← Book details Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 78

Sashe 28

Unaisa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da farko bayan ya tafi ban amsa Masa ba saboda Ina ganin ya kamata na duba Naga meye nake so a wajen namiji? Wanne irin namiji nake so? Se Kuma na ayyana does that even matter a yanzun? Dan tuntuni na fahimci na fara son shi, Amma dukda Haka ya kamata nayi addua. Ya kamata na nema zabin Allah Dan shi kadai yasan me zai faru gobe. Na dage sosae a kwanakin da Suka biyo baya nayi istikhara na Kuma Yi addua sosae, se naji hanaklina ya kwanta dashi Dan Haka a Rana ta biyar na dawo daga class nayi wanka aka kirani akan an aiko min sako daga kano, nasan Anna ce Dan munyi maganar da ita, ankon da muka fitar na Zuhra, Baki daya abinda ya rage saura na bikin wata biyu ne, Kuma a ciki zamu Yi hospital final shiyasa abin ya hade da yawa, ga kaaratu ga Shirin biki. Na zura riga na dauki hijab na saka na dauka wallet Zan fita se na tuna ban fada Masa, na Ciro wayata na fara dialing number din shi Babu jimawa ya dauka

" Babes har an tashi?"

Nace

" Mhmmm an tashi, Kai fa?"

Yace

" Na turo Miki roaster fa, yau call nake so Zan zauna a kazaure"

Nace

" Eyya! Waye zai baka abinci?"

Ya danyi dariya

" Zan nema, beside inada friends ai"

Na gyada Kai sannan na fada Masa zanje karbo sako ne a wajen driver a Tasha,

" Must yo go? Ki Bari nasa a karbo se kije gate din school ki karba, ko ki na son fitar ne?"

Na girgiza Kai nace

" Not at all! Nagode kaji"

Yayi murmushi yace

" Anything for you Babes!"

Baa fi awa ba, naje gate na karbo tarin kayan, Ina shigowa daki na saka gadon Zuhra na dakko wayata na Kara Kiran shi

" Thank you an kawo"

Yace

" Yawwa! Muyi Hira ko Zaki wani Abu? I'm bored here"

Na gyara zamana nace

" Muyi, it's my duty to keep you company"

Ya danyi dariya ta Jin dadi yace

" Da gaske? Naji dadi"

Muka zauna muka ta hira, hirar mu Bata karewa kullum Hira muke se can wajen maghrib nace

" Lokacin sallah ya kusa"

Yace

" Yanzun nake Shirin fada Miki, muyi magana anjima, Zaki Dan jini shiru akwai CS din da zamuyi tsakanin maghrib da Isha"

Na gyada kaina ku kwace Yana gabana sannan mukai sallama na Masa adduar nasara, Bayan na idar da sallah na rike wayata a hannuna, Ina adduar Allah yasa hukuncin da na yanke ya Zama alkhairi gate mu Baki daya

"You asked whether I can accompany you through the rest of the journey of your life? Yes! I'll love to be your everything, I gladly accepted you and I'm happy to tell you that I Love you Cànîm"

Ina sending Masa na kashe wayata Dan nasan sun fara aiki, bansan abinda zai distracting din shi, Haka kurum nake jin wani irin tsananin farin ciki, nake jin tamkar na fita titi nayi shelar na samu masoyi Yana Sona Kuma Ina son shi. Zuhra ta shigo itada Husna dan supervisor su daya, suka fara ganin Kaya bayan Zuhra tace min

" Ki dai na wannan Murmushin kowa yasan kin fara soyayya"

Na Kara sakin wani tattausan Ina jifanta da pillow dake gefena, tayi dariya Husna tace

" Wannan Al'amin din da karfin shi yazo Naga alama, gaba daya ya susuta ki"

Ni dai bance komai ba se matsowa nayi da list din Wanda suka siya Ina fada musu Muna zurawa cikin printed bag me rubutun "Thank you! Khalifa and Zuhra" atamfa daya ta kamu, se lace guda daya, kowa seda yace ankon mu yafi nasu Badi'a da Aysha kyau. Muna gamawa muka fara dauka Muna bin duk Wanda suka siya Muna Kai musu daya bayan daya, se Bayan ishai muka kammalla se na gidan su Yaya Khalifa ya rage da Kuma Wanda muka dakko extra ko akwai Wanda zaice Yana so.

Seda muka Gama karatu sannan na dawo daki na kunna wayata, na kwanta Ina kallon wayar Ina jiran Kiran shi, Bai bani kunya ba kuwa se gashi ya Kira

" Babes Amma kinsan hakan da kikai Baki kyauta ba ko? Ta Yaya Zaki fada min irin wannan abun sannan Kuma ki kashe wayar, it took me lot of courage ban taho hadejia ba"

Nayi ta dariya a hankali, se yayi shiru yana saurara na har na Gama sannan yace

" Idan kina dariya farin ciki nakeji, a kalla nasan I'm part of your happiness"

Na gyada Kai na nace

" Da gaske ne, abinda yasa na kashe wayar saboda bana son ya hanaka aiki"

Yace

" Ai karfin gwiwa ya Kara min Babes, like kowa seda ya fahimci tsananin farin cikin da nake ciki, Allah ya bani ikon faranta Miki Unaisa, Allah yasa mu zauna karakshin inuwa daya"

Soyayyar mu ta cigaba da tafiya cikin aminci da alkhairi, har lokacin da Zan fara hospital final yayi, ya rage lokutan da muke dadewa a waya, ko Kuma idan baya komai to zai kirani muyi karatun tare, wannan abun Suka Kara Masa matsayi a gurina na Kuma Kara sakin jikina dashi sosae ya mamaye ko Ina. Ana gobe paper one mun gama karatu na Dan kwanta a kasa dan na huta, wayar Zuhra Dake setin pillow na ta fara ringing, na watsa Mata harara nace

" Wai Dan Allah Baki son nayi bacci ne"

Tace

" Allah Baki hakuri"

Ta tambayeni wacece na fada Mata, tace na saka ta a speaker ita ba zata iya tasowa ba tasan Nima ba tasowar zanyi ba.

