Sashe 69
Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A bangaren Alhaji Mustapha baice ma Hajiya Attine komai ba se bayan sati daya bayan ya Gama tabbatar da cewar hooking Al'amin da Nura akai, da daddare ya dawo daga inda yaje ya Kira Nura da Hajiya akan su same shi parlon shi, Babu jimawa Suka hayo, shi kadai Yana zaune Yana kallo, a shakarun shi da girman shi he's still obsessed with Hollywood action movies, ya bada hankalin shi Yana kallon wani movie more of sci-fi. Su sun Saba da hakan Basu ma ganin odd din abun. Sunfi awa daya sannan ya dube su yace
" Nura wanene Harith?"
Ta Dan kalle shi idanun ta a Dan warwaje saboda Babu Wanda yasan da Harith idan ba ita ba, ko Al'amin yasan tana da saurayi but she never mentioned even his name. Ta Sosa kanta tana kallon uwarta dake binta da wani irin kallo, tace
" Abbu saurayina ne"
Hajiya Attine tace
"Saura...."
Ya daga Mata hannu yace
" Ina zuwa kanki, gaggawar me kike Yi?"
Tuni taji wani sauyi a tare da ita, Abbu yace
" To shi Kuma Wanda Kika kawo har an saka Rana sati hudu ya rage aure fa? Nura tarbiyyar da nayi Miki kenan? Ko kasa Zaki watsa min a idanuna"
Ta Dan kalla mahaifiyar ta, sannan ta kalla Abbu that looks disappointed Wanda hakan ne ba zata jura ba, she has been good saboda shi, saboda kada watarana yace she's a disappointment
" Abbu bana son shi, ni Harith nake so. Ummiey kiyi hakuri"
Ta fada tana avoiding hada idanu da Maman, Hajiya Attine ta dunkule hannun ta tana Jin zufa na karyo Mata, me yasa maganar nan zata taso duk yadda ta nunawa mutumin nan Nura ke son Al'amin. Yayi murmushi yace Nura taje sannan ya kalla Hajiya yace
" Kiyi min bayani"
Ta rasa ta inda zata fara, ta rasa yadda zata kamo zaren, tasan halin shi shekaru kusan talatin da biyar ana aure ba shekara uku bace, Jin tayi shiru yace
" Ki warware maganar yadda Kika hadata, 'Yata ba zata aura Wanda Bata so ba, 'yata tafi karfin Shiga wannan gidan. Attine tunanin me kike? Me suke dashi? Wa Suka sani? Me Suka Tara? They're just bunch of Nurses, uwar, uban da Kuma dan, so kike na auarar da ita na cigaba da Bata abinci? Yata ba zata aura irin wannan mazan ba da Basu da kudi, ai wanann nauyi ne, liability zai zame min. Na Gama magana ki kunce auren"
Shi sharri Dan aike ne, akace Kan maishi yake komawa, Kuma duk abinda ka shuka watarana shi ne zaka girbewa! Wannan Haka yake, a lokacin da Mummy tace Unaisa zata zamewa Al'amin liability Bata taba kawowa cewar ita ma zaa tambayi me ta Tara ba? Zaa ce danta liability ne. Duk rokon da Hajiya ta Masa Bai kulata ba, a washegari taje gidan kanin Abbu din Wanda ya karba auren Nura ta fada Masa, se yace ta rabu dashi ai da izinin sa akai komai. Daga Haka ta bar maganar ta cigaba da sabga ko hukunta Nura batayi ba, sede Bata San shima ya karba auren Nura wajen Harith ba, Wanda shima Dan wani kusar gwamnatin tarayya ne, ya manta da cewar Yar shi akwai alkawarin aure Akan ta. Kowanne bangare shirye shirye kawai suke, aka hada lefe tas aka Kai gidan kawun Nura kamar yadda Ummiey tace, duk abinda ta nema wajen Alhaji Mustapha na aure zai bayar beyond request din ta, se tayi tunanin maganar ta wuce, Nura aka karba lefen ta gidan kanin Baban ta daban da wancan. A family kowa is confuse saboda wasu sun samu labarin lefe biyu aka karba na Nura, idan aka Masa magana yace Bai San zance ba, itama tace daya ne Bata maida hankali akan komai ba.
Seda biki ya rage kwana biyu, Al'amin ya fadawa Mummy event daya ba zaiyi ba zai dai je saurin aure Amma maganar wani dinner ko wani Abu Bata taso ba. Se ta rabu dashi Dan tasan yayi matukar kokarin Yi Mata biyayya Bata son ta Kure hakurin shi, a bangaren Hajiya Attine, daga inda aka saya furniture yasa sukai Abuja, ya zaba kannen shi biyu yace suje suyi jere, a lokacin Attine tayi sensing abinda ke faruwa, hankalin ta yayi masifar tashi ta samu Nura a daki tana sorting invitation, dama ta Dade da daina saka uwarta cikin hidimar bikin ta, ko kayan da zata saka kanwar baban ta ta zaba mata komai da komai, ta siyo Mata ta Kai Mata dinki, ta dauki card daya ta kalla
Harith&Nura
Ta kalla Nura, ta Kara kallon katin kawai se ta dauke ta da Mari tace
" Ni Zaki watsawa kasa a idanuna, ni Zaki juyawa baya Nura, ni Zaki yiwa Haka, ni Zaki kunyata"
Ta tashi ta zauna tana dawowa daga shock din Marin da ta Mata tace
" Ummiey bana son shi, baya Sona kinki ki gane, na fada Miki, nayi Miki magiyar kinki ji, ya zanyi Ummiey? Dole na nemawa kaina mafita"
Ta Kara marinta tace
" Banyi Miki Baki ba..."
