← Book details Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 78

Sashe 29

Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Unaisa is not free, pay N300 to 3091721807 A'isha kwalam Hassan first Bank of Nigeria and send evidence of payment to 09063467258
[5/26, 1:20 PM] Hauwa Galadima: *Y*

Da sassafe na tashi saboda nasan ranar zamu koma gida muma idan Dada ta yadda, nayi wanka na fito na samu wayata na haske, na nayi tunanin Al'amin ne Amma se Naga Zuhra, seda gabana ya Dan Fadi Ina tunanin Kiran sassafiyya Ashe Wai har Tara da rabi tayi ni ce nake ganin it's still early. Na dauka Ina fadin

" Amarya a gidan Yaya Khalifa"

Ta Dan saki tsaki kadan tace

" Shi ne ma ba Zaki ce min kinyi missing Dina ba"

Se na danyi shiru Jin idanuna sun ciko da kwalla, nayi saurin basarwa nace

" Ke Kika sani. Ya kike?"

" Lafiya Lau! Unaisa bansan me Zan dafa ba, wallahi na rasa abinda Zan dafa"

Nayi dariya sosae nace

" Lallai! To ni me Zan miki?"

Ta marairaice murya

" Come on sister ki fada min Dan Allah"

Nayi dariya na fara Mata lissafi har ta samu ta zaba sannan mukai sallama, Ina kashewa na saki ajiyar zuciya, Zuhra tayi gidan ta, yanzun tana da aure. Se washegari muka samu muka koma gida, se naji Babu dadi rashin Badi'a, mussamman da na kalla inda take jera kayanta dukka Babu komai, shelf dinmu ni da ita a dakin Anna da muke saka kayan aiki, inda keken dinkin ta yake dukka Babu komai, se naji kewar ta na dakko wayata na fara Kiran ta

" Badi'a I missed you!"

Na fada Ina Dan Jin Babu dadi

" Adda har kuka nayi dazun Dana tuna ku, bayan ya fita gidan yayi shiru"

Nace

" Allah sarki, kiyi hakuri ki zauna lafiya da kowa Ina Miki fatan alkhairi"

Tace

" Nagode sosae Adda se yaushe zaku zo Kuma?"

Nace

"Zamu zo inshallah!"

Da Haka mukai sallama da ita na Dan zauna Ina tunanin duniya Ina tunanin haka mutuwa ma zata zo ta riski bawa ba tareda ya shirya ba.

A hankali ranaku suka cigaba da tafiya, muna Kara shakuwa ni da Al'amin, bamuyi  alkawarin tada junan mu sallah ba Amma dai da zarar na tashi zanga message din shi

" Good morning Babes! I hope you had a sound sleep. Se munyi waya"

Ni Kuma Zan bashi reply da yadda na tashi, it doesn't matter duk yadda mood dina yake a hakan Zan fada Masa. Da zarar ya Gama Shirin tafiya aiki zai kirani a wañnan lokacin zamu Yi Yar Hira sannan muyi sallama, se idan yaje zai kirani ko Kuma ni na Kira naji yadda yaje, to Kuma se chat, zamu iya yini idan bama komai muna chatting, shiyasa kullum data ta is on Haka shima tashi, idan munzo kwanciya shi ne zamuyi Hira sosae sannan Kuma muyi exchanging message se bacci. Wannan shi ne routine din shiyasa within shortest of time bana cikakken awa ban tuna dashi sau goma ba, ko me nake Yi kawai tunanin shi nake, duk wata Waka ta soyayya idan naji shi kadai nake kawowa. Ban taba tunanin a duniya Zan so wani namiji bayan Cànîm ba, nayi tunanin a wañnan son Dana Masa bazan Kara son wani ba Kuma.

Na koma makaranta, dukda kafin na tafi Anna ta tambayeni shi Wanda nake waya dashi waye shi, nayi murmushi nace

" Anna da ba kowa"

Ta kalleni da kyau tace

" To abi komai dai a sannu Adda, kada a zurfafa'

Na gyada kaina, da Ina fadawa Zuhra tayi ta min dariya Wai ai kowa ya kalleni yasan I'm in love, yasan cewar soyayya nake saboda I smile for no reason, nidai Ina ruwana, I can't help son shi nake, kaunar shi nake. Dukkan wani namiji idan na kalla baya burgeni, Kar kuce na faye shirme I believe Haka zuciyata take. Da daddare kafin na tafi Ahmad yazo bayan munyi sallar maghrib, Ina daki Muna waya da Al'amin

" Idan Kika koma ba Zaki ji Dadi ba nasan Zaki Yi kewan Zuhra"

Ya tabo min inda yake min kaikaiyi nace

" Ai tun kafin na koma dinma na fara ji, though Ina da Kai"

Yayi murmushi yace

" Sure I'll always be there, Danma kin ki yarda muyi auren"

Mita! Na ayyana kafin na bashi amsa ko naji Anna na Kirana, na leko ta window na hango Ahmad zaune saman tabarmar da Anna ta baza an zuba Masa gyada me kwamso Yana ci, na dauka hijab Dina na fito. Yana ganina ya saki murmushi Yana fadin

" Munyi fada Dake gwara ma ki sani"

Na tabe baki nace

" Shiyasa Naga anzo ganina"

Yayi dariya, Anna dake gefe tace

" Ku zo ku tafi ko kwaje ki dawo da wuri"

Na dubi Anna nace

" Ina zamuje?"

Tace

" A'a gidan Badi'a Mana, Zaki tafi ko lekata bakiyi ba?"

