← Book details Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 78

Sashe 21

Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali na fara lalubo inhaler ta daga cikin jakata saboda yadda nake jin numfashi na na sarkewa, dama I was expecting attack din yazo saboda I was super tired bayan dogon lokacin da mukai a tsaye ward rounds da Yan blue team, suna fita white team Suka shigo, min Gama muka fada wound care, bayana tamkar zai balle Haka nakeji, ga banci abinci ba saboda na kusan makara ga Kuma Raina a bace yake bansan meye dalilin ba. Na Dan fara puffing Amma naji kamar zuga ta nake, hakan ya jawo hankalin chief da sauran staff din dake gurin, kafin a Gama hada kayan tuni na galabaita bansan me yasa kwata kwata asthmar nan is not on my side Kuma Bata favoring Dina ba, indai zata tashi to se Nasha wahala, shiyasa mutanen da suke da muhimmanci a rayuwata bayan family Dina da suka kafa Kan su cikin rayuwa ta dukka a dalilin asthma na hadu dasu. Are you curious? Continue reading 😁

Bayan na dawo daidai Amma har lokacin wannan makakin Bai bar wuyana ba idan banyi Wasa ba se nayi kwana biyu Bai daina ba. Chief din mu yace

" Take this to your clinical preceptor so that you can go home and rest"

Na mike na amsa short note din da ya rubuta har lokacin akwai weakness a tare Dani, na Masa godiya na karba zuwa SOPD inda anan ne work post din shi. Seda na tambaya colleagues Dina na gurin Suka ce Yana office tare da bako, ban wani damu ba na wuce nayi knocking softly a kofar, sannan na Murda knob din na Shiga bakina da sallama, su biyu ne a zaune suna facing juna, Wanda yake matsayin bakon an aje Masa kwalin chi exotic na mango har raba ke sauka a kwalin, se naji kamar na sunkuci kwalin na daddaka saboda zafi da Kuma ranar da akeyi. Idanun su dukka a kaina har na shigo na gaida su, preceptor yace

" Remind me your name"

Nace a hankali

" Unaisa Yahya!"

Ya gyada Kai yace

" Yeah Unaisa! Ya akayi?"

Na kalleshi sannan na kalli bakon Dake wani sly smile Yana danna wayar shi, da daya zakuyi tunanin cewar baya sauraren mu nan kuwa hankalin shi da idon shi akaina suke. Na Mika Masa paper bayan ya karanta se yace na zauna ya fara tambaya ta meye triggers Dina, na fada Masa Wanda na fahimta se ya tambaye ni drugs din da nake using, nan ma na fada Masa se yace naje gida zuwa Thursday na dawo, na Masa godiya Bayan yayi min kashedin kula da kaina. Har na rike knob Zan fita naji murya very deep and silvery yace

" Se ka karba contact dinta yadda zaka Kira kaji jikin nata ko?"

Na juyo na kalle shi, bakon ne yayi magana, hakan yasa preceptor yace

" Sure kayi magana Aminu! Oya bani contact dinki"

Na dawo Ina Dan pouting bakina na fara karanto Masa

" 08029........62"

Ya gyada Kai na fita bayan nayi glaring bakon da hankalin shi ke Kan waya, wa yaga harara a duhu. Bayan na fito na samu Zuhra a tsaye, har an fada Mata kenan, ta riko hannuna

" Ashe bakida lafiya Baki fada min ba! Ya kike ji"..

Nayi murmushi, idan aka bi diddigi zaaga Ina daya daga cikin weakness din Zuhra

" Na ji sauki, kawai gida Zan wuce"

Tayi saurin cewa

" Yafi Kam, na Kira Yaya Ahmad he's on his way!"

Yana zuwa muka wuce gida, ya bubbude windows sannan yace

" Ya kike ji?"

Na Dan kalleshi he looks disturbed, nace

" I'm fine! Naji sauki"

Ya gyada Kan shi, bamuyi nisa ba ya tsaya wani katon pharmacy yayi excusing Kan shi, Bai Jima ba se gashi ya dawo da Leda, ya daura min akan cinyata yace

" Ga drugs din, sannu"

Na kalleshi nace

" Me yasa kake Haka? Kana takura kanka fa?"

Ya harare ni yace

" Da gaske? Wait! Tunda Zaki iya magana ma, can I know dalilin da yasa idan na Kira bakya dauka?"

Na danyi shiru har seda ya Kara maimaita min sannan nace

" Kawai kowa Yana cewa Wai sona kake"

Na fada Ina kawar da kaina,sure nasan nayi wauta, yayi dariya yace

" Unaisa to idan da gaske ne fa"

Na Yi saurin kallon shi nace

" Haba dai?"

Se ya Kara dariya yace

" Ina sonki! Amma bawai na aureki ba, kawai Ina Miki sister love ne irin nasu Aseey da Zuhra. Ni ban Kai auren ki ba, ai mijin ki namijin duniya ne, seya Tara Dan ke dinnan matar manya ce"

Nayi dariya, though I was a bit disappointed, Amma Kuma se naji ba wani damuwa sosae tunda dai ba so din bane. Mukai ta Hira har muak je gida, Anna se gani na tayi kamar an wullo ni, tana ganina tasan banida lafiya ko yadda fuskata tayi, nayi wanka ta Kara hada min magani Nasha naci abinci se bacci Bayan ta kunna min rechargable standing fan.