" Zuhra Ashe aure zakiyi?"

Tace

" Eh fa Naga na tura Miki komai personally"

Tace

" Yeah na gani, ta Yaya Zaki fitar da ankon 15k kacal, kinje kin hada Kai da yaran talakawa kin Zama Yar kauye"

Na hangame Baki, dubu Sha biyar ne kawai, nace lallai Wai yaran talakawa, Zuhra ta kalleni sannan tace

" Naji, idan zakiyi ki turon kudin ya kusa karewa"

" Ki sa min account details din anjima Zan saka Miki, idan kin shigo Kano zanzo na karba"

Tace to sannan na kashe wayar nace

" Kinsan Allah Zuhra ba zatai ankon nan ba sede taje kasuwa ta siyo, Yar rainin wayo"

Zuhra Tayi dariya tace Wai Haka take tun can nace ita ta sani Amma sede tasa wani abun Amma ba dai ankon da na siyo ba, inata mita Zuhra nace min inyi Mata shiru ko Kuma na Kira na kaddamar Mata, wayata tayi ringing se lokacin na fahimci ban ma canja Masa suna ba, a hakan na dauka, kafin na gaishe shi yace

" Na bada sako a kawo Miki, Dan fito ki karba"

Na Dan Bata fuska Amma bance komai ba na Mike, nace Zuhra tazo muje itama seda ta Gama mita sannan ta tashi muka tafi, tun daga nesa na hango mota kamar motar shi, nace

" Zuhra wancan kamar motar shi ko?"

Ta kalla sannan ta Kara hade Rai tace

" Ina Zan sani kin taso ni da ranar nan"

Na kalleta tare da marairaice fuska nace

" Ayya Mana Zuhra to kiyi hakuri"

A Haka muka karasa shi dinne kuwa, Yana hango mu ya fito, na Bata fuska shi Kuma Yana ta murmushi Zuhra tace

" Ki saki fuska Mana, bakiga yadda yake murnar ganin ki ba"

Na harareta Nima, se tayi dariya

" Meye abin fushin, Bai Miki kyau ba fa"

Ya fada lokacin Dana tsaya a gefen shi, na saki murmushi yace

" That's my Babes ko kefa, Zuhra Kinga tayi kyau ko?"

Zuhra tayi dariya tace

" Kawai se kaji kana son ganin ta?"

Yace

" Tun safe na shirya nace yau Babes dita Zan gani, I need to give her tactics on external examination"

Zuhra tace

" To Bari na koma tunda na Gama nawa"

Ta juya ta tafi Yana kiranta nace ya kyalleta, mun Dan taba Hira sannan nace

" Cànîm wannan son Yana min yawa fa, ji nake kamar I'm floating"

Ya danyi murmushi yace

" Haka nake son naji, da kin yarda ma ai da na tura munyi auren tareda su Zuhra"

Nayi saurin girgiza Kai nace

" A'a se bayan council"

Ya langwabar da Kai yace

" Ki tausayina bakya ji, it's in the next six months fa"

Nace

" To baza ka iya hakuri ba?"

Yace

" Of course Zan iya, Zan jiraki ki Gama"

Muka Gama exams, da full support din shi, aka Dan bamu break Wanda a cikin break din zaayi bikin su Zuhra, tunda muka koma gida na tarar da Shirin da ake Yi Babu Kama hannun yaro, duk komai namu sun Zama ready. Abba yace Anna ta dawo gidan Dada ayi a hade, da farko Bata yarda ba saboda tana ganin kamar hakan liability ne Amma se Baffa yace taje Babu komai. Haka kuwan ta shirya dukka da komai Muka tafi can, ni yafi min sauki ma. Henna party shi ne kadai event din da mukai ya hada dukkan amaren, Bilkisu Yaya Muhammad, Zuhra, Badi'a da Kuma Aisha da taho daga hadejia, a gidan Yaya khulthum akai, akai musu kunshi da muma bridal maids, muka ci muka Sha akai hotuna. Wannan ne Karan farko da muka hadu da Bilkisu, tun a ranar na fahimci Yar rainin wayo ce Dan ni ko magana Bata hada mu da ita ba. Washegari ranar jumaa aka daura auren bilkisu da Yaya Muhammad, Zuhra da Yaya Khalifa hatta Cànîm seda yazo. Da daddare mukai dinner. Washegari asabar aka daura auren A'isha da Ibrahim se Badi'a da Yaya Man. Suma dinner din su day daddare. Bikin yayi min Dadi sosae sede kamar yadda kowa yayi tunani ba karamar gajiya nayi ba, ranar lahadi aka dauka amare Dan kaisu, Zuhra nabi Dan Haka Anna tace, tunda muka je gidan yayi kyau a Dutse koami nata irin na Badi'a Dake naje gidan jiya Kai wasu kayan. Sede adduar Allah ya Basu zaman lafiya. Da Zan taho Naga Zuhra nata kuka ai Nima se na fara dan dama kawai Ina Dan jurewa ne, har muka dawo Kano Ina kuka, banyi hakuri ba seda Al'amin ya kirani ya lallashe ni sannan nayi shiru.
Chapter 28 · 0% Book details