← Book details Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 78

Sashe 40

Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta Dan juyo ta kalleni, dama tunda na shigo idanun ta a Kaina, ta sakar min murmushi tace

" Adda ya zaman? Naga ai kin danyi kiba ma, alhamdulillah"

Na saki murmushi Wanda a kwanakin baya nayi tunanin bazan Kara yin makaman cin shi ba, nace

" Alhamdulillah, ba matsala!"

Tace

" Kin fara awo?"

Na Dan sunkuyar da kaina na gyada Kai tace

" To Allah ya albarkaci abinda ke ciki, Ina fatan Babu wani abun dai? Ina son kiji Dadi kullum Dake nake kwana nake tashi"

Hawaye Suka fara sakko min nace

" Ina jin Babu dadi Anna, Ina jin kaddarar tayi min tsauri Anna! Anna na kasa sabawa, kullum Ina jin mutuwar shi sabuwar, ji nake kamar .."

Se nayi shiru Ina sheshekar kuka, ta taso ta zauna gefena ta hada ni da jikin ta tana shafa bayana, I can sense raunin da yazo Mata danma dai she's strong woman.

" Na sani Unaisa, dama Babu Wanda yace ki manta dashi, kowanne Jin Dadi Kika shiga ba Zaki manta dashi ba Amma Ina son kiyi hakuri, Allah Yana sane dake, shi yasan komai Kuma ki daina cewa kaddarar tayi tsauri, Haka Allah ya shirya Miki, a kwanakin karshen shi Zaki zauna dashi. Se ki kalla ki tuna irin gwagwarmayar da aka Sha kafin ayi aurennan, Amma seda akai saboda rabo ya rantse. Kiyi hakuri nasan Babu dadi da ciwo Amma ki daure ladan ki Yana gurin Allah"

Dake na kwana biyu banyi kukan ba yau din se na Jima inayi, seda ta tabbatar nayi shiru sannan tasa na wanke fuskata, suka fara Shirin tafiya harda Nuzla da zata koma makaranta, shima nayi ta kuka da zasu tafi, Anna da Badi'a me kawai basuyi kuka ba, Haka na dawo Ina jina so empty, so depressed, Ina jin kamar duniya ban shigo a saa ba, Amma se na tuna nasihar Anna se na Yi alwala na dakko kurani na fara karatu and I found peace. Lokacin da ya Shiga wata na hudu shi ne daidai fitar Mamaa daga takaba Dan Haka ranar jumaa Ina tashi daga aiki na dawo gida nayi wanka, na saka wata boubou ta wani material Ash me duhu, dake texture din shi me tsantsi ne se ta kwanta tana Kara fidda cikin jikina, yanzun Haka na fara jin motsi sosae, idan naci abinci tamkar filin kwallo Haka ciki na ke komawa, Amma nakan ji dadin hakan Perks of motherhood, idan banci ba se ya dunkule guri guda. Shiyasa bana Wasa da abinci, wannan abin Dake cikina hi nake kamar na bashi Raina tun kafin na rike. Kallon agogo nayi Bayan na Gama shirya karamin akwatin da na saka dukkan abinda Zan bukata a ciki, na dakko Dan karamin hijab da Bai Gama sakkowa kirjina ba na saka color Ash me haske, ya dage saboda parking din gashina, na dakko veil na yafa shi Kuma Ash me duhu color rigar jikina,Wanda na samu ya rufe bump dina, na dauki handbag dita na zuba komai sannan na fito, Baba Asabe ta karba ta fita dashi, Dan motar na waje ma ban shigo da ita ba. Kitchen na Shiga na kashe komai na nado shish tauk din da nayi na dakko lemi me sanyi. Seda na rufe ko Ina sannan nace ma Baba Asabe Zan leka Anty A'isha Kar tazo taji shiru. Tana zaune parlor har megidan na sameta, na Dan tsaya daga waje tace

" Anty Unaisa shi go mana,"

Ba karamin mutuncin su nake gani ba, lokaci zuwa lokaci zasuyi cefane su kawo min wai nayi amfani dashi, dukda ban nema komai na rasa ba Amma hakan ba karamin faranta min yake ba, na shiga fuskata da faraa Ammar Dake cin abinci ya taho da gudu Yana yarda spoon din hannun shi ya rungume ni, Nima na rungume shi Ina fadin

" Bayan ma baa zo an gaishe ni ba"

Yayi murmushi yace

" To munje anguwa da Papa fa!"

Na gyada kai na karasa na gaida su, seda ya tambaye ni Babu matsala sannan ya Shiga ciki, Anty A'isha tace

" Se Ina ?"

Nace

" Kano zanje, gobe Mamaa ke fita daga takaba"

Anty A'isha ta Kama Baki tace

" Kai lokaci na gudu wallahi, Kinga har wannan kwankain sun shude? Ubangiji Allah ya Masa rahma, ya Baki hakuri da Kuma lafiya!"

Na amsa da Amin sannan na mike tace

" Amma ba har kanon zakije ba ke kadai?"

