← Book details Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 78

Sashe 5

Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Nayi murmushi Ina ayyana that's my Queen mother! Ina kaunarta Dan kuwa ita din ita ce komai namu, Fadi tashin da Anna tayi Akan mu bazai fadu ba, ko uban mu haifar mu kawai yayi, Amma cin mu da Shan mu, sutura da komai bamu it's ce, se ya kasance maganar ta a gurin mu it's kadai muke ki, saboda a ganin mu it's din ta cancanci every of our loyalty! Har na Gama ci kuwa ba a kawo Naman ba, na dubi agogon wayata saura awa daya kawai Ahmad ya dawo, na dubi Anna nace

" Anna Kinga har yanzun Badi'a Bata zo ba, Kuma lokaci na tafiya"

Hunainah tace

" Zata zo kuwa, Dan dazun ta Kira Adda Nuzla tace zata zo"

Na gyada kaina kawai tare da Dan kwanciya na Mike kafata, Anna tace

" Da waye Zaki tafi a cikin yaran nan, munyi magana da Dadar ku tace tana Neman dattijuwar da zata zauna dake kafin ki haihu"

Nace

" Duk Wanda kikace Anna daidai ne"

Ta dubi Nuzla tace Mata ta hada kayanta, tayi wani Murmushin jin Dadi ni Kuma na girgiza Kai.  Badi'a Babu jimawa tazo, da yaranta biyu Nasrin me sunan Anna se Wahida me sunan Dada. Mun Sha Hira har Ahmad ya kirani akan ya dawo, Haka Dole muka rabu, Anna nata min nasiha akan hakuri da juriyan, ta nuna min Allah ke tsara  komai Dana gani. Na share hawayena na fito, Yana tsaye ya harde hannayen shi a kirji, his father's look alike, na tuna lokacin da yake kawo Zuhra gidannan, lokutan da suke zuwa da Aseey, wansu lokutan yazo shi kadai, idan na fito shigowa da su yayi ta tsokana ta Yana cemin Wai daga ni gayu ya kare, zai so yaga mijina. Wani lokacin yace min Kar na sake na auri Wanda bashi da kudi bazai iya jurar necessities Dina ba. Amma haduwata ta karshe dashi shi ne Wanda yazo ya zazzage ni har gida, ya cimin mutunci , ya kirani da macijiya me cin Amana me kwadayi, bayan yasan baban shi Yana neman aure na. Wannan ranar nayi kuka har seda Anna tayi fushi Dani. No a lumshe idanuna ganin yadda rayuwar take sauri, Wai har anyi an Gama? Anyi bikin har ya rasu? Su Kuma Dake ba halin su bane har sun hakura, Yana ganin Anna ya tsugunna ya gaishe ta sannan ya bude min kofar din baya na shiga, Nuzla ta zauna gefen shi muka dauki hanya, seda muka biya gidan Dada sannan muka tafi, nan ma seda nayi kuka saboda nasihar da Abba kemin. Tunda muka tafi nake kaartun qurani cikin wayata har mukaje Dutse. Har kofar gida ya aje mu ya fito Mana da Kaya,

" Ka shigo kasha ruwa"

Ya girgiza Kai yace

" Zan dawo dubaki Inshaaa Allah! Dan Allah ki kula ki Kuma Yi hakuri da dukkan abinda Suka faru Dan Allah"

Ina iya hango nadama da Kuma kunya ta a idanun shi, Nayi murmushi Wanda mahaifin sa ya kance Wai shi ne abinda ya fara capturing zuciyar shi. Nace

" Ya wuce. Allah ya kiyaye Hanya ka gaida Mamaa"

Daga Haka na wuce na saka key na bude kofar parlon, na barshi tsaye da Nuzla. Katon parlon da aka tsara shi, na tsaya a tsakiyar Ina tuna ranar da aka kawo ni, ya shigo ya sameni zaune Kan daya daga cikin kujerun na takure, ya zauna gefena ya yaye min veil din da ya rufen fuska, tare da fadin

" Amarya bakya laifi ko kin kashe Dan masu gida!"

Kamar wani video Haka na cigaba da rewinding duk wani moment da muka kasance tare dashi, na zauna jagwab cikin kujera Ina sakin matsanancin kuka, in between sobs din Ina fadin

" I missed you!'

