← Book details Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 78

Sashe 4

Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Asiya magana ai ta wuce, komai ya wuce tunda Wanda akai komai Dan shi dinma ya rasu"

Se ta danyi shiru kafin tace

" Dan Allah Unaisa, ba Haka zakice ba, nasan baki manta abinda ya faru ba"

Na sauke ajiyar zuciya nace

" Asiya ya wuce wallahi, nasan fushi yasa kikai komai, Amma yanzun Ina fata kin fahimci dalilin da yasa Allah ya tsara na aura Baban ki ko? Rabo ne Asiya. Wanann cikin Dake jikina"

Ta jinjina Kai tace

" Na fahimta Unaisa, Dan Allah find a place in your soft heart and forgive me"

Nayi murmushi nace

" Ya wuce na yafe miki kada ki Kara tada maganar, mu fuskanci abinda ke gaban mu"

Ina jin dariyar ta saboda Jin Dadi ta Dan tsokane ni kamar yadda muke da sannan mukai sallama kowa yayi nashi wajen.

Kwanaki suka cigaba da tafiya, har Rana ta zago mukai Masa sadakar arbain, a wañnan lokacin annual leave Dina da na dauka ya Kare haka Kuma na Mamaa. Dan Haka na fara hada kayana Dan komawa aiki. Da yamma ranar asabar na Gama komai na fito daga toilet se na tsaya gaban madubi Ina kallon fuskata, na rame Rama ta ban mamaki, idanuna sun tashi daga asalin farare sun rine saboda yadda kullum se nayi kuka, Haka lips dina duk sunyi cracking kamar bani bace wannan Unaisar da kowa yake kwatancen gayunta, kaina tun wannan kitson biyun da nayi ban Kara ba. Ya kamata na gyara jikina na ayyana. Na cire kayana na dakko shaving cream, da shampoo na shga wanka, seda na wanke jikina da kaina tas sannan na fito, wata ajiyar zuciya na sauke Jin wata iska na shigata ta ko Ina, na zauna na gyara kaina sannan na shafa Mai, na saka turare me sanyin kamshi Wanda nasan bazaa ji ba, na zura wani bakin material dinkin A shaped gown. Anan na Kara tabbatar da ramar da nayi. Na daura dankwali na yafa katon veil na fito parlor. Suka suna zaune, Aarif din Asiya nata tsalle tsalle, Bilkisu na ma yarinyar ta magana. Ko rasuwar nan Bata min gaisuwa ba, Bata taba min magana ba Haka Nima ban taba Mata ba, ko abubuwan aurennmu Yaya Muhammad Bai taba shiga ba, Amma ita tafi Mamaa kishi, Muka gaisa da Muhammad sannan na koma daki Dan Mamaa da Asiya sun fita. Se yamma Mamaa ta dawo, Asiya ta fara shigowa tana fadin

" Kin nane a daki kamar me takaba"

Na tashi na zauna daga kwancen da nake nace

" Da me nakeyi idan ba takaba ba"

Se ta rufe bakinta tana dariya ta shigo, muka gaisa sosae tac e

" Da nazo ai Mamaa tace bacci kikeyi"

" Bana iya bacci da daddare"

Se Naga fuskarta ta Dan canja tace

" Me yasa? Wani gurin nayi Miki ciwo ne?"

Na girgiza Kai na nace

" Kawai abin duniya!"

Se ta Bata fuska tace

" Ya kamata ki Dan sararawa zuciyar ki Unaisa, mutuwa ba yadda zamuyi, we so much missed him wallahi"

Na gyada Kai na ba tareda nace Mata komai ba, se ta kawar da wannan hirar ta dakko wata.

Unaisa is not free, pay N300 to 3091721807 Aisha Hassan kwalam First Bank of Nigeria, send evidence of payment to 09063467258.

