← Book details Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 78

Sashe 56

Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya mike tareda kissing forehead dinta Bai ce komai ba ya fita, shi dai har ga Allah ya sani, yayi lallashin yayi nasihar Amma Taki yadda taki saurar shi, yasan tabbas da zafi hakan shima Bai tsara hakan ba baiyi expecting zaiyi hakan ba, to tunda hakan ta faru Babu yadda zaiyi face ringumar kaddara. Ya nufi parlon shi ya samu dukka suna zaune, gaba dayan su fuskokin su Babu dadi ya Dake ya shiga ya zauna dukka Suka gaishe shi, ya tambayi Muhammad da Aseey iyalai. Duka suka amsa Masa, ita Aseey har da tsoro Dan gani take ko ni ko Zuhra wani ya fada masa abinda taje hadejia tayi, dukda Bayan ta dawo sosae sukai fada da Baban Abil dinta, yace se ya fadawa Abiey taje hadejia Bai sani ba Kuma Bata tambaya ba sannan ita kadai taje. Tayi ta kuka tana bashi hakuri saboda tasan matsawar Abiey ya sani to tata ta Kare, karshen baci se ranta yayi.

" Nasan mahaifiyar ku ta fada muku, but ya kamata officially na fada muku zanyi aure. I'm sorry I don't know you guys were friends to her, nevertheless aikin Gama ya Gama! Ina fata zakuyi hakuri wata Rana zai Zama kamar baayi ba, idan wani Abu kuke ji, ku tunkare ni, ni daku muke da case Amma ita dai Babu abinda tayi, ita she's innocent, I'm not gonna let it slide duk Wanda ya Mata wani Abu!"

Kuna ganin Abiey ya dakko zaman lafiya? Kowa akayiwa hakan tabbas zaiji tsana da haushi, Haka dukkan su suka ji, kada ma Aseey taji labari kamar tayi me sede Abiey ba abin Wasa bane. Muhammad ya dubi Abiey yace

" Allah ya Sanya alkhairi Abiey! Allah yasa ayi a saa"

Abiey ya saki murmushi ya Dade da sanin Muhammad nada hankali yau ya Kara tabbatar wa. Ya dube su yace

" Amin Amin Muhammad nagode Allah yayi muku albarka. Ahmad ka daina maganar nan? Ka fasa ko Yaya?"

Ya dubi Abiey a ranshi Yana Jin ko kunya Bai ji ba yazo Yana cewa Wai zaiyi aure, yace

" Na fasa"

Abiey Yana murmushi yace

" That's ok! Idan Babu wani abun zaku iya tafiya"

Daga Haka ya mike zuwa bedroom din shi, Yana mamakin Ahmad he badly wanted project din, Abiey ya sama Masa Amma zuciya tasa ya fasa. Yayi murmushi yace shi ba uban da yaran shi zasu juya bane, a take ya bada contract din. Bayan ya bar gurin Muhammad yace

" Ahmad, Asiya this is bad of you, Bai dace abinda kukai ba"

Aseey da idanun ta Suka ciko da kwalla tace

" Unaisa zai aura fa"

Muhammad yace

" And so? Se me Dan ya aure ta? Ita tace tana son shi Ina sane kinje har hadejia kin mare ta, idan fitina take so zata fadawa Abiey and kinsan akan yarinyar nan zai hukunta ki. Zaiyi aure Nima ba Dadi nakeji ba Amma ya zanyi? Duk abinda baka da mafita akai to hakuri kake. Ni na Gaya muku saboda ranar da nasani!"