Na koma daki na Ciro wani karamin veil Dan kayana are very ok na fita dasu, na Dan fesa turare sannan na dauki wayata na tura Masa message Akan zamu fita da Yaya Ahmad gidan Badi'a. Anna tace har gidan Muhammad mu karasa mu gaishe su. Se da muka dauki Hanya sannan Al'amin ya Kira , Ina dauka yace

" Who's Ahmad? You've never mentioned him"

Nace

" Yeah, cousin din Zuhra ne"

Se yace

" Ok! Enjoy"

Kit ya kashe wayar, na rike wayar a hannuna Baki a sake se Kuma na shrugging shoulders Dina na cigaba da biyewa Hunainah Dake min hirar makaranta. Nuzla dama ce a gaba suna Dan taba hirar su, na fahimci tun bikinnan suka dinke, da gaisawa kawai suke high high. Bansani ba ko akwai Abu a tsakanin su, se na ayyana kenan itama se tayi aure ta barni kenan? Se na girgiza Kai nace no it can't be Bayan gashi Al'amin na Sona, Kuma nasan wannan son will take us to our matrimony.

A gate Ahmad yace min

" Ai kamar Muhammad na gidannan ma, ga motar shi"

Nace

" Shi kenan ba se munje ba, ma gaisa anan"

" Lazy dama Baki son zuwa"

Muna sallama ko muka same su su hudu a parlon alamu sun nuna Basu Jima da zuwa ba ganin ko drinks din da aka kawo musu Basu Sha ba. Tana Jin sallamar mu ta mike ta yo kanmu da gudu, ta rungume, Nima na rungume ta, tayi kyau sosae a Dan kwanaki, she looks calm Kuma hankalin ta a kwance yake. Na riko hannun ta muka karaso ciki, na gaida Yaya Muhammad da Yaya Man, sannan na dubi Bilkisu dake daddana waya nace

" Ina wuni? Ya taro Allah ya Sanya alkhairi!"

Tace

" Mhmmm"

Shikenan, Yaya Man da kanshi yayi entertaining dinmu Dan ko kusa Taki tashi, Yaya Ahmad nata zolayat ta ita dai Bata ce komai ba, se ni ce nace

" Wai Yaya Ahmad baka girma?"

Muhammad yace

" Fada Masa Unaisa, ai shi dai sede a barshi kawai"

Ya Bata Rai yace

" Are you ganging against me, dadin abun kaima bakunta kazo'

Kawai muka hada Baki ni da Muhammad wajen fadin

" Har da gori?"

Se muka kalla juna muka kwashe da dariya, Nuzla da Badi'a na Taya mu. Bilkisu ta kalleni sannan ta kalla mijin ta tace

" Wannan wanne irin dariyar rashin kamun Kai ne, haba Mana"

Dif na daina dariyar ma tsaya Ina kallon ta, se cika take tana batsewa Nuzla tace

" A'a dariyar ma se anyi Mata bad comment, Wanda ba zaiyi ba ya bar ma suyi suyi abar su"

Tana fadar haka ta mike ta nufi bedroom din Badi'a, muma se muka bi bayanta like dama ni naturally bana son rainin wayo, anan Badi'a ta same mu, muka ta Hira har Bayan Isha sannan muka fito, har lokacin suna nan, sede ko kunyar Man da Ahmad Bata ji ta kwanta jikin shi tana Wasa da sideburns din fuskar shi, shi Kuma Yana ta rike hannun ta Amma a banza, na musu sallama da Allah ya Sanya alkhairi Muka tafi muka bar Badi'a na kuka. Rayuwar kenan ai. Ina komawa gida na shirya Dan kwanciya, a lokacin na dakko wayata na fara Kiran shi, Yana dauka yace

" Yanzun nake Shirin Kiran ki naji Baku dawo ba?"

Nace

" Bamu Jima da dawowa ba Kam, howwa u?"

" Alhamdulillah! Yanzun Zan ci abinci idan na Gama Zan kiraki se muyi Hira idan bakiyi bacci ba"

Na amsa da to sannan na Masa sallama, na kunna kallo Amma ko mintina biyar banyi ba bacci ya daukeni, se asuba na farka Naga calls dinsa hade da message. Na koma makaranta Haka ma Zuhra ta daow, da farko akace mu koma gidan Baffa to Kuma ganin ai final semester ne se aka ce mu zauna kawai, duk bayan sati biyu Zuhra take zuwa weekend, yayin da shi ko sati baya Yi Zaki ganshi yazo, zaman su gwanin shaawa, Babu wani hargowa Amma kana kallo kasan sun damu da juna. Abubuwa da dama sun canja a tare da ita, ta Kara hankali da Kuma nutsuwa se mu zauna a daki muyi Hira Bata fita ba Amma da Bata awa daya se ta fita wajen kawayen ta. Ranar muka shirya zuwa gidan A'isha tunda wuri muka fita, me napep yazo ya tafi Dani har gidan muka wunar Mata ita Kam Bata da lafiya laulayi take, nace Mata

" To ai ke bakiyi amarcin ba"

Ta danyi yake tace

" Ki Bari kawai Unaisa, ni kadai nasan me nake ji"

Nace

" Gaskiya nafi son ace nayi kamar 5 months banyi conceiving ba"

Zuhra tace

" Tabdi, hutun jaki kenan"

Se Kuma hirar tasu ta koma ta masu aure naja gefe Ina chatting Ina dariya, Zuhra tace

" Unaisa idan Baki aura Al'amin ba ya zakiyi?"

Wani irin muguwar faduwar gaba ta ziyar ce ni, take fuskata ta canja nace

" Wai me yasa Baki son zaman lafiya ne?"

Ta Dan dafa ni tace

" Ba Haka bane, kawai kina son shi da yawa ne, Amma kawai tambaya nayi"

Cikin rashin jin Dadi nace

" Amma Ina zaman lafiya na.."
Chapter 29 · 0% Book details