← Book details Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 78

Sashe 3

Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bance komai ba na cigaba da Jan carbina kawai. Babu jimawa Ahmad ya shigo shi tunda akai rasuwar Bayan ankai shi banma Kara ganin shi ba, ya rame ya to duhu na kalleshi shima ni yake kallo, ya karaso ciki ya zauna Dan nesa Dani muka gaisa muka yiwa juna gaisuwa sannan yace

" Ina Mamaa? Bakin zasu shigo"

Kafin na amsa shi se gata ta fito da carpet na Mike, na karba na shimfida sannan Ahmad ya fita se gasu sun shigo,mutum daya na sani Abba, ya zauna da mutanen da suke tare muka gaisa sannan Suka Mana gaisuwa. Sannan Abba yace

" A ganina Babu amfanin a zauna ana Jan magana, lawyer company din shi yazo Hajiya talatu zamuyi proceeding da compiling dukkan dukiyar shi a Raba gado"

Haka fa abun yake, ka Tara dukiya kana rasuwar zancen gado zaa fara, Babu Wanda ya damu da Kai se na kusa da Kai, hawaye suka gangaro min. Nasan Mamaa lawyer ce Kuma ya fada min dukkan takardun shi a hannun ta suke. Ta mike ta dakko katon file ta aje sannan tace

" Amma hanzari ba gudu ba, Baku ganin a Dan Kara lokaci Koda zai kasance Unaisa nada ciki!"

Anty Uwa Dake gefe tace

" Ciki Kuma? Auren kwana ukun haba ke kuwa Hajiya Ladidi"

Abba ya dubeni nidai kaina a kasa yace

" It's very possible, ni tunanin hakan Bai ma zo minba. Ahmad how early ake iya detecting ciki?"

Ya dubeni sannan yace a kalla  da komai na mallakin dukiyar shi, tun ana lissafi Ina ganewa har kaina ya daina dauka, addua kawai nake Masa Allah ya gafarta masa. Anan aka ware abubuwan da ya riga ya mallaka Mana, ce Kar a raba gado dasu. Malamin dake zaune ya kissima yaga eh Bai Shiga yadda musulinci yace kada ayi considering ba. Gidan da ya saka ni ya mallaka min babu a gado,akwai wani gida na Mamaa ne, se wannan gidan ya barwa yaranshi kada a raba dashi.

Unaisa is not free, pay N300 to 3091721807 Aisha kwalam Hassan first Bank of Nigeria, send evidence of payment to 09063467258.
[5/11, 5:55 AM] Hauwa Galadima: 🧕 UNAISA 🧕

*C*

✍️ Ayshatuuu

Haka na cigaba da Zama da Mamaa a gidan, yanayin zaman ya banbanta da abinda nayi tunanin ganin, na dauka baza mu taba maganar arziki da ita ba, yadda ta dinga fadawa Dada ta tabbatar idan Zan shigo na shigo da wasiyya ta Dan kuwa se ta min azabar dazan bar gidan da kaina, Amma ko kadan ko kallon banza Bata taba min ba, hasalima kallon da take min me dauke da tausayi ne. Har mamakin yadda muke zaune lafiya nake, last time da na sani balai take akan zaa auro ni, to gashi Kuma ta karbe ni hannu bibbiyu, ta hakura ta saduda, Amma akwai abubuwan da bazan manta ba. Ranar da aka Yi kwana bakwai akai addua a karkade, aka cire tampons Dake waje, wasu Suka gyara Mana gida sannan aka baje, Anna, Dada da Zuhra Wanda suka kasance tare dani duk ranar suka tafi, har mutanen hadejia ma, Anty Aisha ta tafi tun ranar uku Amma ana bakwai dinma tazo. Wannan tafiyar tasu yasa nayi ta kuka mussamman da Abba yace anan Zan zauna ba se na koma gida ba, Haka na yini a daki Ina kuka, har Anna ranar se da tayi kuka,  Ina ganin rayuwata a garari take, musamman da nazo kwanciya Naga Babu Zuhra da zata raba dare tana lallashi na, da Kuma min Hira Koda bazan amsa ba. Abokan shi Wanda ya kasance Senate president, da sauran senators tunda shima elected senator ne in office. Seda suka saka aka cika Mana store da duk wani nau'in kayan abinci sannan suka shigo suka Kara gaida mu ya aje kudi ya juya ya tafi su Muhammad Suka raka su. Washegari gidan Babu kowa, Jin shirun da gidan yayi yasa na kasa fitowa Bayan na idar da sallah na zauna Ina jin kewar shi a dukkan sassan jikina, kwana uku kawai mukai dashi Amma kwanakin bazan manta dasu ba, sun kasance masu dadin gaske, ya sakani farin cikin da nake mamakin yadda mutum zai iya hakan, Na lumshe idanuna hawaye sun wanke min fuska ta, na saka kaina tsakanin cinyoyina Ina kuka tun karfina, Ina cikin kukan se wayata ta fara ringing, na saki ajiyar zuciya tare da janyo wayar Naga Anna ce me Kiran, cikin sauri na goge hawayena na dauka Ina fadin

