← Book details Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 78

Sashe 22

Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Anna kiyi hakuri Zan shiga abinda Babu ruwana. Zancen Yaya Man ne da Badi'a, me yasa kuka Hana ke da Dada"

Ta kalleni tace

" Saboda mun Isa"

Amsar Bata min dadai ba Amma se na danyi murmushi nace

" Dama Kun Isa Mana Anna, Dan Allah kuyi hakuri ku barsu they are hurting, ba dadi"

Ta gyara zaman ta tace

" Adda ni ba ruwana a maganar nan, kawai dai ke ya kamata ace Man yake so ba Badi'a ba , nawa Badi'a take"

Se yanzun na gane basa son ace Badi'a tayi aure banyi ba, nace

" Anna Dan Allah karki kawo wannan,ni da Badi'a duk daya ne, Kuma Yaya Man ita yake so me yasa zaku ce ni, kowa lokacin Shi zaizo,plus duk cikin mu Badi'a tafi kowa girman jiki Dan Allah ki barta da kin yadda wallahi Dada ba zata ki ba"

Se tayi min banza har na gaji na fita, banji dadin hakan ba, na samu wayata da tarin calls da ban dauka ba, na Kira number farko ta preceptor ce ya tambayeni jiki na amsa da sauki sannan na Masa godiya Bayan Jin dogon lecture din Shi akan na kula da kaina. Se kuam na Kira ta karshen, seda ta Gama ringing har ta katse baa dauka ba so Sena saka wayar cikin pocket din gown dina na dawo tsakar gida nayi shiru deep in thought, Ina kallon yadda Badi'a ke kuka jiya which shows she's in pain, bazan iya rusa Mata ba, plus ni a ganina wannan is irrational ace Wai ya aureni. Da yamma Ina hada miyar kuka wayata ta fara ringing, gaba daya mood Dina is sour, dukkan mu ma, Dan dama Badi'a ita ce carefree entertainer to Kuma gashi tana tsaka me wuya, na Ciro Naga wannan number data Kira dazun ce, na goge hannuna na Kara a kunne na tare da yin sallama

" Waalaikumussalam Unaisa!"

Na danyi Jim Ina son tuna Ina nasan wannan muryar, its really familiar.

" Ya jikin naki"

There and then na fahimci waye, na kumbura Baki nace

" Alhamdulillah! Ya akai ka samu number ta?"

Ya danyi dariya yace

" Lokacin da kike karantawa Salis!"

Na kwalalo idanuna waje, kamar Yana ganina nace

" That's scam!"

Yayi dariya yace

" Ba Haka bane, Ina son na gaishe ki ne"

Na girgiza Kai cikeda mamaki, Ashe Dan kanshi yace a karba number yawa,  maza mutanen mu na ayyana.

" I'm Aminu, Amma mutane da kowa Al'amin ake ce min, so kema Zaki iya fadar Wanda kike so"

Na gyada Kai kamar Yana kusa Dani nace

" Tohm zanyi tunani, Amma me kake so?"

" Al'amin of course"

Se na fahimci Bai gane tambayar ba,

" Me kake so a gurina?"

Se yayi shiru har nayi tunanin ya kashe se yace

" I'm not sure Unaisa, kawai Dana ganki Naga ya kamata nayi magana dake"

Nace

" Ok! Ai munyi magana thank you!"

Ban ma jira amsar shi ba na kashe wayar, Ina mamakin yadda yake da wayo, ya samu number ta Babu wnai Shan wahala. Har na aje wayar se Kuma na dauka Dan saving number, "Nag" na saka Masa dukda zuciyata na kwaba ta Amma nayi mirsisi na aje wayar bayan nayi saving. Babu Wanda yasan gobe se Allah ban taba kawowa cewa akwai ranar da da kaina Zan dawo na cire Nag dinnan na mayar CÃNÎM❤️ ba.

Da dare Yaya Man ya kirani.yaji yadda ake ciki se na fada Masa Babu wani hope Amma ya Bari gobe zani wajen Dada. Nazo kwanciya se na kunna data kamar jira ake Sega pop din message daga Nag,

"Haeee! Kin kashe min waya dazun. That's rude"

Na danyi shiru Ina kallon message din Ina Kuma son sanin amsar da ta dace na mayar Masa se na fara typing

"Saboda kace min kana son magana dani, Kuma munyi magana ai"

" Ya kamata ki tsaya na kashe tunda ni na fara Kira ko?"

Nace

" Ok I want to sleep "

" That's early, ki tsaya muyi Hira Mana"

Naja notification panel na kashe data na koma na lumshe idanu take bacci yayi gaba dani.

Washegari na Kira Anna nace idan na tashi zanje wajen Dada, ta amince, Ina shiga gidan sama na wuce na bar Zuhra na kokarin hado Mana abinci, Ina hawa na same ta a daki

" Yanzun ke ba Zaki ji komai ba Badi'a tayi aure ke kina gida"

Nasan Babu dadi Nima ba dadin nake ji ba Amma ita yake so bani ba, Amma se nace

" To Dada kowa ba lokacin shi bane, lokacin ta ne yayi fa Dan Allah ki daina maganar nan, bana Jin Dadi Ina jin kamar Kun gaji Dani ne Dada, kamar sadaka ta kuke"

Se na fara kuka na cigaba da fadin

" Kuma su Yaya Man zasu ga kunyi son Kai"

Se tace

" Meye abin kukan, shikenan an fasa kema Allah ya kawo Miki naki"

Na goge hawayen fuskata Ina amsa Amin a raina. Daga Haka nayi wanka na saka kayan Zuhra se dare Yaya Man ya maida ni gida, tare da Zuhra muka taho saboda zata je gidan su Aseey Kuma shima Yaya Man zai biya daukar Yaya Muhammad. Dan Haka straight can muka tafi, gidan yafi nasu Zuhra Babu ma hadi, tun daga gate Yaya Man ya e

" Abiey Yana gida kenan!"