A Haka Nuzla ta shigo ta sameni, ko Bata tambaya ba tasan mijina na tuna Bata cemin komai ba, se da nayi me isata sannan na wanke fuskata a sink din dining na dauka wayata na Shiga bedroom dina, ban taba kwana a ciki ba na zauna na Kira Anna, Mamaa da Kuma Dada na sanar dasu munje. Kowannen su seda ya bani Baki a karshe Abba ya kirani ya Jima Yana min nashiha sannan mukai sallama. Zuhra ce kawai ban Kira ba, Dan na San tahowa zatayi.

Unaisa is not free, pay N300 to 3091721807 A'isha kwalam Hassan first Bank of Nigeria and send evidence of payment to 09063467258
[5/11, 5:55 AM] Hauwa Galadima: 🧕 UNAISA 🧕

*E*

Ayshatuuu

Nasan zuwa yanzun Kun kosa kusan asalin Labarina, zaku so kuji wacece Anna? Haka Mamaa Haka Dada? Su Ahmad da dukkan role dinsu cikin rayuwata. Sunana Unaisa Yahya, mutane da yawa sukance Wai a gurina Suka fara jin suna Unaisa, ni kaina Bayan ni me sunan baifi sau biyu na Kara jin me irin sunana ba.

Mahaifina Dan wani kauye ne ko Kuma nace gari a Masaya Dake karkashin Birnin kudun jihar jigawa. Mahaifina sunan shi Alhaji Yahya tun Yana saurayi sunan shi kenan, Dan bashida aikin da ya wuce yaje Saudi Arabia yayi shekara uku, hudu har ma biyar sannan ya dawo. Hakan yasa duk garin kowa Alhaji Yahai ake ce Masa memakon Yahya din. Mahaifiya ta sunan ta Hassana tace Mana ita Yan biyu ce Amma abokin tagwaita Kar tata shi ya rasu. Su biyu ne gurin iyayen su itada Baba Zulai a Wanda ta sani. Tace Mana dukkan Yan uwan ta idan aka haife su rasuwa suke, Amma akwai yayun su biyu Wanda Suma Basu San su ba, ba Kuma ta San inda suke ba, su biyu kadai Suka rage. Iyayen Anna Fulani ne Wanda ke yawo a duk inda Suka samu shanun su zasuyi grazing. Suna tafiya Allah ya kawo su Masaya lokacin Zulai Bata fi shekara goma Sha biyu ba, da suka zo sukai camping can bayan gari ita Kuma tana Dan shiga gari da sauran Yara a Haka dagaci ya ganta ya aure ta. Lokacin ana goyon Anna, da lokaci yayi suka kada shanu suka tafi Suka barta. Se bayan shekara hudu lokacin Yayanta biyu sannan suka dawo, sunzo wucewa, . Zasu tafi dagaci ya samu da kyar ya karbe Anna with the hope cewar idan Anna na nan zasu dinga zagayowa suna ganin su. Suna tafiya baa fi kwanaki uku ba Wanda dagaci ya aika ya gano hanyar da Suka dauka ya dawo yace iska akai sosae wadda tasa da yawa Suka rasu Kuma ciki harda kakkanin mu. Wani maganar ta girgiza kowa se Anna ta tashi hannu Inna Zulai ita ce uwarta da ubanta da komai nata. A Haka ta girma hannun su Babu makaranta da aka saka ta har ta shekara Sha biyar aka dinga zancen Bata samu miji ba, Anna kyakyawa ce ta gaske tana da gashi Haka Kuma karamin jiki me da ita kamar yadda Inna Zulai take. Kana kallonta kaga bafullatanar asali. Fara ce tas har yellow yellow take. A shekarar Alhaji Yahai ya dawo daga saudiyya Bayan ya shafe shekaru acan. Dagaci Baffa ne a gurin shi, da kakata da ta haifi Yahai da dagaci uwa daya uba daya suke, Kuma ita din uwar dakin Inna Zulai ce Dan Haka Yana neman auren Anna Babu wani ja aka hada su auren. Har muka girma nasan Anna Bata son Babana, ban taba ganin ta saki jiki idan tana tare dashi, gashi ni yarinya ce me bin kwakwaffi, I observed kamar spy Haka nake.
Chapter 5 · 0% Book details