" Anna Ina kwana?"

" Lafiya Lau Unaisa! Ya kike Ina fatan bakya kuka"

Na saka hannu na dauke hawayen dake cascading a kuncina, na danyi sniffing nace

" Na daina Anna"

Ta Jima tana min nasiha sannan tace nayi wanka na fita na taya Mamaa aiki. Daga Haka mukai sallama na Mike jikina ba karfi nayi wanka sannan na shirya cikin wata bakar riga wadda Babu ado ko kadan a jiki. Hulata na cire Dan saka sabuwa anan naji yadda kaina ya damkare guri daya. Comb na dauka na taje shi Ina runtse Idanuna saboda yayi tsamu. Na zauna a nutse nayi kitso biyu na hade jelar na saka a hula sannan na dauki katon veil na yafa a jikina na fito parlor. Ba kowa se masu aiki sunata fama, muka gaisa suna kara min gaisuwa, Ina tunanin murya ta Mamaa taji ta fito, idanun ta sunyi jawur Wanda ya tabbatar min kuka tayi, na gaishe ta, ta saki fuskarta tace

" Ya Kika tashi Unaisa?"

Nace

" Alhamdulillah Mamaa"

Muna zaune shiru, tunda ba sabawa muaki ba balle muyi magana, plus Ina Kama kaina, Ahmad ya shigo ya shirya zai tafi aiki, muka gaisa sannan ya nufi kofa zai fita se na dubi Mamaa nace

" Bazai ci abinci ba"

Tace

" Ahmad abinci fa?"

Ya girgiza Kai, ta dubeni sanann tace

" No dawo ka zauna, Bari kasha ko tea ne"

Haka ya zauna aka kawo tea din yasha sannan ya tafi ita dama Aseey ta wuce gidan ta tun Daren jiya, Haka Muhammad ma da Bilkisu matar shi sun koma Gombe tun jiya. Se ya rage daga ni se ita, aka hado abinci Wanda naci kadan se naji zuciyata na tashi kawai se na Bari, ta dubeni

" Ko akwai abinda kike so ne?"

Na girgiza Kai Ina Dan murmushi nace

" Kawai bakina daci nake ji"

Ta gyada kanta kawai ba tace min komai ba. A hankali kwanaki suke shudewa, kullum Rana Yana Kara kwanaki a cikin kabarin shi, duk lokacin da na kebe se nayi kuka musamman idan na tuna yadda mukai rayuwa dashi, ranar da muka fara haduwa da irin artabun da akai kafin na aure shi, Amma Ashe Babu ma rabon zaayi doguwar rayuwa tare, kwata kwata kwanaki uku kawai mukai dashi ya tafi ya bar zuciyata da tabon rashin shi. Na goge hawayena Jin muryar Mamaa tana fadin

" Unaisa dakko hijabin ne Haka?"