Se Kuma tayi shiru ta fice, bibbiyu take taka staircase cikin mummunan tashin hankali me zata fadawa Hajiya Nafisa? Me zata fada Mata biki saura kwana uku? Innanlillahi wa inna ilaihil rajiun! Wannan Abu da tashin hankali yake, Yana zaune ta banka kofar ta shiga ya dago ya kalleta tace cikin karaji
" Haukacewa kake so nayi? Me kake nufi ka karba auren Nura Bayan kasan akwai wata maganar a kasa? Ya kake so na fada musu har lefe na karba, sun kawo key din gidan su Dan nayi jere sede Naga Fatima ta turon video an Gama jere, kamun adalci kenan? Wannan shi ne takamar Yar ka ce?"
Yayi dariya yace
" Ai nayi tunanin a matsayin ki na uwarta Zaki iya aurar da ita, Attine na fada Miki ki warware maganar har yanzun kina da sauran lokaci"
Ta juya ta fita, ta koma dakin Nura tace
" Kije ki roki baban ki ya Bari ki aura Al'amin"
Nura taji Babu dadi ganin mahaifiyar ta a Haka, to Amma Haka take musu she's a pro a wajen matchmaking, duk Wanda yayi aure a gidannan to Hadi ne, she never like that idea ta dauki alwashin rusa abin. Tace
" Ummiey bazan iya ba, kiyi hakuri ki fada musu tunda wuri"
Ta gyada Kai ta fita Babu Wanda yasan me ya faru Haka ta wuni a daki, se ta dauki waya zata Kira Mummy se ta kasa, se ta buga hannun ta akai, Bata taba kawowa Nura da Baban are this capable, se can ta Kira kawarta a Zaria ta fada Mata duk yadda abin ya faru, wani lokacin mu Mata tunanin mu baida da saiti
" Ki bar kasar kawai, ki bar musu kasar suji kunya, idan komai ya lafa se ki dawo"
Ummiey tace
" Anya kuwa Samira? Ya zanyi da Nafi?"
Tace
" Itama kwadayi ya sata yin hakan, se ki Bari idan sunje gun daurin auren taji labari"
Ummiey dake neman mafita kawai ta dauka kayan ta bada kudi me yawa aka Bata ticket ta bar gari if only tasan hakan zaiyi sanadiyar rasa rayuwa da batai hakan ba.
Ranar daurin aure mutane da Wanda aka gayyata da Wanda sukai niyyar zuwa gayyar sodi duk suka Isa venue din, karfe goma ne jikin card din Kuma shi ne maganar da sukai, Al'amin ya Yi kyau cikin wata farar shadda me maikon gaske, yayi kyau dukda fuskar shi Babu annuri ko digo, Yana fata Unaisa ba zata ji labari ba, yasan she'll be heartbroken, tunda ya samu labarin still tana cikin damuwa, Mummy tayi kyau sukai hoto har Baba kafin su wuce, Baba a mota Yana ta Masa fadan ya saki ran shi ya kaddara Haka Allah ya tsara, yace Masa
" Aminu za kaga daidai, ko bayan Raina rayuwar ka ba zata lalace ba saboda kayiwa mahaifiyar ka biyayya, na tabbatar komai zai zo maka cikin sauki da albarka"
Se hawaye ya fara sauka idanun Al'amin yace
" Baba Ina son ta har yanzun, Baba ta rame duk saboda ban aure ta ba..."
Baba ya riko hannun shi yace
" Ka manta Koda na yau ne, ka daina kuka maza basa kuka ko meye zai faru, idan ta ganka a Haka zata ce itama ta fasa ai Banda abinka. Ka share hawayen ka"
Da Haka Suka Isa gurin jiran gawon Shanu, har awa ta wuce Babu labari kowa ya kosa, Al'amin ya sunkuyar da Kan shi Yana Jin korafin mutane musamman na waje da Rana ke dukan su, Baba ya dubi kanin shi yace
" Ka Kira waliyinta kaji, ko meye kada a wulakanta mutane"
Nanma shiru Babu amsa, Bai ma dauki wayar ba, se Al'amin ya dubi Baba yace
" Mu tafi bazasu zo ba"
Baba ya kalleshi yace
" Ya akai ka sani"
Se lokacin ya tuna maganar Nura da Kuma kallon da baban Nura yayi Masa ranar da yaje da ya fada Masa aikin sa. Wani acan gefe ya matso yace da Baba
" Ni abokin baban ta ne, wannan invitation din na samu, yanzun naji labarin ai suna can fada ana daura Mata aure da wani. Kayi hakuri ka sallami mutane"
Gurin gaba daya ya hautsine, maganganu iri iri na Allah wadai da dangin amarya, Baba ya kasa tashi Yana kallon mutane na ta barin gurin suna jajanta Masa, Haka ma Al'amin hi yake kamar zuciyar shi zata fito, wannan shi ne jiran da Nura tace yayi Mata, shi ne turning tables dinta? Seda kusan kowa ya fita suna zaune lukman yazo da wasu makusantan su suna Basu Baki, Baba ya mike Yana fadin
" Shi ne abinda Nafi ta zabar Mana ai!"