← Book details Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 78

Sashe 72

Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Ai Basu Kai three ba Suka fara Haka, Kuma yanzun ko tari nayi se a Fara rige rigen dakko min inhaler, sun masan inda nake ajewa"

Se Naga idanun Nuzla ya ciko da kwalla, na riko hannun ta Ina girgiza Mata Kai, I know she badly wants a baby Amma Kuma na fada Mata hakan ma ai lokaci ne. Min Gama lunch Baba Asabe ta fito tace ana buga gida, taje Bata Jima ba ta shigo tana cemin nayi bakuwa, na kalla parlon komai neatly yake se gata ta shigo bakin ta da sallama, na dago Ina Dan sakin fuska na Mata sannu da zuwa, ta karaso ta zauna, na zauna na gaishe ta Amma ban gane ta ba, Suka gaisa da Nuzla wadda ta wuce ta kawo Mata ruwa da drinks, Ahmad ya kwashi yaran da matar shi Suka fice, na Kara gyara zamana Bayan na kawo Mata abinci se kallona take duk inda na gota se ta kalleni, ni Kuma duk na tsargu, seda na Gama Mata hidima kafin nace

" Kuma ban gane ki ba"

Tayi murmushi tace

" Ai Baki sanni ba ma Unaisa, kina nan kyakyawa kamar yadda na sani, you look younger and beautiful a zahiri akan hoto, ba Wanda zaice kin haihu"

Ni nasan na haihu tunda I still have the scar a marata, Kuma Ina kallon yarana Dake gudu ko Ina, na danyi murmushi bance komai ba tace

" Maman Al'amin ce, Aminu naki"

Nayi saurin dagowa na kalle ta, se Kuma kamannin ta da Amra ya Kara bayyana, nayi saurin sakkowa kasa Zan Kara gaishe ta, ta fara dariya tana dagani tace

" Haba ai mun gaisa Kuma, ya kike? It's nice meeting you in person."

Nace

" Thank you! Ya hanya?"

Tace

" Alhamdulillah! Yaran da aka fita dasu ne jikokin nawa?"

Na gyada Kai na Ina Dan Murmushi a hankali tace

" Kiyi hakuri nazo Babu sanarwa, shima Bai San nazo ba. Naga ni na Bata wannan gayyar ya kamata na gyara ta"

Na Dan kalleta, fuskatar ta a marairaice, tace

" Unaisa Al'amin baiyi aure ba bansani ba ko kin sani, bansani ba ko ya fada Miki hakan?"

Nayi sauri da mamaki nace

" Har yanzun?"

Ta gayda Kan ta, a hankali ta fara bani labarin duk abinda ya faru da Al'amin, da tazo rasuwar Baba kawai se ta fara kuka, tunda ta fara bani labari kaina ya kulle, hankalina ya tashi, Al'amin went through all this alone? Ni dashi mun Sha wahala kenan? Ni da ita se na fuskanci muna da wani Abu in common shi ne mutuwar abinda muke so, tuni na fara ji mutuwar Abiey ta dawo min, na kifa kaina nayi ta kuka tana Yi, to Babu kowa ma a gidan balle a lallashe mu, se ita ta lallashe ni tace

" Da hannuna na watsa farin cikin family na, da kaina saboda kwadayi da ya rufe min idanu na Hana ku farin ciki"

Na girgiza Kai nace

" Kiyi hakuri Mummy, ki daina ganin laifin kamar naki ne, ki dauka Haka Allah ya tsara, ba gashi ba ban taba tunanin Zan hadu da Abiey ba Amma dake Allah ya tsara hakan har na haihu, idan kina Jin ke Kika ja wannan to abin zai dinga hunting dinki, Dan Allah Mummy ke saukaka"

Mummy ta danyi murmushi a ranta tana ayyana wauta da tayi da ta Hana Al'amin aure na. Tace

" Unaisa ya maganar ku ke da Al'amin?, na mishi magana yace na bashi lokaci, na gaji shi yasa nazo da kaina saboda na fahimci matsalar daga gurin ki take!"

Na Dan saki ajiyar zuciya, se Kuma tace

" Ina son na gyara abinda na Bata, Ina ganin shi ne kadai abinda zanyi naji na gamsu Al'amin ya yafe min, Dan Allah Unaisa ki Kara bamu dama"

A hankali bansan kukan meye ba nace

" Mummy Ina kokarin ganin yadda zanyi da yarana ne..."

Mummy tace

" Zai rike su na tabbatar Miki da hakan!"

Na girgiza Kai nace

" Mummy Yan uwan su bazasu yarda ba!"

Se tayi shiru, kowa idan na Fadi Haka se na rufe bakin shi, karshe Haka ta tafi bamu da matsaya, only God knows me matar take shiryawa. Tana zuwa Kano ta nufi gidan Anna I don't even know yadda akai lukman yasan gidan. Kawai Bayan kwana biyar Abba ya kiarni akan nazo Yana son ganina, seda gaba na ya Fadi, ranar asabar da sassafe su Alby Basu tashi ba ma na tafi Kano, takwas na isa straight Kuma gidan na wuce, na same shi muka gaisa yace

" Ya maganar ki da Aminu? Ya ake ciki?"

Na Dan zaro idanuna nace

" Abba wallahi... Ya akai ka sani"

Yayi murmushi yace

" Ni baban ki ne ai, kina tunanin Dan jaha ta rabamu bana saka idanu Akan abinda kikeyi? Me yasa Baki son auren shi?"

Nace

" Abba Dan Allah!"