Da daddare Sega Dada da Zuhra da Yaya Man har da Aseey sunzo duniya, tun maghrib Suka zo har bayan sallar ishai, zasu tafi muka rako su, Yaya Man ya Dan yafito ni gefe na bishi, yace

" I need your help"

Na kalleshi confusingly nace

" Me ya faru?"

Yace

" Karki bacci idan na koma gida Zan Kira ki"

Ok na manta na fada muku Badi'a da Yaya Man na soyayya, da farko bamu gane ba, Dake Nuzla da Zuhra have something in common wajen saka idanu su Suka fara harbo jirgin su, da suka fada min ko kadan ban yadda ba, nace sun Shiga uku Amma se daga baya na rutsa ta a daki ta dauki wayata tana waya dashi, nayi kamar ban ganta ba se da ta Gama sannan na dawo dakin, na Bata hannu alamar ta miko min wayata, ta kuwa bani Babu musu na zauna nace

" Ina jinki"

Ta Dan dirirce nace

" Badi'a fada min meye tsakanin. Ku, I've been watching you closely"

Ta marairaice fuska tace

" Allah Adda..."

" Kinga Badi'a ni ba hanaki zanyi ba idan son Shi kike,ni Zan goua Miki baya amma idan kika min karya ya kike son na Kare ki wajen Anna da Dada?"

Se ta fara fada min wai abin ya faru shekara daya data wuce, yace Mata Yana son ta ita kuma se taki ganin ni bana ma tsayawa da samari, to baayimin aure ba balle Nuzla har a gangaro kanta. Na Bata shawara in har tana son shi she should carry on. Ranar da Anna ta gane se akai rashin saa Ina hadejia, ta Kirani jikin ta a sanyaye Wanda na gane hakan daga muryar ta tace min wai Badi'a soyayya take Man yayi blowing maganar, se na nuna Mata Badi'a is seventeen, ta Gama secondary, admission list muke jira kawai mu gani, nace

" Anna ki barta tana son shi, Kuma Yana sinta shima"

Ta girgiza Kai tace

" Adda nawa Badi'a take, munafurta ta take kenan?"

Na Dan kosa da maganar nace

" Anna addini Bai Hana ba, alada Bata Hana ba, ki barta Dan Allah"

Se mukai sallama a Haka, kullum maganar ya tashi tana cutawa, dukka kowa yayi tunanin Wasa ne se yanzun da aka concluding zaayi bikin Muhammad brother Ahmad da bilkisu, ga kuma Aisha Baffa saboda saurayun ta ya jira da yawa , se aka hada na Zuhra da Yaya khalifa, shi ne Yaya Man shima ya roki Abba a hada dashi da Badi'a. Anan battle din ya fara.

Bayan sun tafi na koma daki na kalla Badi'a wadda ko rakiyar Bata fito ba, kwana biyu na lura tana cikin damuwa, nayi tambayar duniya tace ba komai, na tambayi Anna tace na rabu da ita. Idanun ta sunyi jawur alamar tayi kuka nace

" Badi'a ni ce fa Adda dinki, meye bazaki iya fada min ba"

Se kawai ta rungume ni ta fara sheshekar kuka, hankalina se ya tashi na dubi Hunainah nace

"Kira Anna"

Se tayi saurin girgiza kai Wanda ya dakatar da Hunainah, ta mike ta shiga toilet, na bita da kallon mamaki, wayata dake jikin socket ta fara ringing na saka hannu na janyo ta, Yaya Man ne har sunje gida kenan na ayyana a raina,  na dauka na musu bangajiya da Kuma gaisuwa sannan yace

" Kiyi hakuri da abinda ya faru"

I was confused again nace

" Me ya faru?"

Se ya fara min bayani kamar Haka, Bayan ya samu Abba da maganar se Kuma Abba ya nuna Jin Dadi a ganin shi wannan auren zaiyi strengthening zumunci, Zuhra da Yaya khalifa se Badi'a da Yaya Man. A Daren ya samu Dada wadda shi Abba a ganin shi zata yadda Amma Yaya Man dama ta taba Masa warning akan Badi'a, tace kada ya hargitsa gidan mu, a lokacin se yace Mata ai shi da gaske yake. Bayan Abba ya Mata bayani Dada tace Bata San wannan maganar ba Bata yadda ba, se Abba yace Mata me yasa se tace gani ni banyi aure ba me yasa zaice Badi'a, se Abba ya nuna Mata kowa lokacin Shi ne Amma matar nan tace sede idan ni zai aura. Shi ne yazo ya samu Anna ya fada Mata itama tace abinda Dada tace shi ne daidai.

" To ni Yaya Man ya zanyi"

Yace

" Unaisa wallahi da Zan iya Zan aureki "

Nayi saurin katse shi nace

" A'a Badi'a ita kake so and I'll make sure ka aureta zanyi ma Anna da Dada maganar"

Washegari bayan mun Gama gyara gida Wanda ban saka hannu ba a cewar Anna Ina sick leave ne, na samu Anna a daki tana updating online shop dinta, na kalleta Naga yadda ki karatu batayi ba amma Allah ya buda Mata, tabbas Allah shi ke azurtawa, mudai mun Sha kwana.

Unaisa is not free pay N300 to 3091721807 A'isha kwalam Hassan first Bank of Nigeria and send evidence of payment to 09063467258.

[5/21, 4:40 PM] Hauwa Galadima: *S*

Na zauna na jirata ta Gama updating sannan ta dubeni tace

" Ya akai Adda?"

Nace
Chapter 21 · 0% Book details