike se na dawo na kalla screen din sannan na mike na fice daga dakin, bayan shekaru se yau ya tuna Dani? Ko dai ya ganni a airport ranar? Na girgiza Kai ba yadda zaayi Al'amin din da na sani ya ganni ya share ba zai yiwi ba. Banma Yi niyyar daura dinner a wañnan lokacin ba Amma kawai na samu kaina da daurawa, dukda Kar na koma ya Kira na dauka, ni dashi ta Kare hakane kamar yadda baban shi yace gwara na rabu dashi naji zafi Akan na aureshi maman shi Bata Sona, hakan zaiyi wahala zanji Babu dadi cikin zuciyata, auren Zia fita akaina gaba daya duk kuwa soyayyar da muke ma juna. Se bayan maghrib sannan na dawo daki ni da Maryam Dake faman ce min sub dinta ya Kare, na dauki wayata na Mata vtu sannan ta barnj na tsugunna. Na dauki wayar King me hoton zuciya, da mukulli padlock, da kibiya ta caki zuciya shima ya Kira "King❤️🔐💘" Haka nayi saving number din shi, Babu Wanda na taba kulkewa se Kan shi, shi kadai Kuma ko ba komai dai na aure shi, hannuna na rawa na Kira shi, nasan har korafin ban Kira nace Masa na dawo daga aiki ba se yayi, nasan halin kayana. Bai dauka ba se ya kirani

" Yau anyi dogon shift ne ko kuwa bawan Allah aka manta ?"

Na marairaice nace

" Banida lafiya fa!"

Yace cikin wata irin murya

" Me ya faru? Me ya same ki? Attack dinne?"

Ba karya nake ba, dazun a asibiti da safe na danyi tari kadan saboda Kona incinerator da akai ni Kuma na fita Babu mask zuwa amenity karbar awara, da na Dan Shaka inhaler se ya tafi.

" Mild attack ne Kuma ya tafi'

Cikin damuwa yace

" Baki taking precautions din Dana fada Miki ko? Why is this asthma doing this. To ya kike ji yanzun?"

Na fara fada Masa ai Dana dawo mahar steaming kaina nayi, nayi girki, nayi manicure and pedicure, anjima Zan saka lallae Zan danyi spa a jikina. Yayi murmushi yace

" Duk ayau din, wannan gashi da jiki suna Shan gyara Ina ma ni ake bawa quarter attention din da ake basu"

Nace

" Kenan bana kula da Kai ko?"

Yace

" Ni bance ba, ni ban fada ba"

Nace

" Shi kenan se anjima'

Yayi dariya yace

" Nasan ba fushi kikai ba Kiran sallar Isha ake, pray let's talk before you sleep"

Nayi murmushi gwanin ban shaawa na Masa sallama sannan nayi sallah naci abinci, na dawo na kunna data Dan chatting tare da fara kokarin karbar order kayan sanyi Dan kuwa sanyi na tafe. Ina Gama refreshing se ga message din Al'amin

" Babes!"

Na bude na kurawa Babes din, na tuna lokacin da nake dokantuwa da hakan, na tuna yadda ko wani naji ancewa Babes se fuskata ta haska, Amma dukda Haka yanzun ma seda naji wani iri cikin zuciyata.

" I called earlier I guessed Baki kusa, ya kike? Ina fata kina cikin farin ciki, howwa u?"

Wannan farin cikin da ya ambata se naji haushin shi nake ji, hakan yasa nayi replying din shi

" Of course I'm happy, Dan ka manta dani, Dan ka daina kula ni bazan mutu ba, Kuma I'll find happiness anywhere wallahi"

Seda na tura na Kara typing

" See I've found my love ka gane"

Ya Dan turo min da emoji na dariya yace

" I'm sorry, I'm happy you're happy I guess bani da matsugunni anan. Amma Dan Allah here my story out"

Nace
Chapter 50 · 0% Book details