Ya mike ya fice su Kuma Suka je wajen Mamaa, Ahmad ya Dan Bata Baki sannan ya fice dukda maganar Muhammad ta shige shi Amma dai Mamaa tafi gaban komai. Aseey ta zauna tace

" Mamaa kince Zaki watsa auren Amma har yanzun shiru"

Tace

" Asiya bansan yadda zanyi ba kowa na Kira se yace zai kaini gurin malami"

Aseey tace

" To me kike jira Baki je ba, Mamaa Kinga kije kawai a lalata maganar nan"

Ta girgiza Kai tace

"Bazan iya ba, wallahi ba Zan iya salwantar da imanina ba Aseey! Ni ban yarda da boka ba kwatakwata'

Aseey tace

" Mamaa se kiyi istigfar kawai, Amma wanne abin kunya cikin kawayen ki ayi Miki kishiya da Yar bayan ki Yar cikin ki..."

Ko da Wasa basuyi tunanin Abiey zai shigo ba, take Aseey ta fara tari saboda yadda ta tsorata, bawai takura musu yake ba, Yana mugun Jan su a jikin shi Amma baya daukar iskanci. Ya dube su yace

" Kinji kunya, yace ki rasa abokiyar shawara se Aseey! Ke Kuma dama bakida hankali? Tashi ki fitar min daga gidana, wawuya kawai!!"

Ta mike ta yo saurin kallon Mamaa Dake Mata alamar ta tafi ta fice, ta fita har ya zauna se kawai ya fita.

A bangaren Abba ya Gama duk tunanin da zaiyi ya Kira Yaya Man ya Masa bayani, Yaya Man yaji nauyin abun Amma se yace Masa

" Abba duk yadda kayi, Amma da nauyi gaskiya"

Da daddare suka tafi shi da Dada zuwa gurin Anna, Bayan sun gaisa Abba yace shi ya yanke hukunci zai karba kudin aure ba daga hannun Abiey, saboda abubuwan da suke faruwa shi da Baffa since a saka wata biyu kawai. Anna ta girgiza Kai tace

" Da a bar maganar aurennan kawai, ka lallashi Unaisa ka lallashi baban Ahmad Amma bana son kayi wa wani abun da kasan baka so ayi maka, zanso Unaisa ta aure shi har Raina, na yadda da son da yake Mata Amma Abba ka Kara dubawa iyalan shi."

Dada tace

" Abinda na gani kenan, ni Zan lallashi Unaisa, saboda Talatu zata ga Dan bamu shiri shiyasa na Bari akai hakan"

Abba Bai ce komai ba Amma yasan bazai canza abinda yace ba ya dai bisu da to ne. Yana komawa ya Kira Muhammad, Ahmad da Kuma Aseey akan suzo gida su same shi. Ya Jima Yana musu nasiha me ratsa jiki sannan ya sallame su, a ranshi yace ya rage nasu su yadda da hakan ko su Bari.

Unaisa is not free, pay N300 to 3091721807 A'isha kwalam Hassan first Bank of Nigeria and send evidence of payment to 09063467258.

[6/19, 10:21 PM] Hauwa Galadima: *W_W*

Ana cikin wannan hautsinin ni Kuma Ina hadejia ban masan abinda yake faruwa ba, nidai kawai Ina zaune Ina Kara ninkaya cikin son shi bansan meke faruwa ba, shima Kuma kullum nuna min yake nothing bad will come duk abinda nake tunani to nayi expecting positive outcome. Da daddare na samu Baffa a parlon shi, bayan mun gaisa yace

" Har yanzun kina son Dr. Aminu?"

Dan Haka yake Kiran shi, banji kunya ba dukda zagin da Aseey ke min, warning da Kuma threats, hatta mahaifiyar su seda ta kirani, Ina kwance Ina kallon wani video tutorials Akan knitting, se ga Kiran ya shigo, na dauka da sallama Amma se naji baa amsa min ba, in fact warning ne ta Shiga shimfida min, nayi shiru har ta Gama sannan na kashe wayar na Kira Zuhra na fada Mata, tace

" Na Jima da sanin Bata da mutunci Amma ban taba sanin cewar Bata da hankali ba, kinsan Aseey ke zuga ta, wacce uwar kirkin ce zata Yi Haka. Ke wallahi Dole ki auri Abiey Naga yadda zasuyi"

Ni dai mamaki kusan kashe ni yayi, tutorials din da ban karasa gani ba kenan. Na gyada kaina Ina Wasa da hannuna, yayi murmushi yace

" Amma iyayen ki kamar ba sa so, kunyi magana dasu?

