← Book details Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 78

Sashe 67

Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Se Muka bar maganar har yamma sannan suka tafi, sun min siyayyar foodstuffs sosae da Kuma kudi. Na Kira Mamaa na Mata godiya, na Kira Abba har da Anna na fada musu. Ranar Monday Ina zuwa da kyar na karasa asibiti saboda ciwon ciki da Kuma kaikayi a palms Dina da foot dina, dukka kaikayi suke min fin sati biyu nayi medication Amma Kuma yayi failing Dan farko nayi tunanin allergy ne, Ina shiga na samu na zauna, matron tazo tace

" Unaisa ya jiki jiki"

Ina dagowa muna hada idanu tace

" Subhannallah are you sick?"

Na gyada Mata Kai, ta tambaye ni symptoms din na fada Mata tayi shiru tace

" Ya fitsarin ki?"

Nace Mata ai it always dark tunda na fara having symptoms Kuma nasan Ina Shan ruwa sosae bazaiyi ace dehydration bane. Se kawai tace na shiga na kwanta, Zuhra duk hankalina ya tashi Bayan sunyi magana da Matron, nace Mata

" Wai menene? Wani abun ke damuna?"

Ta zauna tace

" Kin tuna cholestasis ko?"

Nayi shiru wanting to recall, se na mike na zauna nace

" Hakane Zuhra I'm having those symptoms. OMG !"

Na shafa cikina, yawancin Yana zuwa a mace daya cikin Mata dubu da suke da ciki, se ya zamana ni ce daya a cikin dubun, Bai fiya zuwa a cikin farko ba yawanci na biyu ko dai mabiyan sa, ciwon kamar na hanta me Wanda ke zuwa a karshen ciki, wato third trimester. Jikin mutum zaiyi yellow ko ido saboda madaciya da tayi yawa baa amfani da ita yadda ya dace, akwai ciwon ciki, fitsari zaiyi duhu Haka tafin kafa da hannu zasu ta kaikayi, mostly zai zo da kasala da rashin son cin abinci, Kuma yawanci is a threat to the fetus wato yaron cikin, zai iya mutuwa ko Kuma a samu birth complications. A ranar kusan Matron duk aikin akai na ya Kare, duk test din da ya kamata seda nayi sannan ta rakani akai reviewing akai confirming shi ne, gashi yaron are in distress already. Likitan ya kalleni yace

" We've to save you and the babies ko Kuma ke ko Yaran"

Na kalleshi nace

" Save the babies, ko da na mutu Babu matsala, Dan Allah induce me na haife su"

Ya Kara kallona yace

" You're asthmatic, bana tunanin zamu dauki risk din inducing din ki"

Na dunkule hannuna wata zufa na karyo min, Kuma hakane mussamman yadda na dinga samun attack Bayan cikin ya tsufa akai akai. Wannan shi ne tsaka me wuya!

Unaisa is not free, pay N300 to 3091721807 A'isha kwalam Hassan first Bank of Nigeria and send evidence of payment to 09063467258.
[6/27, 10:41 PM] Hauwa Galadima: *E³*

Na fito daga office din idanuna duk yayi zuru zuru ga damuwa da ba ma se an fada ba, na dubi Matron Dake nace Mata

" Mummy am going in for emergency CS"

Ta gyada kanta tace

" Shi ne ya kamata, ki kwantar da hankalin ki is not something bad, Kuma kinsan idan Kika tada hankalin ki jinin ki zai iya Hawa"

Idanuna Suka ciko da kwalla, na shiga uku! Wanne irin rayuwa ne ni Unaisa nake ciki? Na gyada Kai na nace

" To Mummy, ki Kira min Zuhra"

Dama jiran kiran namu take, ana Kiran nata kuwa se gata tazo, ta zauna gefe na tace

" Na Kira Abba ya taho shi da Yaya Ahmad, Amma ba Wanda na fadawa Bayan shi kuma"

Na gyada kaina bana son su daga hankalin su, kafin Abba su karaso anyi admitting Dina an Kara reviewing dina,abinda ya rage anaesthetist review ne kawai. Ina zaune da waya hannuna Ina fadawa Zuhra inda wasu kayan suke se naji kamar maganar Al'amin a nurses station, ban ma kula ba na cigaba da abinda nakeyi, na gama wayar Dan bana tuannin a kayan haihuwa idan ka dauke kayan Yara na mace ko namiji, Babu abinda ban siya ba, komai pair na siya unisex, banyi wani blue ko pink ba, kawai milk da brown ko coffee na siyo. Zuhra ta Kara Kirana tace

" Ashe Baki da mutunci ban sani ba, twins Zaki Haifa nake ganin komai pair?"

Na girgiza Kai Anya Zuhra Bata shaye shaye kuwa? Nace

" Ke Baki da Kai, yanzun time din da Zaki dinga min wannan tambayar ne? Ke Kika sani"

Na kashe wayata, Allah ya bani lafiya nasan bashi naci tabbas. Ina aje wayar ya shigo da folder ta a hannun shi, na gyara zaman mayafin jikina har ya karaso, fuskar shi da damuwa amma Kuma Yana nan yadda na sanshi, Dan gayu me tsafta, sede min kai wata biyu bamu hadu dashi ba, Bai neme ni ba Nima Kuma Haka. Ya janyo kujera ya zauna Yana fadin

" Unnie sannu! I don't know se yanzun akace min nazo nayi reviewing zaayi emergency CS"

Na gyada Kai Ina fadin

" Thank you!"

