← Book details Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 78

Sashe 74

Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan nan mukai komai yadda ala'ada da addini ya tanadar, na dauki wayar shi da tawa nayi plugging dinsu a caji, sannan na karaso gadon da ya riga ya kwanta, na kwanta gefen shi Ina daura kaina saman broad chest dinsa, dukka mukai shiru Babu me magana, duniyar ma gaba daya tayi shiru gani nake kamar mu biyu kawai muka rage, ya saka hannun shi ya janye hular kaina, tare da zare band din, a hankali ya fara min abubuwan da suka saka na kasa resisting din Shi and we went together into lalaland...

Yana bacci na tashi nayi wanka sannan na dakko dryer na fita zuwa dayan dakin na kunna na drying gashin tas sannan na dakko wani skirt da riga na atamfa, I can't wait kamar wancan karon da na ki Masa kwalliyya yazo ya rasu kullum Ina saka manyan kaya, to wannan karon a waye nake. Nayi kwalliyar sosae wadda na tabbatar se ya Yana sannan naje kitchen na hada Mana abinci, Ina cikin aikin naji motsin shi , kafin na juyo naji an rungume ni Yana shinshina wuyana, I moan a bit yace

" Kin barni ni kadai'

Nayi murmushi nace

" So nake kayi bacci da yawa!"

Yayi murmushi da nake jin sautin shi yace

" Kin sani farin ciki, I even cried of joy, na tabbatar alakar mu is never a bad idea, Ina fatan kin zame min sanyin idaniya har karshen rayuwar mu"

Nace Amin sannan ya sassauta rikon ya juya ya fita, na Dan juya Ina murmushi na dubi bayan shi na Kara godewa Allah, Al'amin was all I wanted Kuma gashi I've him amidst my fingers. Na fito da komai na same shi daki ya gyara gadon, da mopping stick hannun shi Yana mopping, na zuro kafata kenan yace

" Babes kada ki shigo ki taka min mopping Dina"

Nayi murmushi Ina kallon shi da mamaki, na kunna Masa fan nace

" Ka kawo nayi kaji"

Ya girgiza Kai yace

" We're sharing duties, you cook I clean the house"

Seda ya Gama yayi wanka sannan muka ci abinci which was romantic cin, tare mukai wanke wanke Yana wankewa Ina dauraya da kifewa, muka Gama tas ya shafa min ruwan hannun shi a fuskata,na zumbura Baki nace

" Ka Bata min kwalliyya ta"

Yayi min gwalo ya fice, na kwalla masa Kira nayi dariya nace bamu Gama ba fa! Bai dawo ba ya kyaleni, na goge gurin tas na shanya duster sannan na fita na sameshi Yana kallo, na zauna muka fara Hira.

A cikin sati daya ba karamin sabo mukai dashi ba, idan kazo gidan mu se kaji soyayyar da muke da yadda zaman mu yake ya burge ka, idan ka tafi se mun tsaya maka a Rai. Na tashi daga zaunen da nake nace Masa

" Cànîm me zamu ci for dinner"

Yace

" Ina ruwanki, Naga dai yau girkina ne"

Na koma na zauna nace

" I'm sorry!"

Ya janyo ni jikin shi yace

" Muje muyi tare"

Muka Mike zuwa kitchen tare mukai girkin muna Yi Muna Hira ko Kuma Wasa, se naji knocking, na dauraye hannuna nace

" Lemme check"

Yace min to, na dauki Abaya na saka sannnan saman 3 quarter na Jeans, rigata sleeveless me hoton butterfly a jiki, dama kaina Babu dankwali, saboda yadda yake son gashi, I make sure na zauna a Haka Dan yaji dadi. Na fita, tun daga Hanya nake jiyo maganar Jr, nayi saurin karasawa na bude musu kofa, suna tsaye Jr Alby da Kuma iyayen su, na tsugunna Suka taho suna fadin Ommaah, na rungume su a jikina, Ahmad yace

" Zamu shigo"

Nayi dariya Ina mikewa nace

" Sannun ku da zuwa, sannun ku"

Muka shigo har cikin parlor, na Basu guri Suka zauna, sannan na shiga kitchen Dan Kiran shi, Yana tsaye da laddle a hannun shi nace

" Su Alby ne Suka zo"

Da Kan shi ya dakko plates da cups muka fito, Nuzla ta fara dariya tace

" Yaya Al'amin Kai ne da girki"

Ya mikawa Ahmad hannu Suka gaisa yace

" Ke Baban Alby baya Taya ki aiki?"

Tayi dariya Ahmad yace

" Kun burgeni!"

Tare mukai dinner dasu, duk inda yaran sukai Ina kallon su.

Unaisa is not free, pay N300 to 3091721807 Aisha kwalam Hassan and send evidence of payment to 09063467258.*Ending...*

Da sassafiyar jumaa Bayan munyi sallar asuba Muka koma muka kwanta, Amma ni banma Yi wani enough bacci ba saboda hankalina baya tare Dani, Yana kitchen Kan aikin da na sawa zuciyata zanyi, Dana tabbatar yayi bacci na fito zuwa kitchen, na dakko kaza a freezer na daura a wuta sannan na fara kokarin gyara gidan, zuwa lokacin na kammalla sulale na soya, na wuce zuwa store na cika bucket dam da kayan gara sannan na fito dasu na aje, na dakko katon warmer na juye stew din da nayi da daddare na kawo inda sauran kayan suke, Ina tsaye rikeda kuguna Ina tunanin abinda ya kamata na karayi, a lokacin ya fito Yana sanye da short da vest, ya kalleni yace

" This is cheating!"