Na girgiza Kai nace

" Na tambayi Anna akan na hakura tace Wai nayi addua"

Ya gayda Kan shi yace

" Ki cigaba da addua! Allah ya zaba mafi alkhairi"

Bayan na baro parlon shi na dawo dakina, na Kira King, ya kashe ya Kira ni

" Abiey na"

Yace

" Naam Darling ya akai?"

Nace

" Kawai I'm missing you"

Yayi murmushi yace

" I missed you also, ko nazo"

Nayi sauri Na girgiza Kai nace

" A'a ka Bari se sun yadda an Gama magana"

Yayi dariya yace

" A Ka'aba mukai addua kin manta? Aikuwa dai kinsan Allah zai karba adduar mu ko. Unaisa ban taba jin bazan aure ki ba, I'll Marry you Inshaaa Allah, just continue loving me"

Wani Dadi naji cikin zuciyata, naji sanyi ya mamaye min zuciyata se naji tamkar gobe ne ma auren, naji zuciyata ta cika da farin ciki. Nace

" Ina sonka sosae kamar zuciyata zata fashe fa, I'll overflow"

" Thank you Baby for being strong!"

Na gyada kaina mukai sallama. Washegari na fara morning duty a wañnan ranar labor ward dinmu masu haihuwa ne kacakaca, tun Ina jin Dadi har na fara gajiya. Na dawo daki na zauna, kamar jira ake Wayata ta fara Kara, seda gabana ya fadi ganin sunan Dada ke yawo a screen din hakan yasa na dauka da sauri, muryar ta fes muka gaisa sanann tace

" Unaisa nasan maganata ba zata Miki Dadi ba, nasan ba Haka kike son ji ba Amma hakan zaayi saboda farin cikin ki da kwanciyar hankalin ki da namu Baki daya"

Tsoron da nake kenan, ranar da zaa zo ace na rabu dashi, ranar da iyayena zasu ce na hakura dashi, duk yadda nake son shi indai matannan guda biyu Basu amince ba tabbas Zan rabu dashi, Ina ganin shi dinma bashi bane, Ina ganin wannan din da nake ta addua akan shi watakila har yanzun Bai zo ba, to Amma se yaushe zai zo? Hakurina kullum karewa yake? Na gaji da kullum na dinga counting heartbreaks, na gaji da ganin laifin maza, I need to settle, I need to be Happy, Ina son na kalla namiji kwaya daya na Kira mallakina, se yaushe ne? Se yaushe?? Kowa yazo akwai matsalar da Zan barshi ba Dan naso ba.

" Dada ba komai, indai hakanne mafi alkhairi shi kenan"

Wannan maganar da nayi, ba karamin sacrifice bane, Ta danyi shiru inaga ba Haka tayi tunani ba, sede ita da kanta tasan dama bazan Musa musu ba, se Kuma tace

" Na sani Babu dadi, nasan kina son shi to Amma aure muke so kiyi Wanda idan kinje Babu dawowa, Honorable bashi da matsala, Hajiya Talatu ita ce matsalar, yaran shi ba damuwa bane tunda sunyi aure, Ahmad ba Zama zakiyi dashi ba, ita din ce dai matsala"

Wani iri nake ji a zuciyata, ji nake kamar an saka wuka an cakar min zuciya, wani Abu nakeji ya taso min daga cikina zuwa makogaro na ta tokare min, but I still have to continue listening

" Ki Kira shi kice Masa kin fasa, ki fada Masa yayi hakuri..."
Chapter 56 · 0% Book details