← Book details Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 78

Sashe 24

Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali ba tare da na fahimta ba se Al'amin ya.zama someone very close to me, har ya ture kujerar Ahmad. Dukda ni kaina Ina ayyana ba Wai kawance muke ba ko yanayin wayar mu zai tabbatar maka we're confuse, Amma ni dashi min Bari a kawance muke.  Mun kasance komai a kudundune muke yi, a bangare na Babu Wanda ya San shi Dan kumbiy kumbiya kawai nake a buna. Ana Haka posting dinmu ya Kare zamu koma hadejia, kafin zuwan lokacin da zamu koma da daddare Abba da Dada suka zo, ranar ba wuta ga zafi da ake kamar zaka cire kayan ka, damuna ta riga ta wuce kiris ya rage sanyi ya shigo, Ina zaune na kunna lantern Ina saka Mana shawl ni da Zuhra saboda sanyin school. Badi'a na Kan keke tana dinka Abaya Dan ita abinda ta iya kenan dinki, har da ta Gama js3 Anna tasa ta wajen top fashion designers dinnan ta koya dinki, idan ta dinka Abaya se kace ba local made bace. Nuzla na danne danne a waya, idan kana neman matar zuciya ka samu Nuzla kawai ka Gama, donut aka kaita ta koya, physical classes Amma data dawo dukkan kayan se ni ce nake dauka idan Naga wani recipe a ig na gwada, tun Anna na fada har ta rabu da ita, to a hankali Kuma se muka ga tana catching interest a kunshi, tana following yawancin manyan masu zanen kunshi, to shi ne da weekend Anna ta tura ta can wata unguwa take koyo, to ita Bata saka Abu a ranta ba kamar mu ba masu nacin gaske. Tace Mana shi ne kadai abinda zata Mana na gata, Bayan karatu se Kuma Sanaa dogaro da Kai, to hatta Hunainah steps Dina take following tare muke saka da ita.

Sallamar Dada yasa dukka muka aje abubuwan hannun mu Muna Mata oyoyo, ganin ita kadai yasa nace

" Dada ke kadai Zuhra fa?"

Ta tabe baki tace

" Wai ke da Zuhra Baku gajiya da juna, da yaushe kuka rabu? Ni da Abban ku ne a waje"

Anna tayi saurin mikewa tana fadin

" Kuma se ki bar shi a waje Yayah, Adda jeki shigo da Abban ku"

Na mike na saka hijab na same shi a tsaye jikin mota har kasa na durkusa na gaishe shi, da faraar shi ya amsa yace

" Ya asibitin? Har yanzun ko allura baayi min ba"

Nayi dariya nace

" A'a Abba Dan Allah stay healthy! Wanne irin allura Kuma"

Shima yayi dariya yace

" Wai Dan na tabbatar my kids are doing well"

" Inshaaa Allah we'll make you proud Abba"

Daga Haka na bashi sakon Anna muka shigo tare dukka muka gaishe shi ya zauna kan sallayar da na shimfida Masa, daki muka koma Dan Basu guri sui magana.

Unaisa is not free, pay N300 to 3091721807 A'isha kwalam Hassan first Bank of Nigeria and send evidence of payment to 09063467258

[5/23, 10:21 PM] Hauwa Galadima: *U*

Bayan sun gaisa Abba ya dubi Anna yace

" Zainabou tace Wai kin fara siyayya? Hakane?"

Anna ta dubi Anna tace da Abba

" Na fara, Wai amce me kwarmin Ido da wuri yake fara kuka"

Abba yayi dariya yace

" Yaushe fulani Suka iya Karin magana. Amma kinsan Babu Kara ko? Ta yaya Zaki ma Badi'a siyayya?"

Anna tace

" A'a Abba Dan Allah nauyin se yayi yawa Kuma, beside Badi'a ba ita ce Yar ka ba Unaisa ce, Kuma wallahi Zan iya Ina son ma jibi naje Masaya na fada musu su sani"

Abba yace Shifa dukkan mu yayan shi ne Dan Haka komai shi zaiyi Anna Babu yadda zatayi ta hakura da Jan, Danma duk abinda zata siya zance ta siya da Zuhra, to Dole muka tsayar da siyayyar Dada da Anna Suka cigaba.

" Se magana ta gaba! Ya kamata Hassana kiyi aure, ko saboda yarannan"

Dada ta kauda Kai ganin Anna tayi saurin kallon ta, tace

" Abba zamu iya barin wannan maganar Dan Allah"

Yace

" Me yasa?"

Anna ta Dan sunkuyar da Kai tace

" Bazan iya ba Abba, gaba daya na Dade da sarewa, bana Jin Zan iya budewa wani zuciyata, wannan yaran ne kawai a gabana. Abba bazan iya ba"

Abba yace

" Na sani nasan da hakan, Amma akwai Wanda suka ga abinda yafi hakan Kuma Basu karaya ba suka sake gwadawa"

Tayi saurin girgiza Kai tace

" Abba wallahi bazan iya ba, Yahai ya tafi da komai, ka Dan bani lokaci"

