← Book details Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 78

Sashe 13

Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da wannan mukai sallama, naji Dadi na Kuma Yi adduar Allah yasa hakan ya kasance da naji dadin gaske, Dan Ina son Nima Naga munada Yan uwa. Aikuwa washegari na fadawa Anna cewar Dada zata zo, tayi niyyar fita clearing kayan ta da Suka iso Amma se ta Bari, mukai girki sosae na tarbar ta. Karfe daya Suka iso itada Yaya Man da Zuhra, har waje naje na taro su, tana ganina ta rungume ni se nake Kara ganin yanayin Anna a tare da ita, wallahi har jikin su iri daya ne. Tare muka shigo har Yaya Man da da farko yaki seda Dada tace ya shigo kafin ya shigo, Anna ta fito ta tarbesu, Ina ganin kallon da sukewa juna. Zuhra na tama Anna surutu itama tana biye mata se can muka Basu guri Dan suyi magana. Dada ta dubi Anna tace

" Maman Unaisa bansan ta Ina Zan fara ba, Amma dai Bari ki gani"

Ta fada tana Ciro wani tsohon hoto daga jakar ta, Anna ta karba ta tsirawa hoton idanu kafin Kuma tayi saurin mikewa ta nufi bedroom dinta ba tareda tace komai ba, Amma yadda take tafiya tana hardewa shows she's nervous, ba jimawa se gata ta dawo da irin hoton itama, ta mikawa Dada, Dada ta karba tace

" Ke kanwa tace Maman Unaisa, ke jini  na ce, Ina Zulai?"

Anna se hawaye Shar a fuskarta tace

"  Inna Zulai ta rasu, Yaya hafsatu Ashe kina da rai, Ashe kina nan? Har ta rasu duk lokacin da zamuyi magana da ita se ta tambaye ni ko na hadu dake? Allah me iko Ashe kina kusa"

Dada tana kuka tana jajanta rasuwar Yar uwarta, hoton anyi shi ne ranar bikin Dada, a hoton akwai Dada, Inna Zulai da Kuma mahaifiyar su Anna. Seda Suka daina kukan se Kuma Hira ta barke, ita Dada Bata masan an haife Anna ba, ba Kuma tasan rasuwar iyayen ta ba, wayar ta ta dakko ta Kira Abba ta fada masa labari me dadi, Yaya Man na zaune se ya Kira mu muka zauna, nace

" Amma Anna Baki taba fada Mana cewar kina Neman Yan uwanki ba"

Tayi murmushi tace

" Unaisa kenan"

Dada ta hada mu mu hudun ta rungume mu Jin irin wahalar da muka sha, har seda ta saka ni kuka se nake jin abin banbarakwai, Wai yau ni ce na samu wata matsayin yayar mahaifiya ta. Basu tafi ba se bayan sallar ishai, Yaya Man ne ma ya fita da Hunainah da Badi'a da Nuzla, mu Kuma Muna daki Hira. Dukka muka rakasu akan zasu saka Rana suje Masaya Dan Dole aje aga yaran Inna Zulai dukda sun watsar da Anna Suma.

Unaisa is not free, pay N300 to 3091721807 first Bank of Nigeria and send evidence of payment to 09063467258

[5/15, 9:46 PM] Hauwa Galadima: Duk kayan da zanyi amfani dashi Dada ta siya min, duk Dunkin da akaiwa Zuhra seda aka min, komai namu iri daya Haka aka Mana, ranar Wednesday Anna ta hada kanmu duka da wurwuri muka tafi gidan Dada, wannan ne karon farko da zasu hadu bayan zuwanta gidan mu. Yaya Saif yazo ya dauke mu, Dake shi baida sakin fuska Bayan gaida Anna Bai Kara magana ba, mune ma muka Kara gaishe shi. Ya amsa, tunda muka shiga Zuhra na tsaye tana jiran mu, Muna parking ta kwaso a guje ta rungume Anna, Nuzla tace

" Allah Adda Zuhra Baki jin kunyar gudu"

Ta saki Anna ta bisu ta rungume su tana fadin

" Lallai Nuzla Naga Anna se naki gudu, ke Bari Naga idan Kinga Dada ko ba zakiyi gudu ba"

Duka mukai dariya, se ta dawo gefena tana murmushi tace

" Kiyi gaba Mana, kamar wata bakuwa"

Tasan bazan Yi magana ba shiyasa tayi dariya muka shige ciki, Abba da Dada, Yaya Saif da Yaya Man da Kuma Ya khulthum, ita bamu taba haduwa da ita ba, ita ce babba tayi aure da dadewa, sure muna Kama da ita kamar yadda Dada ta fada Mana ranar. Suna tsaye alamar suna jiran mu, gaba daya fuskokin su murmushi ne akai Haka muma namu, aka zazzauna cikeda farin ciki, se Hira. Ranar se dare muka koma gida. Wannan kenan!

Ranar lahadi Yaya Man yazo tafiya dani, tunda sukai sallama na fara kuka karku manta tunda nake ban taba zuwa wani guri na kwana ba, bani kadai ba dukkan mu ma, Babu inda muka taba zuwa duk abinda ya faru to zaka ga muna gida da iyar mu. Anna ta dubeni da fuskar ta me nuna damuwa tace

" Meye abin kukan? Menene?"

