← Book details Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 78

Sashe 73

Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A wannan karon ban barta ta gama kukan ba na ce, duk laifin ki ne fa, nan da nan ta yi shuru ta ce 'Kamar yaya laifina Anti na gaya miki fa ina masa biyayya ina hakuri da shi, sai ya kwana yana waya da chatting da yan mata a gabana.'

Na ce eh laifin kine, domin kin fara wulakanta kanki tun kina waje, kin zubar da kimar ki, don haka mutuncinki har abada ba zai dawo a gurinsa ba, sannan zai ci gaba da zarginki da miki wulakanci, kuma ina zaton ba ki yi Istibira kafin ku yi aure ba, don haka kin ga akwai matsala ta sabawa ubangiji cikin auranku, daman shi ubangiji yana yiwa bawansa talala sai ya kama shi ta gurin da bai zata ba, don haka sabon da kuka yiwa Allah shine ku ke ganin illarsa, kuma yawanci daman mata sun fi shan wahala idan suka bari irin haka ta faru, domin shi namiji yana da dama fiye da su tunda shine a sama su a kasa, dole komai ya kwaso ya jibga akansu.

Sai ta kara fashewa da kuka 'Yanzu shikenan haka zan ci gaba da rayuwa cikin bakin ciki Anty.'

Na ce mata a'a, ai kina da damar da zaki gyara kurakuranki, don haka ki mayar da hankali gurin tuba sosai da kai kukan ki gurin ubangiji, na san yanzu ba ki da darajar da zai saurareki idan kin ce za ki yi masa nasiha, to bai fi karfin Allah ba, ki kai kararsa gurinsa, ki rokar masa shiriya da neman ya zama mai sassauci a gurinki, ki yawaita sadaka, sannan ki rage saka damuwa a ranki, ki kuma rage gayawa yaranki abun da ya ke miki, suma ki yi ta musu addu'a da nasiha, Insha Allah sai ki ga Allah ya kawo miki mafifa, ba makawa ma dukkan tsanani yana tare da sauki, karshe dai ta gano babban laifin da ta aikata wanda tare suka yi amma ita ya fi bibiyarta.

Aunty Fauziyya D. Sulaiman
[7/2, 4:18 PM] Hauwa Galadima: *I³*

Akwai banbanci tsakanin auren Abiey da auren Al'amin, a wañnan auren I'm exposed nasan dukkan abinda ya kamata ace nayi da kaina ba se anyi min ba. Kayana da kaina na Kai dinki na Kuma fada Masa irin styles din da nake so, gyaran jikina kusan wata biyu to biki na fara, ni kaina jikina ya canja, kallon kaina nake and I found myself blushing da hakan.

Kamar Wasa kamar mafarki, se ga kwanakin biki sun taho dab. Saura wata daya na hade kayan su Jr tas na bar kadan su Nuzla Suka zo Suka kwasa, two weeks to biki suka zo Suka dauke su, bayan sun tafi na shiga dakin da katifa ce kawai ta rage se akwatin da kayana suke ciki, na zauna gefe na Sha kuka na, Ina cikin kukan Al'amin ya Kira ni, na dauka yay shiru Jin Ina sniffing, yace

" Are you crying?"

" I missed them already fa"

Yayi Dan murmushi yace

" To yayi kiyi hakuri kinji? Zaki dinga ganin su ba gari daya muke ba, idan kina kuka Zaki iya samun attack no hankalina bazai kwanta ba"

Nasa hannuna ina dauke hawayen dake min zarya nace

" Na daina!"

Yace

" Yawwa! Are you going out yau dinnan?"

Na girgiza Kai nace

" A'a, Zuhra zata zo Ina karasa parking kayana ne"

Yace to na Gama zamuyi waya daga baya. Gidan Abba yace zaa saka Yan haya, tunda gyaran da zaayi kadanne. Da azahar Zuhra tazo muka karasa kwashe sauran kayayyakin da suka rage, Anty Aisha ta shigo da yamma muka gaisa tana daya daga cikin mutanen da suka bani goyon baya dark bisa dari a wañnan zaman da nayi, min Sha Hira kamar ko yaushe ta bani shawarwari sannan da Kuma gudunmawar ta. A washegari na tafi Kano Wanda idan na dawo Dutse to aure ya dawo Dani. Na kwanta a dakin mu Ina tuna rayuwa yadda ta dinga gudu har lokaci ya tafi Haka ba tare da na ankare ba, abubuwan duniya ba karamin shagaltar damu suke ba da sede kawai mu jiya muga shekaru sun tafi, ga Wanda ya dace har ya fahimci lokacin na tafiya wani kawai sede ya farka yaga me faruwa ta faru, Allah ya rufa Mana asiri! Kalla irin gumurzun da akai akan auren Abiey wai har ya wuce anyi auren har ya rasu Zan sake wani auren, kowa da akai abin min shirya Bilkisu ce kawai bamu shirya da ita ba tunda dama can ba yi muke ba, Kuma aka zo wani sati da Mamaa take dutse se ta karaso se take cemin ai aure Muhammad zaiyi ma, na danyi mamaki tace to Bilkisu taki bada hadin Kai ayi zaman lafiya, shi Kuma ya gaji tunda sukai haihuwa daya Taki karawa Wai ita jikinta. Nace

" Mamaa kafin yayi auren kiyi magana da ita"

Tayi dariya tace

" Ommaan Alby ni da kaina naje har gidan sasanta su Amma taki ji, bayan na tafi tayi yaji, I still followed her gidan su, maman tace Wai idann min gaji mu sake ta"

Nayi salati banji Dadi ba tace ita Kuma duk abinda zaayi Bata son saki gwara kawai yayi aure dama shi ya kawo maganar shi, nayi musu fatan alkhairi, bamu Kara haduwa da ita Bilkisu ba se recently da Zuhra ta haihu tazo suna, tana kallona Taki tayi min magana, no Kuma na musu magana Haka dai abubuwan Kara lalacewa suke.