Ranar asabar da asuba na idar da sallah nayi wanka, duk ranar asabar nake spa Dina, Dan Haka na zauna na kunna lantern na sahfa fuskata da mask din Dana hada na kunna stop watch Yana kaiwa lokaci na murje sannan na goge da oils kafin na shirya cikin brown din atamfa riga da skirt, na shafa powder ma saka kwalli na lakuta balm a lebena da Suka fara haskawa saboda maikon balm din. Indai a gurin gyara ne I no dey carry last! Karfe shida da rabi Muka bar gida Muka dauka hanyan masaya. Seda na zauna a mota sannan na tuna ban fadama Al'amin min fita ba , nasan anjima idan ya Kira morning greeting yaji na fita zai dinga mita ban fada Masa ba, wani lokutan Ina jin kamar na bashi power da yawa, kamar na sakar Masa yasan dukkan wani Abu dake faruwa da rayuwata amma wani lokacin se Naga ko fita zaiyi he'll text to tell me his whereabouts, dukda Bayan sunan shi da wajen aikin shi da Mummy Babu abinda na sani Kuma, ni ban tambaya ba shi Bai fada ba se kawai na Bari a hakan. Wayata na dakko na tura Masa text Akan na tafi Masaya da Anna! Baiyi replying ba da ya tabbatar min bacci yake. Bayan wajen awanni biyu muka Isa Masaya, Yaya Isa ya tare mu tunda Anna ta sanar dashi zuwan mu. A tsakar gida aka shimfida Mana tabarma hade da salayyu akai Wai muji laushi, Haka mutanen kauye suke su din sun iya karrama mutane Amma idan sunzo birni ba kasafai suke samun karamcin da suke Yi ba. Tea aka fara kawo mana, sannan fanke da aka bade shi da sugar, ga wainar hatsi Tasha karago. Seda muka ci me idar mu sannan na Kama Mata tayi wanke wanke, Yaya Isa Suka shigo shi da Yaya surajo.

" Wallahi kin Zama babbar mace, ance min har Dubai kike zuwa"

Anna tayi dariya tace

" Say daya naje fa"

Ya gyara Zama yace

" Zaki koma ai, inama Inna Zulai na da Rai taga yadda Kika cigaba alheri ko ta ina"

Tayi murmushi tana Mata adduar da Babu ranar da batayi Mata na samun rahmar ubangiji

" Isah yace min wai aure Zaki yiwa Badi'a, nace Masa a'a baiji daidai ba sede Unaisa"

Na maida hankalina Kan Wattpad da nake updating Ina son karanta Fara Yar shehu,

" Da gaske Badi'a ce, zata aura Dan Yaya zainabou Suleiman, ai ta fada muku?"

Yaya Isa yace

" Allah yasa hakane mafi alkhairi, mune ke ganin Dole idan zaai aure se a jere shi Kuma Allah yadda ya tsara daban"

Anna tace

" To ya zaayi, shi ne nazo na sauke hakki na fadawa dangin ubanta idan zasu karba to, idan sunki Kuma Yaya maharazu Yana jira"

Wajen karfe Tara muka nufi can gidan su Alhaji Yahai, a kofar gida Muka tadda shi sun hada majalissa, se musu ake zabgawa tun daga nesa Yaya Isa yace da Anna

" Ga mutumin naki can fa Hassana! Kullum anan yake Zama Yana bin inuwa Babu aikin fari balle na Baki"

Anna ta Harare shi Jin yace mutumin ta, tace

" Isa yaushe ya daina zuwa saudiyya?"

" Yafi shekara biyar fa, Kuma se cinye abinda ya Tara yake, kede kawai wani abun Kar a fada saboda rufe shi din shi ne alkhairi"

Duk abinda suke fada Ina jinsu, nayi tamkar ban ji ba, ya cigaba da fada Mata alhakin mu ne na wofantar da mu da yayi bamu ji ba bamu gani ba, Haka Allah ya ke Babu Wanda yake hukunci daidai kamar shi. Muna karasawa wajen gaba daya tamkar mutuwa ta wuce kowa yayi shiru suna kallon mu, mukai gaba ni da Anna se Yaya Isa da Yaya surajo suka tsaya yin magana da Alhaji. Ciki muka shiga wajen Inna Fiddau, tana zaune dokin kofa ita dinma shekaru sun Kara ja ta Kara yamushe wa duk abin tausayi ma. Da farko Bata ganemu ba seda Anna tace Mata

" Hassanan Zulai ce"

Se kuwa ta saki salati tana fadin

" Hassana yau ban ganeki ba, dukka Kun canja. Akace bakua kasar?"

Tace

" Eh naje na dawo!"

Ta fara Mana lale tana korafin baa zao da takwarar ta ba, ta shimfida Mana tabarma anan rumfa sannan ta fara kokarin a siyo Mana abin karyawa, Kuna son wuce wulakanci? To ku nemi na kanku, kufi karfin kayan mutane, lokacin da muka zo Alhaji ya saki Anna wani wulakanci ne bamu gani ba, hatta nasabar mu seda aka ce mu ba yaran shi bane, to Amma baa je ko Ina ba se gashi table yayi turning, se gashi idan an ganmu jiki har rawa yake, kowa so yake yace Muna da relation, kyautata Mana ake so ayi. Idan da Anna Bata nema na kanta ba bana tunanin zasu karbe mu, Amma yanzun sunsan Basu Isa ba, Babu ficikar su day zata Mana amfani.

" A'a ba se an siyo ba, munci abinci gidan Isa"

" To barka!"

Se ta fara kwalla ma jamaar gida Kira akan su zo su ganni ni jikarta ce, ni Kuma bana uhm bana uhm uhm, hanaklina ba wani a tare Dani yake ba saboda har lokacin Al'amin Bai kirani ba Bai Kuma Yi replying message Dina ba. Duk na damu gani nake kawai Babu lafiya, na kunna data yafi sau cikin kwando Amma Babu message din shi a WhatsApp balle telegram da muke Dan yin chat acan lokaci zuwa lokaci. Shigowar Alhaji da dagaci yasa na aje wayar, Bayan su Kuma kawunnan mu ne Wanda da wuka bazan iya fadar sunan su dukka ba, se Kuma su Yaya Isa da Suka taho dasu. Na gaishe su dagaci yace
Chapter 24 · 0% Book details