Nayi shiru se kuka nake saboda wani Abu naji ya tsaye min a makogaro na, ta Dan janyo ni jikinta tace

" Ya Isa kukan, bayan kullum zamu dinga waya Banda abinki?, kawai dai Adda kuyi karatu, ku sani yarda ce ta Sanya muka amince muku kuje wani garin kuyi karatu, ku rike mana Amana, ku Kare mutuncin ku, kuyi abinda ya kaiku. Allah yayi muku albarka"

Naso har zuciyata ace na rike wannan kalaman na Anna, naso ace na cigaba da kula da kaina har zuwa lokacin da zaa kaini dakin mijina, sede banyi hakan ba,na bar kula da kaina da kowa yayi min fadan, mutuncin da na tsare a karshe na sake shi. Kaico!

Zuhra ta amsa da Amin Amma nikam Banda kuka Babu abinda nakeyi har seda muka tafi a Haka. Badi'a ke zaune a gaban mota se ni da Zuhra a baya, Babu yadda baayi ba Yaya Man ya taho da Nuzla yaki yace ma Anna shi Badi'a kawai yace. Muka karasa school har kofar gate din hostel sannan ya aje mu, lokacin na daina kukan na hakura, Amma fuskata duk tayi alamar kuka. Yaya Man ya dube mu yace

" Take care of yourselves, idan akwai matsala it's just a call away, ok?"

Muka gyada kanmu, ya fito Mana da kayan mu sannan ya Kara Mana 5k Akan kudin da already aka bamu. Nan ma da zai tafi na dinga kuka Badi'a na Taya ni, Yaya Man ya dubi Zuhra yace

" Take care of her kinji?"

Ta gyada kanta ta ja hannuna mukai ciki, already munsan dakin da akai Mana allocating, Babu kowa a dakin muka Shiga muka aje Kaya, kowa da katifar shi akan gado, na zauna gefe, ta fita tana jido kayan a hankali har ta Gama, toilet ta saka na wanke fuskata nayi sallah itamaa tayi, sannan ta Kira Wanda ya dace tace min karasa. Da kaina na bude manyan lockers din dake jikin bango, ta gefen gadon Zuhra na saka Mana kwanukan mu da kayan abincin mu, na kusa da nawa Kuma na jera Mana kayan sawan mu da takalma, trollies din da sauran abinda ba zaa rasa ba. Ita ta shimfida Mana bedspread akan gado sannan na Dan kwanta na juya Mata baya. Se bayan maghrib sannan na ware muka ci abinci na Kira Anna ta Kara Mana nasiha da Dada nan ma seda nayi kuka. Wasawasa satin duka cinye shi akai wajen Mana orientation tun daga Kan rules din makaranta da Kuma na council Wanda yake Kare interest din profession din, ethical conduct da Kuma penalties ga Wanda yayi breaking a single rule. Abubuwan da tsauri Amma ga Wanda yake ganin yafi karfin bin doka, aka zo Kan exams nan ma Suka Mana yadda ake exams da Kuma penalties din faduwa Wanda either they withdraw or demote you. Na saki ajiyar zuciya Ina ayyana ko da ace mutum daya ne zaiyi passing exams din that person is definitely I, na sawa Raina determination me karfi na Kuma sawa Raina cewar karatun me sauki ne.

Banbanci sosae tsakanin nida Zuhra, Yan set dinmu dukka sunyi tunanin gidan mu daya ne se idan kaji surname din mu ya banbanta sannan zakaa fahimci hakan, ita din mutum ce so friendly and care free, kafin muyi wata daya Babu Wanda Bai santa ba cikin class din mu maza da mata, yayinda ni wasu Basu San sunana bama sede ace min sister Zuhra, Haka kowa yake addressing dina. Ki hostel muka dawo Ina daki yayinda ita har team din karatu ne da ita, tsabar yadda tasan halina yasa Bata takura min akan lallai se naje class karatu ta tabbatar ni din zanyi karatu a dakin, kawai tasan mutane ne bana son shiga. Haka idan weekend yayi zata tarkato friends dinta dakin mu to anan ne ma idan suna Hira nakan saka Baki ayi dani, Amma da zarar an fara musu Zan dauki wayata nayi wani abun. Tsakanina da ita Babu matsala mun riga mun fahimci kanmu, ni Ina son girki yayinda ita Kuma Bata Faye so ba se ya zamana kusan ko da yaushe ni ke girkin yayida take Mana wanke wanke da gyaran daki, idan tazo kayan sawa ni nake wanki ita Kuma tayi Mana guga.

Watanmu uku muka fara midsemeter exams, dukka mun dukufa da karatu da addua saboda it's either you make it or you get withdrawn. Ni na fara fitowa daga hall na Koda na mikawa chief examiner seda ya kalleni yace

" Are you sure you are done?"

Na gyada Masa kaina na amsa shi, still ya bubbude pages din yaga na Kai har kusan karshen booklet se kawai yace naje, na ninke question paper na nufi hostel, na bude daki na fada Kan gado Ina jin sanyi yau mun Gama theory se a washegari zamuyi instrumentation. Wannan bashi da matsala Dan dukkan forceps din da aka koya Mana na San su Kuma Zan iya identifying dinsu. Har na Gama dafa noodles sannan Zuhra ta dawo, ta zauna muka tambaya juna exams sannan ta wanko hannun ta muka ci, washegari last paper Bayan mun fito akai addressing dinmu se Kano, kowa Yana hada kayan shi ya tafi dashi naki no da Zuhra saboda inada tabbacin duk abinda aka tambaya na amsa Kuma nasan Allah will take care of the rest!

Se yamma muka karasa Kano, tun a Tasha kowa yayi hanyar gidan su, it feel so good Bayan watanni ka dawo gida, Ina Shiga dukka suka yo kaina suna Yar rige rigen rungume ni, na hada su dukka na rungume su Ina fadin

" I've missed you girls!"
Chapter 13 · 0% Book details