Na dauki hijab din da wayata na fito, ta dubeni tace

" Kuka Kika Yi ko?"

Kamar ta zuga ni se wani kukan ya Kara kwace min, ta janyo ni jikin ta tana lallashi har nayi shiru sannan muka nufi asibiti. Ahmad na tsaye sanye da labcoat Yana jiran Karasowar mu. Muna zuwa office din shi muka zauna,  da kanshi ya dauka sample sannan ya cike forms ya Kai Lab, seda ya dawo Mamaa tace

" Ahmad dama scan kawai akai ko?"

Se yace Yana shafa Kai

" Wallahi mantawa nayi. Anty Unaisa sorry na bula ki"

Nayi murmushi ba tare da nace komai ba Dan har lokacin na ksa sakin jikina dashi ba duk yadda yake kokarin ganin na saki jiki, Yana Kuma kokarin wanke laifin shi a gurina, Amma Wanda yasa yayi min laifin ma Baya duniyar, meye abin fushi, kawai dai Ina iya takuna ne, Kuma dama bahaushe yace baa Bari a kwashe daidai. Tare muka fita zuwa scanning room din cikin asibitin, an cika sosae a gurin, ya Shiga Babu jimawa ya fito yace na shiga, Ina Shiga na kwanta dukda naji Babu dadi Ina Kuma ganin hararar da ake wurgo min ta kowanne guri, nasan munyi chancing dinsu. Gel ya shafan a ciki Bayan yayi min gaisuwa sannan ya dauki probe din ya fara gogawa a ciki na zuwa marata, yanayi suna magana da Ahmad da yayiwa screen kuri da idanu.

" She's pregnant Doctor!"

Nayi saurin duban fuskar Ahmad se Naga ya saki fuska Yana murmushi yace

" Alhamdulillah! Mamaa zata ji dadi. GA din fa?"

Yace fuskar shi a washe

" 20 days ne"

Shi Kuma a ranar kwanan shi Sha takwas da rasuwar, a raina na ayyana kenan ranar da muka fara having affairs a ranar na samu ciki. Na tuna ranar daurin aure friend Dita tace

" Kina zuwa Zaki samu ciki tunda ovulation kike yau"

Na harareta nace

" Ki gani akan ki, se na huta tukunna"

A hankali hawaye suka gangaro min na sakko daga gadon Bayan ya bani tissue na goge ciki na, na fito ganin hawaye na tsere a fuskata wani na korar wani, Mamaa tayi saurin tasowa tana fadin

" Ya akai Babu cikin ne kike kuka?"

Kaji Mamaa da wata magana, kawai Dan babu cikin se na dinga kuka, na karasa inda take tsaye har lokacin Ina kuka ban Bata amsa ba, Ya fito Yana fadin

" Mamaa akwai Mana"

" To meye abin kukan Unaisa? Kiyi murna Mana"

Na rike hannunta nace

" Haka zaa haife Babyn Bai masan mahaifin shi ba"

Se Naga duk jikin su yayi sanyi suma, Ahmad yace

" Haka Allah ya tsara, Allah ya jikan Abiey!"

Nace  Amin, bamu koma office din ba muka koma gida, da kanta ta Kira Anna ta fada mata, Anna tace Mata

" Kinga rabo"

Mamaa tace

" Wallahi kuwa, ni kaina abinda nake fada kenan. Allah ya inganta"

Ta Kira Abba ta fada Masa da daddare kuwa se gashi yazo shi da Dada ya duba mu, Asiya ma ta kirani tana fadin

" Nasan nayi Miki laifi Unaisa kiyi hakuri"

Ina zaune dirshan akan gado na Gama Shan kunun tsamiyar da Mamaa ta dama min Kiran nata ya shigo wayata, na dauka ko gaisawa bamuyi ba, na danyi  murmushi kadan Dan a kwanakinnan Murmushin ba sosae nakeyi ba. Nace
Chapter 3 · 0% Book details