Da kanshi ya duba vitals Dina, duk abinda ya dace yayi sannan yace

" Saboda condition din ki Zan Baki spine, I'll be with you ki haifi farin cikin ki, saboda har yanzun ke din farin ciki nace"

Na lumshe idanuna bance komai ba, ya dauki file din yace

" Karki tada hankalin ki, you'll be safe Inshaaa Allah!"

Ganin shi cikin team din se naji hankalina ya Kara kwanciya, naji kamar irin I'm safe dinnan. Bayan kamar minti shida Abba yazo da Ahmad da Dada, Ahmad kafin ya shigo yayi signing consent, Abba ya zauna bayan mun gaisa yace

" Na daina magana, idan aka fito se muyi magana"

Gani yake da zarar nayi magana ko zanyi kuka jini na ya hau, nima Ina son nayi kukan, Ina tuna Abiey ace dai Yana da Rai ake wannan abin? Da tabbas zance ya canja da tuni Yana ta safa da marwa may be hankalin shi bazai taba kwanciya ba, na Kara shafa cikina, Babu jimawa aka zo aka saka min cannula da komai aka tura ni zuwa operating room! Duk sun Zama ready ni kawai ake jira, ana zuwa nayi addua wadda Bata dauke daga bakina ba, seda na shiga na fara tunanin idan na mutu banyi magana da Anna ba fa? Ya kamata ace nayi waya da ita kafin a Fara, but it was too late hakan. Al'amin ya bani spine kamar yadda yace min, ya cigaba da monitoring vitals Dina, Ina jin hirar su Amma bana Jin zafi gaba daya an kashe jikina numfashi kawai nakeyi se blinking idanu, baifi mintina goma ba aka Ciro daya, sede Babu kuka, Al'amin ya mike Yana fadawa midwife din da tazo tayi resuscitating Babyn, can ya mike ya saka wata gloves ya karba, aka ciro na biyun shima Babu kuka, zuciyata kamar zata daina aiki Haka nakeji, Babu damar na dago na kalle su. Amma can naji sun fara picking, Ina jin kusur kusur din su se naji wani sanyi ya mamaye min zuciyata, na dinga hamdala cikin zuciyata. Da aka Gama aka fito Dani yaran tuni anyi gaba dasu Dan ayi warming din su, bacci a hankali ya dauke ni. Nafi awa uku Ina bacci dab da maghrib na farka, na Dan motsa hannuna se naji ya motsa Haka ma kafata nasan tabbas allurar ta sakeni, na fara kokarin tashi,naji wani ciwo na cije Baki na. Na tashi na zauna, Zuhra ta shigo tana ganina a zaune ta koma se gata da Anna da Kuma Dada sun shigo, Anna ta rungume ni tana fadin

" Sannu Adda! Sannu kinji"

Nayi murmushi nace

" Yaushe kuka zo?"

Dada ta dinga jera min sannu kamar zasu maida ni ciki. Aka dakko yaran aka bani dukkan su, an musu shiga iri daya, na karbe su Ina jin kamar na tsaga kirjina na maida su, bacci suke peacefully na rungume su na saki kuka

" Da tuni Yana nan, da tuni Yana murna zai dauke su, gashi sunzo Basu da uba ma..."

Nayi ta kuka Kuma Wai Suka kasa rarrashi na, seda nayi me isata sannan Dada ta karbe su ta cigaba da bani Baki. Being a mother is joyous, Haka na kwana banyi baccin kirki ba, gani nake Dana farka zaa sace su, ko Kuma na tashi Naga mafarki nake, se asuba aka hada min ruwa nayi wanka sosae sannan na dawo dan sunce nayi ambulating, na gayra jikina se na tuna na Gama idda, nayi murmushi Ina sakin alhamdulillah a Baki na. Suma akai musu wanka nayi feeding dinsu naci abinci na kudundune. Ko Yan unit dinmu da suka zo bacci nake Yi, se Sha daya na tashi shima kukan daya daga ciki naji, na tashi na zauna na karbe shi, dukkan su maza ne identical ma kuwa, naji kowa na fadin Kama suke da Ahmad Wanda ya tabbatar da kamar su daya da Abiey kenan! Na rike shi a hannuna Ina kallon fuskar shi, hannun shi dan mitsitsi cikin nawa, idanun shi a rufe Amma Kuma sucking yake, shigowar Mamaa, Bilkisu, Badi'a da Aseey yasa na gyara zamana Ina cije Baki, Dada ta shimfida katon carpet tana musu sannu da zuwa, Mamaa ta Karbe su suna tayi min sannu na sakko muka gaisa, na dingisa toilet na gyara jikina sannan na dawo muka gaisa, Mamaa ta bude flask ta zuba min abinci ta Miko min, Aseey ta hada min tea me kauri nasha sannan muka fara Hira, kowa se yace ai na tsoratar dashi. Se dare dakin ya lafa, daga ni se Dada se Baba Asabe, kowa ya tafi naci abinci Ahmad ya kirani a waya muka gaisa yace

" Wanne sunan Kika zaba musu? Ko na zaba Miki?"

Ya fada Yana dariya, nace

" Eh tunda Kai ka haihu ba"

Yayi dariya yace

" God ya kamata nayi aure an fara min gori"

Na kalle yaran cikin cradle Ina murmushi nace

" I'll name them after Abiey and Abba!"

Yayi shiru yace

" Nayi tunanin sunana Zaki saka musu, tukwicin abokan ta"

Na harara wayar nace

" Kai ka sani,gwara kayi aure ko ka samu ka Yi ma kanka takwara, by the way ka fadawa Abba decision Dina"

Yayi musu addua sannan na kalla Dada Bayan na aje wayar nace
Chapter 67 · 0% Book details