Nayi saurin rufe Baki nace

" Ni kaza! Gidan Zuhra Zan aje motar se mu wuce Trae da su"

Tace

" Yanzun naji magana. Anty Unaisa Allah ya kiyaye ki gaida kowa da kowa, se munyi waya"

Na amsa ta sannan na fito, na saka belt Dan kaidar honorable kenan, yace you must wear a seatbelt while driving, if not your safety is not guaranteed. Na danyi murmushi Ina tuna zuwa hadejia da yayi, ranar zuwan ba zata yayi min, shi kadai a mota ko security Babu Kai ko driver Bai taho dashi ba, hasalima shigar kananan Kaya yayi ya saka nose mask da farin glasses din shi na kullum, na Kara karfin idanu, ya shigo motar haya ya taho hadejia, ta Ina Zan manta wannan kaunar, ta Ina Zan manta soyayyar daya gwada min, ya kaunace ni kamar me yayi fito na fito da dukkan wani me son raba mu, Allah kenan se mutuwa ta yanke Jin dadin! Tun Ina gurin aiki Anty Yusra ta kirani tace min nayi sauri na dawo gida nayi Baki, nayi ta tunanin su waye tunda shi Bai fada min ba, har na shiga mota na tayar na mnata ban fada Masa ba, na dauki wayata nayi dialing number din dhi,

" Beautiful!"

" King! Baka kirani ba"

Na fada a shagwabe, yayi murmushi me sanyaya min zuciya yace.

" Baki koma gida ba har yanzun!"

Na Dan turo Baki nace

" Ni nayi fushi ma tunda topic din kake canjawa"

Ya marairaice fuska har seda taikar jikina ta tashi yace

" Ayya Mana Beautiful, ni din?"

Nace

" Eh!"

Se yayi dariya yace min na karaso gida se na Kira shi, na kashe wayar na fara tuki cikin nutsuwa, Ina parking Bayan an bude min gate naga tamkar shi tsugunne a gaban kofar da zata kaika parlon Baffa, na kashe motar Ina tantamar idan shi dinne nayi saurin fitowa Ina fadin

" King!"

Ya dago da wannan fuskar ta shi me cikeda haiba, kwarjini da ilhama, Murmushin da yake yasa bakin shi yayi curving kadan, he looks cute.

" Beautiful! Kin dawo"

Bakina yaki rufuwa kamar zai yage saboda murna nace

" Baka fadamin zaka zo ba, yaushe kazo?"

Ya Dan Tako daf Dani yace

" I missed you na Kira Abban ki nace Ina son zuwa na ganki, se ya tausaya min yace zai ma Baffa magana, shi ne nazo Naga wannan dimples din"

Ya fada Yana min murmushi, na Kara bude Baki Ina jin asalin farin ciki na shigata Wanda rabon da kalmar baki tasa ni irin shi tun Al'amin, na kawar dashi daga tunani na na Masa jagora ciki, ya zauna na kalla center table da aka cika da kayan motsa Baki kamar ansan da zuwan shi, Babu abinda ya taba a ciki, na dube shi nace

" Baka ci komai ba"

Yace

" Jeki cire uniform ki dawo, kafinnan na Dan taba ko?"

Na gyada Kai with lots of excitement nayi ciki, da hanzari na fada ma Anty Yusra na dawo, tayi ta tsokana ta naje nayi wanka a gaggauce na dakko wani sabon atamfa gown me kyau Tasha stonning, se daukar idanu take na saka na daura dankwali, na kawo Jewelry na saka, nayi kyau sosae. Na same shi ya Dan tsakuri kadan na zauna....

Traffic ta tsayar damu se na dawo daga tuannin da nake tundaga nesa me bike din ya taho, seda yazo gaf damu ya lura an tsayar, yayi koajrin cin brake Amma saboda gudun da yake se ya kasa tsayawa har ya bugar min mirror sannan ya zube shi da machine din. Nayi saurin fitowa Ina mamakin yadda accident me zuwa a kankanin lokaci, duk yaji ciwo, aka daga shi police din se fadan gudun da vehicles keyi Yana korafin ko Basu son dadin Rai ba, ni dai nace su shigo dashi na Mika shi asibiti, bayan na duba lokaci Naga biyu ma Bata karasa ba, muna zuwa asibitin nai parking na Shiga na sanar da staff din na kawo victim, tunda na shiga unit din se na tuno ranar da na fara Shiga ranar da honorable ya rasu. Na kawar da tunanin na fita muka shigo dashi, kamar Wasa se naji muryar Al'amin a baya na, nayi saurin juyawa a tunanina ko gezau yake min, se Naga shi dinne kuwa. Muka gaisa yace ai Yana opposite din mu lokacin da abin ya faru shi me ya biyo ni, na Dan saci kallon shi, idanun shi Akan bump dina nace

" Nagode, Bari na shiga"

Se ya biyo bayana, tunda ya Shiga naji suna Kiran sunan shi, alamar sun San shi, yayi musu introducing Dina wasu sun game ni a ciki, Suka min gaisuwa na amsa sannan muka shiga wajen victim din. Tunda na shiga se memories din wannan ranar ke dawo min, naji gaba daya karar machines nake ji Kamar lokacin da oximeter ta dinga bada karar no pulse, Haka nan oxygen concentrator da suction machine, se naji yawu me daci ya cika min Baki na, naji wata irin hajijiya tana dibana

" Time of death 4:05pn"

Haka yayi ta min echo, se Naga ranar kawai nake gani, kaina naji Yana juyawa wani Abu ya tokare min kirji, ai kawai se nayi baya na Dan bude idanuna Amma a haka na zube sumammiya!

Unaisa is not free, pay N300 to 3091721807 and send evidence of payment to 09063467258

[6/12, 5:52 PM] Hauwa Galadima: MATA👰‍♀MASU🧕DARAJA👸🏻

🌹Gurop chat🌹

Litinin
Gyaran jiki🥛

💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦
SIRRIN MATSI
Chapter 40 · 0% Book details