Sati na zagayowa muka fara biki, wannan karon a gidan mu Anna tayi taro, mutane sosae suka zo, kawayena abokan aiki na, mutanen Anna, dangin Alhaji Yahai da dangin Abiey sun yimin Kara, Anty Salma a gaba. Yadda na tsara was a single day wedding, tun safe da nayi wanka akai min kwalliyar na shirya nayi kyau idan ka kalleni karya kace na taba aire, nayi kyau abuna. Da Rana aka daura aure na Kara shiryawa cikin wani lace me kyan gaske, Ina gyara bow din jikin zanina, Mamaa ta shigo hannun ta da kasko se kamshi ke fita, tace

" Mashaaa Allah! Kinyi kyau, you made a beautiful Bride Allah ya dawwammar muku da farin ciki"

Ina Dan Murmushi na amsa Amin, ta turara min jikina da kayan Dake jikina sannan ta lulluba min mayafi har kaina tace

" Allah ya Sanya alkhairi"

Na Kara fadin Amin sannan ta fita, Babu jimawa se gidan ya kacame da guda Wanda ya tabbatar min an daura min aure a Karo na biyu, Ina fatan wannan lokacin ya zamana auren me daurewa ne, na Dan lumshe idanuna Ina tuna ranar da aka daura aure na da Abiey, irin murnar da nayi dukda seda nayi kuka, na saki murmushi Ina Yi Masa adduar Kara samun rahmar ubangiji. Babu jimawa muka fita inda Al'amin da abokan shi Suka shigo, yayi kyau har na kasa daina satar kallon shi, fuskar shi kwance da tsantsar farin ciki, mukai hotuna, aka gaggaisa aka saka Mana albarka, kakkani nata tsokanar mu. Da yamma Abba yazo inata shiryawa saboda ance shi zai kaini da Kan shi, Jr yazo yaga ana daura min lafaya, ya rike hannuna na dube shi nace

" Ina Alby?"

Yace

" Yana wajen Grandma"

Na gane Mamaa yake nufi, na rasa yadda akai suke ce Mata Haka, nace musu ba Grandma din su bace Amma sunki yarda, nace

" Jeka kaima wajen ta, yanzun Zan fito"

Har ya sakeni se ya dawo ya riko lafayar yace

" Unguwa Zaki je?'

Na gyada Masa kaina saboda bana Yi musu karya, yace

" Zaki dawo?"

Nace Masa eh, se ya sakeni ya fita, na koma kan gadon na zauna Ina sakin kukan da nake rikewa, Zuhra ta fara lallashina tana ce min nayi hakuri, seda nayi me isata sannan muka fito, ana ta min addua muka tafi, na bar gida a Karo na biyu. Tafiyar ba kamar yadda nayi tunani ba, Abba Bai kaini ba kawai yayi min nasiha ya Kuma tsaya yaga tafiyar mu, Ina tsakiyar Dada da Mamaa, se Muhammad ke driving Zuhra a gefen shi, it was a ride suna tayimin nasiha da bani tips Akan rayuwar aure. Mutuwar Abiey tasa an samu reconciliation tsakanin Dada da Mamaa, zumuncin da Abiey yasi sui Taki yadda yanzun dai gashi anayi. A Karo na biyu Ina fatan na karshe se gashi na dawo Dutse matsayin amarya, amayar Al'amin. Ina ganin Babu wnai buri da nake jiran ya cika Kuma, sede da yake ba a raba Rai da buri.

Gidan mu yayi kyau, asalin kyau ma kuwa, Suka aje ni suka Dan yimin gyare gyare zuwa Bayan sallar maghrib suka juya Zuhra ma bata zauna ba, Dan hatta Little a gida ta barshi. Nayi jugim Ina tunanin yadda zaa Fara sabon babi kuma, sabuwar rayuwa Kuma. Har akai sallar ishai sannan naji an bude gate, gabana ya fadi tuna shigowar Abiey se nayi saurin dauke wannan tunanin, Abiey is in the past Haka Abba da Anna Suka cemin, nayi kokarin mantawa da waccan rayuwar na karba sabuwa shi me kawai Zan zauna lafiya, inata tunani se sallamar shi naji a bakin Kofa, na dago a hankali na kalleshi, ya karaso ciki fuskar shi kamar gonar auduga, Baki yaki rufuwa murmushi kawai yake, ya karaso ya zauna gefena tare da kwantar da kaina a kafadar shi yace

" I'm so happy! Ban taba farin ciki irin na yau ba Unnie, I finally found you I even have you"

Ya yaye lullubin saman kaina yayi min peck a goshi yace

" Bude idon ki ki ganni Mana"

Na bude na sauke cikin nashi, seeing all the molecules da suke fitowa suna Shiga naaa, tamkar mu dawwamma a Haka Haka nake ji, ya riko hannuna cikin nashi, ya Kara bani peck a hannun yace

" Don't let go of my hands no matter how hard it becomes"

Na damke hannun nace

" I promise you"

Se ya rungume ni mukai shiru Muna Jin yadda zuciyoyin mu suke bugawa, kamshin jikinmu Suka gairaye Suka bamu iska me dadi. Me yafi soyayya Dadi? Ka dace shi ne komai!
Chapter 73 · 0% Book details