" Unaisa ba dai cemin zakiyi ba zakiyi aure ba Kuma? Shekaran ki suka nawa? Aure zakiyi that's final, Zuhra ta tabbatar min kina son shi, so cikin sati Zan karba kudin auren. You decide Wanda Zaki bawa yaran ya rike"

Se na fara kuka sosae nace

" Abba Dan Allah ka bani lokaci, Dan Allah, Abba yarannan bana son barin su a wani gurin, bana son yin auren Kuma"

Yayi shiru yana Jin shehseka ta yace

" Ya Isa haka, ki bar kukan but zakiyi aure Zaki aura Aminu, mahaifiyar shi for three days tana zuwa Kuma nasan kina son shi, nayi magana dashi shima and I truly appreciate son da take Miki, kiyi hakuri Haka rayuwa take Bata zuwa yadda muka tsarata"

Abu kamar Wasa zancen aure se ya baza ko Ina, Ashe kowa zuba min idanu yayi, kowa yayi ta murna kada Al'amin yaji labari, tun Ina nokewa har na fara shiri, Shirin da ko a aurena da Abiey banyi ba, Kar kuga laifi na tsohuwar Zuma ake magana. A Yan kwanakin Banda soyayya me kwantar da hankali Babu abinda muke Yi, na Gama resolving nayi magana da Anna Akan Zan bawa Ahmad da Nuzla yaran, ko Babu komai suna Dutse zamu dinga haduwa akai akai.

Unaisa is not free, pay N300 to
[6/30, 10:40 PM] Hauwa Galadima: INDA MATSALAR TA SAMO ASALI

Ina zaune wayata ta yi ringing na dauka sai na ji kukan mace da karfi, cikin kukan tana magana da karfi 'Anty Maza macuta ne, Maza Azzalumai ne...ba su da imani.' Jin yadda matar nan ke fadin maganganu kala-kala kuma tana kuka ya sa na ce, kin ga kashe wayar ki gama kukan ma yi magana anjima.

zuwa can ta kara kira lokacin ta daina kuka, sai na ce mata ina jin ki gaya min me ya faru, cikin damuwa ta fara bayani 'Anty ina cikin matsalar zaman aure mijina kullum fada zagi cin mutunci, zargi ga wulakaanci kala-kala, jiya ta kai har duka na ya yi duk ya farfasa min jiki, yarana suna ji suna kuka amma bai sauraresu ba.'

Na nisa na ce bai kyauta ba, amma ke me ki ka yi masa har ya kai ga dukanki, domin ance karfe daya baya amo, cikin sheshekar kuka ta ci gaba da magana.

'Yarona na biyu ne ya je ya yi fada da yaran makota har ya fasawa daya kai, aka zo aka kawo masa kara, shine ya kama bala'i wai shi gaskiya ya gaji da masifar yaranan, shi ya fara shakka ma anya yaran nan jinin sa ne, shine raina ya baci na ce masa, ai tunda kasan ka saba barin 'ya'ya ga matan banza a titi dole ka yi zaton wadannan ma ba yaran ka ba ne, shine fa ya hau dukana yana zagina da gaya min munanan kalamai yar iska, sakarya, shashasha!.'

Ta kara fashewa da kuka tana magana ' Na rantse da Allah Anty ban taba sanin wani namiji a duniya bayan mijina ba, amma shine ya ke min wannan zargin, wallahi Allah ya isa.'

Ta ci gaba da kuka sai da na barta ta yi ta gama sannan na ce mata, yanzu ina son zan miki wasu tambayoyi, kar ki boye min komai, ke a ganinki meye dalilin da ya sa mijinki ya ke miki wulakanci, shin kin aure shi ne saboda kudi, ko ke kika ce kina sonsa, ko iyayanki sun masa wulakancki ko dai wani abu da ban lissafa ba ne ba?

Ta ce 'Wallahi lokacin da na aure shi ma a gidan haya muke, da kyar ya samu yayi gida mai daki biyu, kuma har yanzu kullum sai an futa an nema, sannan iyayena sun aura masa ni ba tare da sun bukaci komai ba, kuma yanzu fa saboda wulakanci cewa ya ke yi, wai wallahi da ya na da kudi da tuni ya rabu da ni ya auro yar mutunci, biyayya ina yi masa daidai gwargwado ina kuma hakuri da shi, amma wallahi na gaji yanzu.'

Cikin kalamanta na kama wata kalma daya don haka da ita na kara tambayarta, kin ce yana cewa zai auro yar mutunci tsakaninki da Allah me hakan ke nufi, kin taba wani abu na zubar da kima ne a gurinsa, ko kafin aure ko bayan aure ki gaya min gaskiya.

Ta yi shuru tsahon lokaci sannan ta nisa ta ce ' Eh gaskiya kafin mu yi aure, bayan an saka mana rana wata tara idan muna zance yana bukatar ya taba jikina ni kuma ina kin yadda, har ta kai yana fishi yana cewa bana son shi, daga karshe dai na yadda da shi watarana mun je wata unguwa, tun daga lokacin idan ya zo har kuka ya ke min idan ban amince da shi ba, har ta kai aka yi mana aure, to ni ko irin dadin amarcin nan ban ji ba, kullum sai zargi da wulakanci, yanzu ga shi har mun tara yara biyar, kuma idan na je na gayawa iyayena sai suce na yi hakuri, idan ma na kashe auren babu inda za su ajiye ni tunda a gidan haya suke daki daya, amma wallahi ni yanzu gwara ko duniya na bi na gaji wallahi Anty.' Ta kara fashewa da kuka.
Chapter 72 · 0% Book details