Nayi dariya Ina kallon yadda yake throwing daggers daga idanun shi, na karasa ta Bayan shi na zuro hannuna ta bayan shi zuwa cikin shi nace

" Of course not, jiya Haka Kai min"

Ya harareni sannan yaja hannuna muka tafi mukai wanka, muna fitowana dakko karamin akwatin na fara Ciro Kaya na da nashi Ina zubawa, ya rike hannuna yace

" Wai kwana zamuyi idan munje?"

Na kalleshi ya tsatsareni da idanun shi nace

" To da me zamuyi? Se Monday zamu dawo ai"

Ya bubbuga kafafun shi kamar karamin yaro na tsaya Ina kallon shi with so much affection a idanuna yace

" Dan Allah mu dawo yau"

Na girgiza Kai nace

" Seriously se Monday"

Ya girgiza Kai yace

" Ai shikenan yadda Kika ce"

Nayi Masa murmushi Ina cigaba da hada kayan, ko tayani baiyi ba, har na kammalla na dakko Masa Kaya na Taya shi ya shirya sannan na shirya Nima, ya saka min dankunne da sarka, muka fito zuwa parlor, breakfast mukai sannan muka dauki Hanya. Tunda muka dauki hanya muke Hira har muka shigo kano, direct gidan Mummy muka nufa Dan shi ne makasudin zuwan namu, a waje yayi parking na dauki jakata muka Shiga ciki, gidan shiru kamar Babu kowa Haka, Amma a parlor muka same ta zaune da katon hijab, da sallama a bakin mu muka Shiga, ta mike tsaye tana murmushi tana Mana lale marhaban, na Kara fadada murmushi na lokacin da ta hada mu ta rungume mu, Bayan ta sake mu na durkusa na gaishe da ita, ta amsa sannan na zauna tana Kara tambayar yadda muke, ta mike ta shiga ciki, na dube shi nace

" Muje mu shigo da kayan ko?"

Yace

" A'a ki Bari Zan kawo"

Nace

" Zaka iya?"

Ya harareni nayi dariya Ina Masa gwalo, ya mike ya fice se gata ta dawo tana fadin

" Me zaku ci for breakfast? Gidan ni kadai ce se lukman shi Kuma ya fita ma"

Nace

" Munci abinci kafin mu taho, sede Bari yazo ko zaici abinci"

Ta gayda kanta, Sega sallamar shi ya shigo da trolley da bucket, nayi sauri na mike na karba, na karaso dasu ciki ya juya ya kawo sauran, na dubi Mummy nace

" Mummy stew ce wannan ko Ina zaa juye ta?"

Duka suka dubeni a tare, Mummy tace

" Stew kikai, sannu Allah yayi Miki albarka"

Nayi murmushi nace Amin, shi Kuma yace

" Yaushe kikai bansani ba"

Ki kulashi ma banyi ba, ni na juye mukai ta Hira da ita, wajen azahar zaije masallaci tace ya dauki kayan mu ya Kai Mana can, sannan ya rakani Naga dakin. Muka fito tare dawowar lukman kenan, ya karaso ya bugi kafadar Al'amin yace

" Ango ango!"

Nayi murmushi Ina kallon su, ya juyo ya dubeni muka gaisa sanann muka karasa, dakin shi ne na da, Suka fita na gyara ya danyi kura kadan sannan na dawo na samu Amra da Maman Akram sun zo. Ranar Haka Muka wuni, suna da kirki sosae koma wanne makami ne hannunta to yasar dashi. Washegari mukaje yawo gidan Anna, gidan Abba da gidan Mamaa, kowa a cikin su idan ya kalleni yasan hankalina a kwance yake, yasan Ina cikin Jin Dadi da farin ciki. Anna kamar zata maida ni ciki tayi nan tayi can, Dan nan na yini. Bayan maghrib yazo mu tafi muka biya gidan Aunties dinsa guda biyu. A Hanya na gaji nace

" Muna zuwa zanyi wanka nayi bacci Allah na gaji, duk ka kaini yawo"

Ya dubeni yace

" Ni gida uku nace muje ke Kika dinga janmu yawo, Kuma gaskiya I need you, ki hakura da baccin"

Nace

" A'a!"

Yace

" Ni din?"

Na gyada Kai, se ya maida hankalin shi Kan titi, Muna zuwa gida Mummy ta Gama abinci, na zauna na zubo sannan na fara ci, tana ta tambayar mu yadda muka baro kowa, na Bata sallahun gaisuwar su Ina gamawa nace

" Mummy bacci nake ji"

Tace

" Karki kula shi wuce kije kiyi kwanciyar ki ya zauna hira"

Na wuce na Mata sallama, Ina jin hirar su a bakin gate, makwabcin su ya tsare shi da magana nima se fitowa nayi na shigo, kafin ya dawo har nayi wanka na shirya, na kashe wuta kenan se gashi Ya shigo, ya kunna wutar na bude idanuna na kalleshi nace

" Ka Gama?'

Yace

" Shi ne Zaki kwanta ban zo ba, Mummy tace har kinci abinci ma"

Na Dan tashi na zauna nace

" Cànîm to ka tsaya Hira, I was very sleepy shiyasa"

Na nuna Masa gefena alamar yazo ya kwanta ya girgiza Kai irin yayi fushi dinnan! Nayi murmushi na mike na janyo shi ya zauna nace

" I missed you!'

Na fada Ina hade bakina da nashi, I wasn't in the mood sosae but he said it and I wanted to support him sosae, se da mukai wanka Dana kwanta inaga ki juyi banyi ba se asuba!
Chapter 74 · 0% Book details