[5/11, 5:55 AM] Hauwa Galadima: 🧕 UNAISA 🧕

*D*

✍️ Ayshatuuu

Ranar lahadi da sassafe na fito a wanka , na Gama shiryawa cikin doguwar riga coffee Ina yafa veil naji sallamar Mamaa, na amsa se gata ta shigo na gaishe da ita, ta zauna gefen gado sannan na zauna tace

" Har kin Gama shiryawa se tafiya kenan?"

Na gyada Kai na Ina Dan murmushi kadan

" Allah ya jikan honorable!"

Na amsa da Amin sannan tace

" Zaki dinga zuwa ko? Ko Dan Zan dinga zuwa Ina ganin ki. Ki kula da cikin jikin ki Dan Allah, kada ki Bari damuwa tayi Miki yawa, ki sani komai shiryayye ne daga gurin Allah, sannan kiyi hakuri abubuwan da suka faru a baya, bansan me yasa nayi Haka ba, bansani ba"

Nayi saurin riko hannun ta ganin idanun ta na cikowa da kwalla nace

" Ai ya wuce Mamaa, Inshaaa Allah Mamaa ya wuce, "

Ta aje min kudi tana min godiya, nayi saurin dubanta Ina girgiza Kai nace

" Mamaa inada kudi Dan Allah ki barshi"

Ta dube ni na Dan lokaci sannan tace

" Karki damu hakkin ki ne ai, kawo Mana akai kin manta"

Ban tuna ba kawai se na gyada Kiana na zura kudin a jaka Ina Mata godiya, tana murmushi tace

" Nagode da Kika zauna Dani na wajen kwanaki hamsin, nagode sosae duk abinda kike bukata ki sani hakkina ne na Nemo Miki shi, Allah ya jikan Honorable ya gafarta Masa ya kyautata namu zuwan"

Inada saurin kuka, wannan maganar tata tasa na fara kuka, ta rungume ni a jikinta tana lallashi, seda ta saka ni a gaba naci abinci sannan ta janyo akwatina na biyo ta da karamin da Kuma handbag dina. Suna zazzaune dukkan su a parlor suna breakfast. Ina shigowa Muhammad ya saki murmushi yace

" Anty Unaisa Ina kwana?"

Nace

" Lafiya Lau Yaya Muhammad, ya Islam?"

Ya dubi Islam Dake cinyar Maman ta yace

" Gata nan me kukan dare"

Nayi murmushi, Ahmad ma ya saki fuska sosae muka gaisa yace

" Babu matsala ko? Ba wani Abu?"

Na girgiza Kai nace

" Babu komai!"

Dan gaskiya nakan manta cewar ciki ne dani, bana laulayi ko kadan ko craves dinma ba nayi. Asiya ta dubeni muka gaisa na karbi Aarif a hannunta. Amma Bilkisu ko kallona batayi ba tana spreading chocolate spread akan slice bread a gaban ta. Idon Mamaa yasa nace

" Bilkisu Ina kwana!"

Muhammad ya kalleni sannan ya kalleta Bai ce komai ba, Mamaa tace

" Bilkisu kinada matsala da Unaisa ne? Na lura ko magana bakya mata"

Ta girgiza Kai Bata ce komai ba, Mamaa se tayi shiru, Ahmad ya Mike tareda Jan trolley na yace

" Anty Unaisa mu wuce ko?"

Na mike Ina gyara lullubi na na dubi Mamaa data mike nace

" Nagode Allah ya saka da alkhairi"

Ta rike hannuna muka fita harda Asiya me min kashedin na dinga cin abinci, se Dana shiga mota sannan Muhammad ya karaso mukai sallama dasu Mamaa na Mana Allah ya kiyaye Hanya. Tunda muka dauki hanya mukai shiru se karar radio Dake aiki har muka karasa kofar gidan mu, ya samu guri yayi parking yace

" Zaki Dade naje wani gurin? Ko Dan Zan dawo nan da 2 hours. Is that ok by you?"