Securities ko ta ina, muka shiga Yaya Man ya Dan gaisa da wasu. A katon parlon su muka tarar da Mamaa wato Hajiya Talatu Kuma mahaifiyar su Ahmad tana zaune, da alamu zamanta kenan , kana kallon ta ko da ranar ne na farko zakaga alamar izza da mulki a tare da ita. Ba karamin Kama kaina nayi ba da ban zauna waige waige ba, parlon ya hadu karshe. Tun da mukai sallama take kallon mu har muka karaso, muka gaishe ta tace

" Se yau Zaki zo? Tun yaushe aka cemin kin dawo"

Zuhra ta danyi murmushi tace

" Ayya Mamaa wallahi idan na dawo na gaji shiyasa"

Ta gyada Kai ta dubeni tace

" Wannan Kuma fa?"

Zuhra ta dubeni yadda na sunkuyar da kaina tace

" Unaisa ce, cousin dita"

Ta kalleni sannan tace

" Ina jin sunan ta bakin Ahmad da Aseey! Sannu Unaisa! Kuma tayi Kama da kakar ku Dan dai Baku Santa ba"

Na Dan saki fuska na Kara gaishe ta, ba tareda ta amsa ba ta maida hankalin ta Kan Zuhra. A lokacin na Kara fahimtar ita da Dada Basu shiri Amma Kuma Basu saka yaran su a cikin abin nasu ba, Kuma kowannen su is good towards yayan su.

" Abiey na nan, kije ki gaishe shi Dan ana jimawa zai tafi Abuja sunada zaman majalissa. Sannan Kuma Babar ku uwa ma tazo"

Zuhra ta mike kamar nasan abinda zai faru se nayi zamana tareda fitowa da wayata, Zuhra ta kalleni tace

" Unaisa muje ko?"

Na girgiza Kai daidai fadin

" Yi tafiyar ki ke kadai, kinsan Bai son hayaniya"

"Hayaniya" ni zanyi hayaniyar kenan na ayyana, Zuhra ta Bata fuska Amma ba damar musu ta Kama staircase itama se ta bi bayanta aka barni ni daya duk makeken parlon nan, kowa zai ga kamar wulakanci ne Amma ni se Banga hakan ba tunda dama ya kamata a komai mutum yasan iyakar shi. Ina nan zaune Sega shi an kawo min dambun nama cikin karamin glass da Kuma juice hade da tumbler a saman tray, banma kalla ba balle naci, wajen five minutes Zuhra ta sakko tace min

" Kiyi hakuri!"

Na danyi murmushi nace

" Ke kina da matsala, muje gurin Aseey"

Dayan staircase muka bi zuwa dakin ta, tana kwance tana video call taji sallamar mu, yadda ta tarbeni.yasa na manta da abinda akai a kasa,

" Se dare Kuma zaku zo?.... Ina Anna dasu Badi'a?"

Muka Dan taba Hira sannan muka sakko Dan tafiya gida tana jadadda min Bata karba wannan zuwan ba. Muna sakkowa Yana saka kan shi wajen parlon, Banga fuskar shi ba se Bayan shi. Rayuwa is fun a times, akwai abinda idan aka ce maka zai faru zaka karyata hakan, ko a mafarki ko a hauka ko a Wasa ban taba kawowa Zan hada idanu dashi ba balle har ta kaimu ga soyayya, but Allah Babu ruwan shi.

Tun a mota Yaya Muhammad ke ta complain dalilin da yasa Yaya Man ya nace zai aure Badi'a

" Wannan child abuse ne wallahi Man,ka bar yarinyar tayi karatun ta zakai exposing dinta wata rayuwa, ga manyan Mata a waje"

Yaya Man ya kalleni ta front mirror kaina a kasa Nima Ina dealing da Al'amin da ya takura min wai so yake yazo.

" Kai Ina ruwanka kaje can da wannan Bilkisu ni Badi'a ce tayi min"

Ya tabe baki ya fada kasakasa yadda bazan ji ba Amma ni da Zuhra munji

" What about Unaisa, she's more matured kasan da ace I knew Unaisa first I wouldn't have chosen Bilkisu"

" Se na fada Mata Dan iska, yadda take creamy Allah taji se ta tada bomb inaga"

Ya kwantar da kanshi jikin kujera yace

" I was just sighting an example"

Ina shiga na samu Badi'a a daki da tsananin murnata nace Mata

" Badi'a Dada ta yadda"

Yarinyar nan ta kalleni ta yatsina fuska kamar ko yaushe tace

" Love Ya fada min ai"

Na Bata fuska Ina hararata, Nuzla Dake gefe ta wulla Mata pillow tace

" Ke uwarki! Shegiya!! Addar kike fadawa Haka? Dan kinyi saurayi Zaki dinga Mana kallon daidai, to mu ba Yan iska bane"

Nayi dariya na fita zuwa dakin Anna, na barsu anan Nuzla se surfa masifa take yayinda Badi'a ta Mata banza. bayan mun gaisa tace

" Kinyi kokarin turning table, se ki dakko biro ki fara list din abubuwan da zaa siyo"

Na danyi dariya nace

" Kai Anna kawai bana son suji Babu dadi ne"

Unaisa is not free, pay N300 to 3091721807 A'isha kwalam Hassan first Bank of Nigeria and send evidence of payment to 09063467258
[5/22, 12:52 PM] Hauwa Galadima: *T*
Chapter 22 · 0% Book details