Na gyada Kai nace

" Yayi, seka dawo"

Daga Haka na shige gida yayi reverse ya bar unguwar, da Hunainah na fara Karo ta fito daga kitchen dauke da plate din abinci, tana ganina ta aje plate din ta taho ta rungume ni tana fadin

" Anna ga Adda Unaisa tazo"

Kafin Anna ta fito tuni Nuzla ta fito tana ihun

" Adda Unaisa oyoyo"

Itama ta fado jikina, karon farko da nayi dariya tsakanin da Allah tun Bayan rasuwar shi, bayan sun sake ni na hangi Anna a tsaye tana murmushi, rabo na da ita tun ranar sadakar bakwai, tayi kokari Bata Kara komawa ba, su Nuzla ne Suka jemin wajen sau uku, Zuhra duk sati se tazo, Dada da Abba ma sunzo har bazan iya irgawa ba, Baffa Dake baya nan akai rasuwar ranar da ya dawo daga China, ko hadejia Bai he ba ya taho gidan, ranar nayi kuka da ya saka ni gaba da lallashi, da nasiha. Rayuwa kenan!

Na karasa da sauri na rungume ta, itama ta rungume ni tana sakin murmushi, sannan ta ja hannuna muka shiga parlon Dake kunshe da dakuna biyu, daya mallakin Anna daya Kuma namu mu uku, Dake ba kasafai muka Faye Baki ba shiyasa gidan Bai Mana kadan ba. Na zauna saman carpet nace

" Anna Ina kwana?"

" Lafiya Lau Unaisa! Nayi tunanin se yamma Zaki tafi"

Na girgiza Kai nace

" Bana son nazo nan a tsatsaye shiyasa Naga gwara na taho da wuri"

Se ta gyada kanta, sannan ta mike tana tambayata abinda zanci, na danyi shiru Ina tunanin kafin nace

" Kawai Anna ki bayar a siyo min awara"

Tayi murmushi tace

" Aikuwa nama manta har nake tambayar ki"

Ta shiga daki Babu jimawa ta fito da note din dari biyar ta bawa Hunainah tace taje can makwabtan mu ta siyo min, Amma ta dauki food flask Bata son Abu a Leda. Hunainah ta mike yayinda Anna ta fita ita Kuma, se ya rage daga ni se Nuzla Dake danne danne a wayatta se sakin murmushi takeyi. Na dubeta nace

" Nuzla whatsup?"

Tayi dariya tace

" Nothing! Tare zamu tafi ko?"

Nace

" Abinda Anna tace"

Se ta aje wayatta ta matso kusa Dani tana magiyar nace ita Dan Allah, na Harare ta nace

" Saboda me Wai? Me yasa kike son Bina Wai"

Ta langwabar da Kai tace

" Kawai Kinga strike akeyi Ina bukatar fresh air"

Na tabe baki nace

" Ni Kam su Baffa Me gishiri Basu San anyi min rssuwa ba"

Anna dake shigowa tace

" Ki kyalesu, bawani Abu bane Dan Basu zo ba"

Na dubeta na gyada Kai, Nuzla da bakinta baya shiru tace

" Amma Anna ai sunzo biki, har yayan shi na aure seda suka zo cin shinkafa Amma gaisuwa sun kasa..."

Me zanyi Banda dariya, Anna ta wurga mata Parker Dake aje a gefenta tace

" Ubanki Nuzla! Bakin ki baya shiru ko"

Ta mike tana dariya tayi ciki, na Mike kafata daidai sallamar Hunainah, ta shigo da kwanon ta aje sannan ta mikawa Anna kudin da baa fasa ba tace

" Anna Baba Delun tace Wai ba zata karba ba tunda ta Adda ce, tace tana Miki sannu da zuwa zata shigo"

Nayi murmushi Ina yin godiya Haka ma Anna, plate ta kawo min na zuba ga lettuce da tomatoes data yanka min na hada, tana ta kallon kofa kamar me jiran Abu,  hakan yasa nace

" Anna kina jiran Abu ne?"

Ta gyada min Kai tace

" Naman da kike so na bayar a siyo Miki Kuma har yanzun baa kawo ba"
Chapter 4 · 0% Book details